Fina-finan Kannywood mafiya shahara a 2023

Kannywood actors

Asalin hoton, AMINU SAIRA/FACEBOOK

    • Marubuci, Daga Muhsin Ibrahim & Habibu Ma’aruf
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, .

Yayin da 2023 ta yi ban kwana, wani babban abin takaici da koma-baya da ya faru a shekarar, shi ne kulle babbar sinimar 'FilmHouse' a Kano.

Hakan ya jawo ƙarancin fina-finai falan-ɗaya, kuma ya durƙusar da fitar da su a sinima daga masana'antar Kannywood.

Sai dai duk da wannan koma-bayan, an samu gagarumin sauyi ta fannin fina-finai masu dogon Zango, inda manyan daraktoci da kuma furodusoshi suka ci gaba da tsunduma fagen shirya su.

Daga kan 'Labarina' da 'Alaqa' da ‘Manyan Mata’, zuwa 'Fatake' mu je ga 'Amaryar Tiktok' da ‘Kishiyata’ da kuma ‘Dan Jarida’, da sauran su, fina-finan masu dogon zango sun nishaɗantar da yan kallo a 2023.

Yayin da wasu masu sharhin ke ganin da yawan fina-finai masu dogon zango, kwashi-kwaraf ne kawai babu inganci, amma dai waɗannan bakwai sun fita zakka, kuma suna da inganci daidai gwargwado.

Ba dukkansu ne aka fara a 2023 ba, amma duka sun yi tasiri a cikin shekarar.

Ga yadda jerin fina-finan ya kasance a cikin shekarar gwargwadon nazarin da muka yi:

1. Labarina

A Kannywood film cover

Asalin hoton, AMINU SAIRA/FACEBOOK

Wannan fim, ba ya buƙatar gabatarwa saboda yadda ya yi fice a tsakanin masu sha'awar kallon fina-finan Hausa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Duk da an fara shi tun cikin 2020, Zango na 7 da na 8 da suka fita a baya-bayan nan, sun ci gaba da samun karɓuwa sosai a 2023.

Labarin ne da ya fara da rayuwar wata zankaɗeɗiyar budurwa mai suna Sumayya (Nafisa Abdullahi/Fati Washa).

Tun tana yar talaka futuk, har Allah ya ɗaukaka ta, ta zama babbar mawaƙiya cikin dambarwar soyayyarta da Mahmoud (Nuhu Abdullahi), Lukuman (Yusuf Saseen), da Presido (Isah Feroz Khan).

Labarin ya kuma gabatar da wasu yan wasa ƙwararru masu matuƙar burgewa irin su Baba Ɗan Audu da abokinsa Rabe, Ummi Ƙarama mai son maso wani, Raba-Gardama, da dai sauransu.

Duk da dai ya samu tsaiko na ɗan wani lokaci, shirin ya dawo da ƙarfinsa bayan ya canza salo zuwa sabon labari mai ɗaukar hankali tare da sabbin yan wasa.

Aminu Saira ne ya bada umarni, yayin da Naziru Sarkin Waka shi ne furodusa.

Sauran jaruman sun haɗar da Teema Yola, Sadiq Sani Sadiq, Fatima Hussain, Amina Rani, da dai sauransu.

Fim ne da a yanzu haka masu kallo suka cika da shauƙi da zumuɗin son ganin abin da zai faru a cikin kashi na gaba, saboda ƙayatarwarsa.

A Kannywood actor

Asalin hoton, ALI NUHU/FACEBOOK

2. Alaqa

Alaqa, fim ne na Kamfanin FKD, wanda Ali Nuhu da kansa ya ba da umarni, kuma shi ma yana jan hankalin da yawan yan kallo.

Hakan ya faru ne saboda zaren labarinsa mai riƙe tunani, wanda duk mako yake barin masu kallo suna ɗokin jiran fitowar kashi na gaba.

Shirin ya bibiyi labarin wani hamshaƙin ahali ne na Alhaji Saleh Alfindiki (Tahir Fagge), wanda ke fama da rashin jituwar cikin gida da ta wurin aiki.

