Abin da aka tattauna a taron shugaba Buhari da manyan jami’an tsaro

Asalin hoton, STATE HOUSE
A yau Litinin ne shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya gana da manyan hafsoshin tsaro na ƙasar a fadarsa da ke Abuja.
Tattaunawar da shugaban ya kira cikin gaggawa ta mayar da hankali ne kan barazanar tsaro da ke ci gaba da tayar da hankalin al’umma, musamman a babban birnin ƙasar.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro Babagana Monguno, da shugaban hafsan hafsoshin Najeriya General Lucky Eluonye Irabor, da shugaban hukumar tsaron cikin gida Yusuf Magaji Bichi, da kuma ministan harkokin waje na Najeriya Geoffrey Onyeama, ne suka gana da manema labaru bayan tattaunawar.
Muhimman abubuwan da suka faɗa a bayan taron su ne...
- Jami’an tsaron Najeriya na sane da duk wani abu da ke faruwa a ƙasar, kuma suna yin bakin ƙoƙarinsu wajen shawo kan duk wata matsala.
- An kama mutane da dama a cikin kwana bakwai zuwa goma da suka gabata waɗanda ake zargin su da yin zagon ƙasa ga harkar tsaron ƙasar.
- An tabbatar da harin da ake zargin wasu ƴan ta’adda ne suka yi yunƙurin kai wa a kan wani barikin soji da ke jihar Neja.
Abin da ya sa shugaba Buhari ya kira taron gaggawa da jami'an tsaro
A kwanakin da suka gabata ne manyan ƙasashe kamar Amurka, da Birtaniya, da Canada suka gargaɗi ƴan kasarsu da su yi taka-tsantsan saboda sun samu bayanan da ke cewa za a kai hare-hare a ƙasar, musamman ma a Abuja, babban birnin ƙasar.
Ƙasar Amurka a nata ɓangaren ta buƙaci ma’aikatan ofishin jakadancin ƙasar a Najeriya su fice daga Abuja.
Koda yake fadar shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari ta fitar da sanarwa, inda ta buƙaci al’ummar ƙasar da su kwantar da hankalinsu.
Kowa ya kasance cikin shiri amma a kwantar da hankula - Shugaba Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shawarci hukumoin tsaron ƙasar da dukkan al’umma da su ci gaba da yin taka tsantsan da kula kan sha’anin tsaro, amma kuma ya ce yana da matuƙar muhimmanci a guji tayar da hankula.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar a yau Juma’a, shugaban ya nemi ƴan ƙasar da su kwantar da hankali. “Sabbin matakan barin ƙasar da Amurka da Birtaniya ke ɗauka ba za su zama dalilan tayar da hankali ba.”
“Najeriya ba ita kaɗai ce ƙasashen duniya ke bai yi wa gargadi kan barazanar ta’addanci da kuma bai wa ƴan ƙasashensu shawarar tafiye-tafiye ba.
“Abin takaici ne cewa batun ta’addanci ya mamaye duniya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa sai dai gargaɗin ba yana nufin lallai za a kai hare-haren ba, don tun bayan harin daka kai gidan yarin Kuje an sake tsaurara tsaro a ciki da wajen Abuja.
“An daƙile hare-hare. Jami’an tsaro ne bankaɗo barazanar da ake fuskanta don tsaron ƴan ƙasa – sai dai mafi yawan ayyukansu ba a gani saboda ana buƙatar sirri.
“Zaman lafiyar ƴan Najeriya shi ne mafi ƙololuwar burin gwamnati. Jami’an tsaro na aiki babu dare babu rana,” in ji sanarwar.
Kazalika shugaban ƙasar ya bayar da tabbacin cewa gwamnati na bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da tsaro.










