Gwamnoni na sace kudaden kananan hukumomi - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamanonin jihohin kasar na sace kason kudaden da ake tura wa kananan hukumomi duk wata daga asusun tarayya.
Shugaban ya yi wannan zargi ne a taron manyan jami'an gwamnati na wannan shekara, na cibiyar nazarin manufofi da dabaru ta kasa (NIPSS) da ke Kuru, a Jos.
A duk shekara dai masu yin kwas a cibiyar, sukan dauki wani muhimmin lamari da ya shafi kasa baki daya, su yi nazari game da shi, kuma a karshe su gabatar da sakamakon bincikensu da shawarwarinsu.
A bana sun duba batun mulkin kananan hukumomi ne bayan da Shugaban ya ba su umurnin gudanar da nazari a kan yadda ake gudanar da mulkin kananan hukumomi.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Mallam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa manyan jami'an gwamnatin sun kammala aikin nasu kuma sun bayar da shawarwari:
“ Muhimmai a ciki sun hada da rashin tsari na dimukraddiya”
Shugaba Buhari ya ce a yanzu haka jihohi 20 ne kawai suke da zababbun shugabannin kananan hukumomi da jama’a suka zaba.
Ya ce wasu mulki ake yi a karkashin kantoma wanda ba zababbe ba ne kamar yadda Garba Shehu ya bayyana.
''Wuraren da aka zabi shugabannin kananan hukumomi ba lallai ne a ce an rungumi al’umma na kananan hukumomin ana tafiya da su ba.'' Kamar yaddaya ce.
''Akwai rashawa da cin hanci, akwai kuma rashin fahimtar aiki, akwai rashin kwarewa na ma’aikata, akwai rashin kudi da za a yi aiki da shi” in ji shi.
Shugaba Buhari ya danganta rashin kudin aiki a kan wasu jihohi da ke facaka da kudi.
Ya kuma yi ikirarin cewa akwai 'wata jiha da ya san cewa akwai gwamnan da za a ba naira miliyan dari, na karamar hukuma ya raba gida biyu, ya rike rabi.'
Mafita
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugaba Buhari ya ce ya zama dole ne a tashi tsaye a kawo gyara a cikin kasar domin magance wannan matsala.
Ya ce duk wani matakin da za a dauka ya dogara ne a kan abin da zai biyo baya.
‘’Su wadanda suka yi wannan nazari, akwai shawarwari mataki-mataki sun kai guda goma wadanda suka bayar wadanda ya kamata a yi , a cikinsu kuma har da gyara ga tsarin mulki.’’
‘’A kwato kananan hukumomin nan, a ba su 'yancin cin gashin kansu, su zamana suna samun kudinsu, su zauna da al'umomi da ke karkashinsu, su yi shawara yadda za su kashe kudaden, amma ba a ce an aiko da shi ta hannun wani jami'i ko kuma wani gwamna ba'' in ji kakakin na Buhari.
Sai dai ana fargabar cewa duk wani mataki da za a dauka yanzu ba zai yi tasiri ba yayin da kasa da wata 6 ya rage wa Shugaba Buhari a kan mulki.
Ko-da-yake mai magana da yawun Shugaban ya ce shawarwarin da za a dauka mataki-mataki ne.
Saboda akwai wadanda aka ce a dauka nan da watanni uku na farko na sabuwar shekara.
Akwai kuma wanda za a dauka bayan watanni shida da shiga sabuwar shekara da karshen shekara.
Garba Shehu ya ce fatan gwamnatin kasar shi ne a ce za a shawo kan matsalar sannu a hankali.