Labarin ya kuma nuna tsohuwar gabar da ke tsakaninsu da ahalin wani babban ɗan adawa, wanda ɗansa Audu Luluwa (Sadiq Ahmad) ya karɓa.

Alhaji Saleh Alfindiki na da burin suna da kimar ahalinsa su wanzu har bayan ransa ta ɓangaren ‘ya’yansa maza; Nameer (Ramadan Booth) da Hisham (Shamsu Dan Iya).

Sai dai kuma yayin da Nameer ya kasance mai nutsuwa, shi Hisham ba shi da halin kirki. Don haka Audu Luluwa yake son amfani da raunin Hisham, abin ya janyo rikici.

Labarin fim ɗin ya yi matuƙar tsaruwa, kuma ya samu ingancin aiki.

Hotunansa sun fita tarwai. Kuma wuraren ɗaukarsa, suturun da aka sanya, tare da yadda ƴan wasan suka taka rawa masha-Allah duk suna da ban sha'awa.

Sauran jaruman fim ɗin sun haɗa da Zikrullah Abubakar, Auwal Isah West, Teema Makamashi, Mommy Gombe, da dai sauransu.

3. Manyan Mata

Hausa film foster

Asalin hoton, ABDUL_AMART/SOCIAL MEDIA

Fim ɗin Manyan Mata, yana ɗaukar hankalin ‘yan kallo ainun.

Sadiq N. Mafia ne ya ba da umarni, sai Abdul Amart ya samar da shi (wato furodusa).

Manyan Mata wasan kwaikwayo ne da ya shafi al'umma musamman a kan 'yancin ɗan'adam, ƙarfafa gwiwar yara da mata, kuma yana fito da matsalolin da talauci kan jawo da ma halin ni-’ya-su da wasu mata ‘yan gudun hijira ke ciki.

An fara nuna shi ranar 4 ga watan Fabrairu, 2023, kuma tun daga lokacin ne ya samu karɓuwa sosai.

Shirin ya yi amfani da tsayayyen tsari wajen nuna barazanar Almajirci, halin ko-in-kula daga iyaye, da cin zarafin yara da mata.

Ta hanyar matsayin da Hadiza Gabon ta fito, shirin ya jaddada muhimmancin ilmin 'ya'ya mata da kuma cibiyoyi irin su 'Manyan Mata Foundation' wajen tallafawa al'umma game da al'amuran zamantakewa.

Shirin ya ƙunshi dukkan manyan jaruman Kannywood kamar su Ali Nuhu, Rabi’u Rikadawa, Adam A. Zango, Sadiq Sani Sadiq, Jamila Nagudu, Hadiza Gabon, Mommy Gombe, Aisha Humaira, da dai sauransu.

4. Fatake

Fatake, ba shakka yana cikin jerin fina-finai mafi zarra a shekarar da ta bankwana.

Shirin ya zo wa Kannywood da muhimmin ci gaba, kasancewar sa fim mai dogon zango na farko da aka ɗauka a wasu ƙasashen Afirka, tare da nuna hadin gwiwar taurarin Najeriya da Ghana da kuma Nijar.

Fatake labarin soyayya ne da ya ta'allaƙa a kan Fatima (Amina Umar), wata budurwa 'yar Ghana da ke fama da rikicin asali, yayin da maza da yawa ke neman aurenta.

Babu shakka, fim ɗin yana burge ‘yan kallo matuƙa.

An samar da shi cike da fasaha tare da tsaida hankali a kan inganci maimakon ƙyale-ƙyale maras ma‘ana. Don haka, karɓuwarsa wajen 'yan kallo bai zo da mamaki ba.

Dukkan jaruman shirin kuma sun yi rawar gani sosai, musamman ‘yar Ghana kuma sabuwar fuska, Amina Umar, wadda take taka rawar Fatima da cikakkiyar ƙwarewa.

Mun yaba wa darakta, Yaseen Auwal da furodusa, Umar UK, tare da sauran ma'aikatan shirin baki ɗaya.

5. Zaman Aure; Amaryar TikTok

A Kannywood actor

Asalin hoton, HUMAIRA AMARYAR TIKTOK/FACEBOOK

Wannan mashahurin wasan kwaikwayo na iyali, shi ma ɗaya ne daga cikin jerin fitattun fina-finan Kannywood na 2023.

