Man City ta sayi Claudio Echeverri daga River Plate

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta ɗauki ɗan wasan Argentina ɗn ƙasa da shekara 17 Claudio Echeverri daga River Plate.
City za ta biya kimanin fan miliyan 12.5 kan ɗan wasan, wanda ya sanya hannu kan kwantaragin shekara hudu da rabi wadda za ta ƙare a 2028.
Dan wasan mai shekara 18, wanda ya bugawa River Plate wasanni shida zai ci gaba da wasa a Argentina zuwa ƙarshen 2024.
Irin wannan yarjejeniya City ta cimma da River da ke Argentina kan Julian Alvarez a watan Janairun 2022.
Echeverri shi ne kyaftin ɗin Argentina na 'yan ƙasa da shekara 17 lokacin da aka yi gasar kofin duniya a watan Nuwamba, ya ci kwallo ukun da suka ci Brazil a wasan kusa da daf da na ƙarshe.
Ya kammala gasar da kwallo biyar, yayin da Argentina ta ƙare a matsayi na hudu bayan rashin nasarar da ta yi a wasan neman na uku.






