Yadda Trump da Clinton suka yi abota da Jeffrey Epstein

    • Marubuci, Lucy Gilder
    • Aiko rahoto daga, BBC Verify in Washington DC
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shugaban Amurka, Donald Trump da tsohon shugaban ƙasar, Bill Clinton suna cikin fitattun mutanen da aka tabbatar sun yi alaƙa mai kusanci sosai da Jeffrey Epstein, wanda aka kama da laifukan lalata.

Trump da Clinton sun ɗauki hotuna da dama da Epstein a shekarun 1990 da kuma 2000, kuma a wasu lokutan suna cikin abokan shaƙatawarsa.

Daga Trump har Clinton, babu wanda aka zarga da aikata wani laifi, bayan tattara shaidu a tsakanin waɗanda Epstein ya ci zarafin su, kuma duk sun musanta sanin wani abu game da laifukan cin zarafi ta hanyar lalata da Epstein ya aikata.

Duk bayanan da ake da su a ƙasa kawo yanzu sun nuna cewa tsaffin shugabannin Amurkan biyu sun raba gari da Epstein na tsawon shekaru kafin a yanke masa hukunci.

BBC Verify ta yi bincike kan wasu bayanai na kafar intanet game da dangantakar shugabannin ƙasar biyu da Jeffrey Epstein.

1980 zuwa 1990

Abotar Jeffrey Epstein da Donald Trump ta fara ne a ƙarshen shekarar 1980, kuma abotar shi da Bill Clinton ta fara ne a farkon 1990.

A wata hira da ya yi da jaridar New York Magazine a 2002, Trump ya ce ya san Epstein tsawon shekara 15, lamarin da ke nuna alamun sun fara alaƙa ne a 1987.

Akwai hutuna da bidiyo masu yawa na Trump da Epstein a taruka daban-daban a farkon shekarun 1990.

Wani bidiyo ya nuna mutanen biyu suna halartar wani taron shagali a Mar-a-Lago a 1992. A cikin bidiyon kuma ana iya ganin Ghislaine Maxwell, wani abokin Epstein da aka samu da laifin cin zarafi ta hanyar lalata a 2021, yana tsaye a bayansu.

NBC, wadda ta zaƙulo bidiyon daga taskarta a 2019 ta ce an ɗauki bidiyon ne a lokacin wani shirin tattaunawa da manyan mutane na Amurka mai suna "A Closer Look," wanda ya ware wani sashi nasa domin tattaunawa da Trump, bayan rabuwa da matarsa.

A cikin bidiyon an ga wani waje da Trump ke rawa yayin da wasu ƴanmata ke zagaye da shi.

NBC ta ruwaito cewa ƴanmatan magoya bayan ƙungiyar Buffalo Bills ne waɗanda suka je domin wasan da ƙungiyarsu za ta yi da Miami Dolphins.

Wasu hotuna da CNN ta samu sun nuna cewa Epstein ya halarci ɗaurin auren Trump da Maria Maples a 1993.

A 1999, an ɗauki hoton mutanen biyu suna tattaunawa a wani taro a birnin New York.

Akwai kuma hotunan Bill Clinton tare da Epstein tun daga farkon 1990.

A misali, a watan Satumban 1993, an ɗauki Epstein da Maxwell hoto suna tattaunawa da tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton a wajen wani taro a White House.

Rahotanni sun ce Eptein ya bayar da gudunmuwar $1,000 ga kwamitin neman zaɓen shugaba Clinton.

Daga 2000

Alaƙar Trump da Clinton da kuma Epstein ta ci gaba da gudana har aka shiga shekarar 2000.

Hotunan da jaridar Palm Beach Post ta Florida ta wallafa sun nuna Trump da Epstein da Ghislaine Maxwell da kuma yarima Andrew a wajen wani taron tattara gudunmuwar kuɗi a Mar-a-Lago, a cikin 2000.

Shekaru biyu bayan nan kuma, mujallar New York Magazine, ta ruwaito Trump na cewa Epstein "Mutum ne mai daraja" kuma ya ƙara da cewa "ana cewa yana son kyawawan mata kamar yadda nima nake so, kuma mafi yawan su matasa ne.''

A wannan lokacin ne kuma Clinton e tafiye-tafiye a jirgin saman Epstein.

Jim kaɗan bayan kama Epstein kan zargin lalata a watan Yulin 2019, kakakin Clinton ya wallafa sanarwa a shafin X cewa tsohon shugaban ƙasar ya yi tafiya har sau 4 a cikin jirgin Epstein tsakanin 2002 da 2003.

A wata maƙala da ta wallafa a 2002, New York Magazine, Kakakin Clinton ya ce "Clinton na godiya ga gudunmuwar Epstein a aikin da gudauniyarsa ke yi a Afirika a fannin bunƙasa dimokuraɗiyya da ƙarfafa masu ƙaramin ƙarfi da wayar da kan mutane da kuma yaƙi da cutar HIV/AIDS."

Rahotanni sun ce Trump da Clinton duk sun bayar da gudunmuwa, tare da wasu mutane 50 wajen wallafa littafin cikar Jeffrey Epstein shekara 50 da haihuwa a 2003.

A farkon wannan shekarar, jaridar Wall Street Journal (WSJ) ta wallafa wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun da ake zaton na Trump ne wadda ke da zanen wata mace tsirara, a saman zanen kuma an rubuta: "Barka da zagayowar ranar haihuwar ka - kuma ina fatan ka kasance cikin aminci da rufin asiri a kowacce rana."

Trump ya musanta rubuta wasiƙar, kuma ya maka jaridar WSJ a kotu yana neman a biya shi diyyar ɓata suna. Ya shaidawa ABC cewa "Ba sanya hannu na bane wannan, kuma ba yadda nake rubutu kenan ba. Duk wanda ya san ni a lokaci mai tsawo ya san ba haka nake aikewa da saƙo ba.

Bayan kama Epstein a 2019, Trump ya ce ''Na raba gari da shi tuntuni. Bana tunanin na yi magana da shi a shekaru 15 da suka gabata.'' Wannan na alamta cewa daga 2004 suka yanke alaƙa da juna.

A 2025, Trump ya shaidawa manema labarai a Scotland cewa ya kori Epstein daga Mar-a-Lago saboda ya "sace" ma'aikatansa,''

"Na gargaɗe shi kada ya sake. Ya sake yi, don haka na kore shi,'' in ji Trump.

Kakakin Clinton ya fadi a 2019 cewa tsohon shugaban ƙasar ya shafe shekara goma bai yi magana da Epstein ba.

A labarin da ya wallafa a bara, Clinton ya ce baya da masaniya kan irin laifin da Epstein ya aikata. Ya ƙara da cewa ''da aka kama shi a 2005, na riga na raba gari da shi.''

A 2008 aka fara yankewa Epstein hukunci. Jim kaɗan bayan an tura shi gidan yari a 2019, ya kashe kansa a gidan yari.

BBC Verify ya tuntuɓi fadar White House da kuma ofishin Bill Clinton domin su yi martani.

Fadar White House ta bamu ansa cewa: "Shugaba Trump ya kasance mai bari a fitar da bayanai yadda suke ba tare da ɓoye komai ba, game da Epstein, kuma gwamnatinsa ta ansa kiran da ake yi na fitar da kundin bayanin binciken Epstein mai dubban shafuka, tana kuma gwamnatin Trump ta fi ta Democrats kula da waɗanda Epstein ya ci zarafi.''