Fim ne a kan manyan al'amuran da ke haifar da ƙalubalen aure a yau.

Labarin ya ta'allaƙa ne a kan Sule (Ahmad A. Bifa) da Humaira (Aisha Usman). Sun yi aure, amma suna da bambancin fahimtar rayuwa.

Da farko Sule ya yi adawa da TikTok da matarsa take yi; sannan ya yi adawa da barin ta ta yi aiki, wanda hakan ya haifar da dagulewa a zaman aurensu.

Fim ɗin yana da matuƙar ma'ana tare da kyakkyawan jigo.

Ya nuna sarƙaƙiyar rayuwa irin wadda akan fuskanta tsakanin miji da mata, tare da binciko abubuwan da sukan sa maza su ƙara aure.

‘Yan wasan sun ƙara masa ban sha'awa ta hanyar taka rawar tamkar gaske.

Amryar Tiktok

Asalin hoton, Ahmed Bifa

Fim ɗin ya samu karɓuwa kamar yadda muka faɗa, kuma yadda ake tururuwar kallonsa a YouTube ne ya ba shi cancantar kasancewa cikin wannan jerin.

Babban jarumin fim din, Ahmad A. Bifa, ne yake shirya shi, kuma shi ne ya ba da umarni.

6. Kishiyata

Hassan Giggs ne ya ba da umarnin wannan fim da aka fara a 2022 wanda kuma ya ci gaba da jan zarensa da kuma tashe har a shekarar da ta yi bankwana.

Hakan ya jawo wa shirin kasancewa a jerin fina-finan da suka fi shahara.

Kamar yadda sunansa ya nuna, fim ɗin Kishiyata ya ƙunshi yadda ake zazzafan kishi a gidaje a ƙalla uku, waɗanda kuma duk matan ke zuwa wurin boka don yin galaba kan kishiyarsu ko samun karɓuwa a wajen mazajensu.

Akwai dirama da jimirɗa ta yadda ‘yan kallo ba su zata ba.

Wannan kuwa ya jawo wa shirin masu kallo, musamman a tsakanin mata. Misali, akwai mutumin da ya aure matar da surukinsa ya saka!

Ana yawan tattauna abubuwan da suka faru a fim ɗin a kafafen sada zumunta, wanda hakan ya zama wani ƙarin ma’auni na tantance shahara ko akasin haka ga fina-finai a wannan zamanin.

‘Yan wasa sanannu irin su Lawan Ahmad da Tijjani Faraga da Maryam CTV, da irin su Maryam Muhammad (Malika) da Samha M. Inuwa ne suke taka rawa mai ƙayatarwa a cikinsa.

7. Dan Jarida

A Kannywood film cover

Asalin hoton, DAN JARIDA SERIES/FACEBOOK

Fim ɗin Ɗan Jarida wanda Bashir Maishadda ya ƙirƙira, ya samu ba da umarnin tsohuwar zuma Hafizu Bello “King of Kannywood Box Office”.

Shirin ya yi ƙoƙarin fitowa da ‘yan kallo yadda wasu ‘yan siyasa marasa gaskiya ke yin duk yadda za su yi a gwagwarmayar neman mulki.

Hakan kuwa ya haɗar da ba da cin hanci, azabtarwa da ma aikata kisan kai ɗungurungum musamman ga ‘yan adawa da ‘yan ba-ruwana.

Ɗan Jarida ya haɗa taurari manya da ƙanana, sabbi da tsoffi, shahararru da masu tasowa na Kannywood.

Duk da irin yadda aka yi ta nuna abubuwan da suka faru a baya zai iya rikita masu kallo, fim ɗin ya yi tashe sosai saboda waɗancan yan fim da ya haɗa. Kuma an kashe kuɗaɗe masu yawa wajen ɗaukar sa.

Dadin daɗawa ma, fim ɗin ya sha talla daga masu taka rawa a cikinsa da ma wasu da yawa cikin magoya bayan Kannywood.

‘Yan wasan ciki sun haɗar da Sha’aibu Lawan (Kumurci), Tijjani Asase, Daddy Hikima, Aisha Humaira, da dai sauran su.