Waƙoƙin Hausa 10 da suka fi fice a 2023

A Kannywood actor

Asalin hoton, Umar M Shareef/Youtube

    • Marubuci, Daga Ibrahim Sheme da Abba Muhammad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, .

A kullum, idan aka ce fitattun waƙoƙin Hausa na shekara, ana nufin waƙoƙin da aka fi saurare a kafafen yaɗa labarai kamar rediyo, talbijin da soshiyal midiya.

Sauyawar zamani ya sanya waɗannan waƙoƙin su ne na zamani da ake buga su a situdiyo da kiɗan fiyano ko haɗin fiyanon da kalangu, ba na gargajiya irin na su Shata da Ɗanƙwairo ba.

A 2023 ma, kamar kowace shekara a wannan zamanin, waƙoƙin fiyano su ne aka fi saurare a kafafen yaɗa labarai. A binciken da muka yi, mun gano cewa a bana waƙoƙin soyayya ne suka mamaye fagen, kuma maza ne suka riƙe kambin a cikin waƙoƙi guda 10 mafi fice da aka samar.

Ga su kamar haka:

Bayanan bidiyo, Waƙoƙin Hausa 5 da suka fi fice a 2023

1. Sauti – Ado Isah Gwanja

A Kannywood artist

Asalin hoton, ADO GWANJA

‘Sauti’ waƙa ce a jerin salon waƙoƙin da Ado Isah Gwanja yake yi a yanzu, wanda kusan ita ce ta biyar a cikin irin wannan waƙoƙi na salon habaici, tun daga kan waƙoƙin ‘Warr’, ‘Cass’, ‘Iye’, ‘Luwai’, sai kuma ita ‘Sauti’.

A cikin duk waɗannan waƙoƙin, ‘Warr’ da ‘Cass’ sun yi fice a shekarar da ta gabata.

Musamman ganin mawaƙin ya zo da sabon salo, wannan ya sa jama’a suka so waƙoƙin, wanda har sai da ta kai an hana saka waƙoƙin a gidajen rediyo, wasu lauyoyi suka yi ƙarar mawaƙin a kotu.

Amma kuma sai ya zama kai ka ce an ƙara wa Gwanja fiƙira ne, domin kuwa ya ci gaba da sako irin waɗannan waƙoƙin, har zuwa wannan mai suna ‘Sauti’, wadda yanzu watan ta uku da saki.

Baitin da ya ɗauki hankalin jama’a, ya yi yawo musamman a TikTok, wanda a yanzu a can ake baza waƙoƙi, shi ne:

‘Turmi ya cashi tsaki, a banza, a banzazza!

Talaka ya girmi sarki, a banza, a banzazza!

Kaska ta zagi kifi, a banza, a banzazza!

Ɗaki babu murfi, a banza, a banzazza!

Barazana babu ƙarfi, a banza, a banzazza!"

2. Rayuwa Ta – Umar M. Shareef da Zubaida Mu’azu

Kannywood artist

Asalin hoton, UMAR M.SHARIFF

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rayuwata, waƙa ce ta soyayya tsakanin saurayi da budurwa. A cikin ta, gwanayen mawaƙan nan Umar M. Shareef da Zubaida Mu’azu sun nuna ƙwarewa wajen karya murya da kuma zuba kalmomi na shauƙi.

Waƙar ta yi fice a soshiyal midiya, musamman a TikTok, inda za ka ga budurwa ta ɗauki bidiyon kanta, ta kuma saka hoton masoyinta a jiki tana bin kalaman da mawaƙan suke rerawa tare da nuna shauƙin soyayya.

Baitin da ya kama zuciyar masoya a waƙar shi ne:

"Na samo yarinya kyakkyawa,

kun gan ta son kowa, ta sa min jin daɗi.

In ta fito, kowa na rububi gun kallonta ya yi ta rawa a jikinsu suna kauɗi".

Ita ma macen sai ta maimaita abin da namijin ya faɗa.

Sai ya ƙara da cewa:

"Da Turanci in zan kira ki, darling tsarina,

da Larabci ƙurratu ainun, sanyi na idona,

Faransanci monafur, shi ne zaɓina,

kin zarce yadda suke tunani a cikin raina."

Ita kuma sai ta ce:

"Da Turanci in zan kira ka, Babyna,

da Larabci kuma sannu nurul ƙalbina,

Faransanci masheri, abin ƙauna,

ka zarce yadda ake tunani a cikin rai na."

