Soludo ya ta da ƙura game da ikirarin Peter Obi na zuba jari a Anambra

Asalin hoton, Soludo Facebook
Kalaman da gwamnan jihar Anambra Chukwuma Soludo ya yi kan ɗan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar Labour Peter Obi sun tayar da ƙura da muhawara musamman a kafofin sada zumunta na ƙasar.
Soludon dai ya yi maratani ne a kan ikirarin da Mista Obi ke yawan yi a wuraren yaƙin neman zaɓensa inda yake kafa hujja da ɗumbin zuba jarin da ya yi a jihar daga tsakanin shkarar 2006 to 2014 lokacin yana gwamna.
A wata hira da Soludo ya yi da gidan talabijin na Channels, ya ce, “Ban san da wani labarin zuba jari ba. Hirarmu a kan kasafin kudin 2023 ce.
“Ba zan yi magana a kan batun zuba jarin magabatana ba. Kuma ma ni ban san komai a kan shi wannan zuba jarin da ake magana akai ba,” in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa “Ina jin na karanta wania u a kan batun da wani ke yaɗawa kan zuba jari. Abin da nake gani a yau shi ne, waɗannan zuba jarin da ake magana ba su da wata daraja. Don haka a bar wannan batun a gefe."
Wadannan kalamai na hirar Soludo da Channels sun jawo ce-ce-ku-ce sosai musamman daga ƴan kudu maso gabashin ƙasar, wato yankin da Peter Obi da Soludo suka fito.
A shafin Tuwita dai an yi ta amfani da maudu’ai da suka haɗa da #Soludo sau fiye da 111,000 da #Obiano wato gwamnan Anambra da Soludo ya gada sau fiye da 34,000, da kuma #Anambra sau fiye da 80,000.
Masu tattaunawar sun rabu biyu, da masu goyon baya da jaddada kalaman Soludo da kuma masu kare Peter Obi.
Ga dai wasu daga cikin saƙonnin da muka gani a Tuwita.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Fearless@iamfearlessking ya rubuta cewa: "Idan wani ya ji yadda Soludo ke bayani a gidan talabijin na Channels, sai ya zaci shi ne ya gaji Peter Obi a kujerar gwamnan Anambra, bayan kuwa akwai ratar shekara takwas a tsakanin mulkinsu.
"To me ya sa Soludo ya fi yin kwatance da mulkin Peter Obi maimakon na gwamnan da ya gada?
End of Karin wasu labaran da za ku so ku karanta
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Wasu kuwa irin su Chukwuemerie Uduchukwu @EmerieUduchukwu kamar nuna goyon bayan gwamnansuka yi.
Ya ce: "Muna godiya mai girma Gwamna Charles Chukwuma Soludo!
"Obiano nake zargi da yin sunan da bai dace da shi ba kan batun Anambra a shafukan sada zumunta. Obiano ya kasa yin magana a kan farfagadnar yaudara ta Obi."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Wasu kuma da suke rugar tsakani irin su Ahmed Ibn Mustapha@MrAfobaje ga abin da suke cewa: "Ku ƴan Anambra ke ne masu ikirarin cancanta kawai kuke zaɓa. Go ga daidai cancantar taku da kuka zaɓa yana cewa wanda kuke ganin shi mai cetonku mazambaci ne.
"Yanzu Soludon bai cancanta ba kenan ko?"