'Babu inda za mu binne waɗanda suka mutu a hatsarin kwale-kwale, ko ina ruwa ne'

OGGOCHUKWU/ABS

Asalin hoton, OGGOCHUKWU/ABS

A ƙalla utum 76 ne aka bayar da rahoton mutuwarsu bayan afkuwar wani hatsarin kwale-kwale a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Kwale-kwalen, wanda ke ɗauke da mutum 80, ya kife ne a ranar Juma'a a yankin Ogbaru da ke jihar Anambran.

Mafi yawan wadanda abin ya rutsa da su mata ne da yara, da ke ƙoƙarin tsere wa yankinsu da ambliyar ruwa ta mamaye.

Wani mutum Benard Achonu ya shaida BBC cewa ya shiga cikin tashin hankali matuƙa: "Rayuwata ta jirkita," ya ce.

Mutumin mai shkeara 60 ya rasa matarsa da ƴaƴansa uku, ƴan tsakanin shekara biyu zuwa shida.

Suna daga cikin waɗanda ke ƙoƙarin yin ƙaura don guje wa yankin da ambaliyar ya shafa, in ji shi.

Shi ma wani da ya zauna a yankin a da, Precious Umeh, ya shaida sashen BBC Pidgin cewa yanayin mai munin ne.

Mutane da yawa da ƴan uwansu suka mutu a hatsarin ba su san yadda za su binne su ba, saboda babu wani busasshen waje, ko ina ruwa ya mamaye.

Kafafen yada labaran yankin sun ce jirgin ruwan yana kan hanyarsa ne ta zuwa kasuwar Nkwo a Ogbakuba kafin ya kife din.

Wasu jami'an sun ce injin jirgin ruwan ne ya lalace sai kuma ya ci karo da wata gada, kafin daga bisani ya kife.

Shugaban hukumar agaji ta gaggawa a yankin kudu maso gabas Thickman Tanimu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: "Ruwan ya yi yawa kuma yana da hatsari ta yadda ba za a iya aikin ceton yadda ya kamata ba.

Gwamnan Anambra Charles Soludo ya ƙara da cewa lamarin ya tayar da hankalin mazauna yankin da kuma gwamnatin jihar, inda ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mamatan.

Buhari ya jajanta

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin sake yin duba don inganta matakan kiyaye afkuwar haɗurra a tsarin sufurin ruwa na ƙasar, sakamakon hatsarin wani kwale-kwale da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane a jihar Anambra.

An samu rahotanni masu cin karo da juna kan ainihin yawan waɗanda abin ya rutsa da su a jihar da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Amma wata sanarwa da mai taimaka wa Buhari kan yada labarai ta ce, ana jiran bayanai har yanzu, sai dai hukumimin agaji sun tabbatar d acewa "yawan waɗanda suka mutu ya kai 76."

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Presidency

Shugaba Buhari ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan waɗanda abin ya rutsa da su, yana mai bayyana hatsarin a matsayin mummuna, sannan ya ƙara da cewa dole ne hukumomi su yi duk abin da ya dace don gano waɗanda har yanzu ba a gansu ba.

Kazalika shugaban ya bai wa hukumomin gwamnati umarnin sake yin nazari kan tsarin tabbatar da tsaro a sufurin jiragen ruwa da kwale-kwale don kare afkuwar irin hakan a gaba.

Ana yawan samun hatsarin kwale-kwale a Najeriya - inda a mafi yawan lokuta ake ɗora alhakin hakan kan ɗaukar mutanen da suka fi ƙarfin jirgin da sauran matsaloli.