Wan mawaƙin, wato jarumi Abdul M. Shareef, da jaruma Maryam Malika ne suka yi bidiyon waƙar.

3. Aisha – Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) da Zuwaira Isma’il

A Kannywood artist

Asalin hoton, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu

Waƙar ‘A’isha’, an saka ta ne a fim ɗin ‘A Cikin Biyu’ na jaruma A’isha Ahmad Idris (A'ishatulhumaira).

Sanannen mawaƙin siyasa, Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) ne ya rera ta tare da fitacciyar zabiya Zuwaira Isma’il.

Mawaƙin ya yi wa mutane bazata domin ba a taɓa jin waƙar soyayya daga wurin sa ba sai a wannan karon. Waƙar ta ɗauki hankalin mutane sosai, har ta kai ana yaɗa ji-ta-ji-tar zai auri A’isha Humaira ne, wadda tana ɗaya daga cikin manyan muƙarrabansa a Kannywood.

A waƙar, Rarara ya zo da wani salo da ya sha bambanta da sauran waƙoƙin soyayya.

Ya yi amfani da kalamai masu ratsa zuciyar duk wata mace da ke cikin shauƙin soyayya.

Waƙar ta yaɗu a soshiyal midiya, musamman a lokacin da ake ɗaukar fim ɗin ‘A Cikin Biyu’ a Jihar Jigawa. Jaruman fim ɗin su ne Ali Nuhu, Adam A. Zango da ita A’ishatulhumaira.

4. Halitta – Nazifi Asnanic

Halitta, waƙar soyayya ce inda mawaƙin ke siffanta halittar masoyiyarsa.

Nazifi Asnanic ya gigita masoyan zamani da wannan waƙa.

Ya yi amfani da kalmomi masu cafke zuciya ta yadda duk macen da take cikin nishaɗi irin na soyayya sai ta ji kamar ita ake furta wa kalaman da take saurare daga bakin mawaƙin.

Nazifi ya ƙalubalanci abokansa mawaƙa a kan wannan waƙa, inda ya yanki amshin waƙar da baiti ɗaya, daga nan kuma sai duk wanda zai yi baitinsa, sai ya ɗauka shi ma ya yi, sai ya ɗora a soshiyal midiya.

Manyan mawaƙa da ƙanana sun yi. Wannan ya ƙara fitar da waƙar, ta yaɗu sosai.

5. Farin Ciki Na – Auta Waziri da Shamsiyya Sadi

A Kannywood artist

Asalin hoton, AUTA WAZIRI

Ita ma 'Farin CikiNa' waƙar soyayya ce.

Mawaƙan sun yi amfani da kalmomi masu taɓa zukatan matasa matuƙa. Waƙar ta yi fice sosai, kuma ta yi tasiri musamman a wajen masoya.

Duk inda ka shiga a soshiyal midiya za ka ga maza da mata suna amfani da ita, saboda kalaman da aka yi amfani da su.

Auta ba sabon mawaƙi ba ne, amma yana ɗaya daga cikin masu tashe a yau.

A baya waƙoƙin sarauta da siyasa da ire-irensu ya fi mayar da hankali a kai, amma sai ya rikiɗe ya koma waƙoƙin soyayya.

6. Chiza Dani Na – Abdul D. One da Shamsiyya Sadi

Chiza Dani Na, waƙa ce tsakanin saurayi da budurwa wadda Abdul D. One ya shirya sannan ya rera.

A cikin ta, fasihan mawaƙa (Abdul D. One da Shamsiyya Sadi) sun nuna ƙwarewa wajen zuba kalmomin soyayya da shauƙi.

Sai dai kuma mawaƙan sun yi waƙar da wani salo ne, inda namiji ya yi tasa daban, mace ma, ta yi tata daban (da Ingilishi 'male version' da 'female version').

A ɓangaren macen, Ali Nuhu da wata sabuwar jaruma mai suna Rabi’a ne suka hau waƙar.

Bidiyon waƙar ya ƙayatar, musamman irin yadda aka shirya shi, tsarin dandalin da kuma furucin da aka yi amfani da su. Bidiyon shi ya ƙara sanya waƙar ta yaɗu da kuma shi kansa Ali Nuhu.

A nasa ɓangaren, Abdul D. One ya yi bidiyon waƙar ne da jaruma Humaira Dawaki.

7. Alƙawari – Hamisu Breaker Ɗorayi da Shamsiyya Sadi

A Kannywood artist

Asalin hoton, Hamisu Breaker Ɗorayi

Waƙar 'Alƙawari' ta soyayya ce.

Mawaƙan sun zazzaga kalaman soyayya da ke nuni da cewar so da ƙauna ya kama zukatansu ta yadda ba sa iya rabuwa da juna.

Waƙar ta yi tasiri a wajen masoya. Ga duk waɗanda suke sauraren waƙar, in har ka fahimci kalaman mawaƙan za ka samu sanyin zuciya da ƙwarin gwiwa a kan soyayyarka.

A bidiyon waƙar, an nuna iyayen yarinyar ba sa son Hamisu Breaker saboda kasancewarsa mawaƙi.

Duk da haka bai karaya ba, har sai da mahaifin yarinyar ya saka gasar kokawa tsakanin sa da wani, kuma ya sha kaye. Saboda nuna nacin sa, haka nan iyayen suka haƙura suka ba shi ita.

Da ma kuma a cikin waƙar akwai kalaman alƙawari da suke furta wa junansu.

8. Soyayya Ba Faɗa Ba Ne – Auta MG Boy da Hajara S. Umar

A Kannywood artist

Asalin hoton, AUTA M.G

Jigon wannan waƙar shi ne soyayya.

Mawaƙan suna magana ne a kan irin yadda ake samun matsaloli a soyayya. To amma kuma soyayya ba faɗa ba ce kamar yadda mawaƙan suka bayyana a waƙar.

Sannan suka ce ba kuɗi ba ne soyayya, ba rashin faɗa ba ne soyayya, ba kyawu ba ne soyayya, shi fa ba ado ba ne soyayya, ba kuma abin gudu ba ne soyayya. Mawaƙin ya kawo wasu daga cikin matsalolin da ake samu a soyayya.

Baitin da ya fi ɗaukar hankalin mutane shi ne:

“In ka ji ƙauna maganar aure ce,

maganar so maganar baki ce,

a idanu ka ga so ƙarya ce,

a cikin zuciya ko ka zauce,

ka ji daɗi ya kamar ka dace,

yana nan da dafi soyayya."

Haka dai mawaƙin ya ci gaba da aika saƙo game da soyayya.

9. Ko Wuya Ko Daɗi – Sadiq Saleh da Fati Nijar

A Kannywood artist

Asalin hoton, SADIQ SALEH

Waƙar 'Ko Wuya Ko Daɗi' waƙa ce ta masoya masu matuƙar ƙaunar junan su.

Sadiq Saleh da fati Nijar sun zazzaga kalaman soyayya da duk wani masoyi - tsoho, matashi ko yaro - idan ya ji su, in dai yana soyayyar, sai ya ji mawaƙan sun gama masa komai a ɓangaren ɓarar da kalaman soyayya.

Waƙar ta ƙara tasiri ne musamman jin muryar fitacciyar mawaƙiya Fati Nijar a cikinta.

Kowa ya san irin ƙwarewarta a fannin waƙoƙin soyayya. Hakan ta sa masoyanta suka yi farin ciki da sake jin muryarta a yanzu. Waƙar ta tsaru, kuma ta mori kalaman soyayya.

10. Sa Ido – DJ AB 'Sa Ido'

Waƙar 'Sa Ido' ta DJ AB ce kan gaba a bana cikin rukunin waƙoƙin gambara na hip-hop.

Mawaƙin ya yi waƙar ne a kan ‘yan sa ido, inda yake faɗin cewa an sa masa ido. Ya kuma ce maganganu sun yi yawa.

Ya kuma ce haka za su yi ta yi, har su gaji.

Tsawon shekara uku zuwa biyar, DJ AB ne mawaƙin hip-hop ɗin da in ya yi waƙa a arewacin Najeriya take karaɗe lungu da saƙon lardin.

DJ AB, wanda asalin sunansa Haruna Abdullahi, ɗa ne ga tsohon Shugaban Ƙungiyar Furodusoshi ta Jihar Kaduna, wato Alhaji Abdullahi Sa'id Bello mai kamfanin MDC Production da ke Kabala Costain, Kaduna.

Mahaifin nasa ya taimaka wajen samun gogewa a harkar waƙa tun yana ƙarami.