Me ya sa ma'aurata ke ƙaurace wa juna a yanzu?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Fernanda Paúl
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Bincike ya nuna cewa duk abin ya fara ne bayan ɓarkewar annobar korona.
Cecilia tana kasa yin bacci sakamakon munsharin da mijinta ke yi, wanda hakan ya sa ta rinka tura mijin da nufin ko idan ya juya, munsharin zai tsaya.
Sai dai ƙoƙarinta ya ci tura, wanda hakan ya sa Cecilia mai shekaru 35 ta gaji inda daga ƙarshe ita da mijinta suka amince da su dinga kwana a ɗaki daban-daban.
"Ba na iya mai da hankali kan aikina, kullum a cikin gajiya nake, mutum zai iya jure munsharin da farko amma daga bisani, dole ne ya fara damun mutum kuma ya ji ya ishe shi." Cecilia ta fada wa BBC daga gidanta da ke London, inda ta zauna a shekaru da dama.
"Yanke shawarar kwana a ɗaki daban-daban bai zo mana da sauƙi ba, shawarar ta dan sa mana damuwa da farko, amma da muka gano muna iya bacci, shi ke nan sai murna." in ji Cecilia.
Cecilia da mijinta mai shekara 43 sun bayyana shawarar da suka yanke na kwana a ɗaki daban-daban a matsayin "ƙaurace wa juna"
"Kaurace wa juna a wannan bangaren na ɗan wucin gadi ne, amma ma'aurata sun gano cewa sun fi samun bacci me kyau idan suka kwana daban-daban," in ji Stephaine Collier, wata likitar ƙwaƙwalwa a asibitin McLean da ke Amurka.
"Yawanci dalilan da suke sa ma'aurata kwana a ɗaki daban-daban suna da alaƙa da kiwon lafiya da suka haɗa da munshari da magagin bacci ko kuma yawan tashi domin shiga banɗaki saboda haka ka ga suna yawan juye-juye da tashi sosai wanda hakan ke takura wa mata ko miji." In ji Collier.

Asalin hoton, Getty Images
Halayyar wadanda aka haifa a 1980 da 1990s
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A karshen shekarar da ta gabata, fitacciyar ‘yar wasan fina-finan Amurka Cameron Díaz ta fada wa kafar yada labarai ta Lipstick a shirinta na on Rim podcast cewa ita da mijinta suna kwana a ɗaki daban-daban.
"Kuma ina ganin ni da mijina muna buƙatar mu daidaita kwana a daki daban-daban," in ji ta.
Wanna fallasawar dai ta haifar da dubban martani a shafukan sada zumunta - kuma ta haifar da labarai daban-daban a kafafen yada labarai a kan ƴar fim din.
A cewar wani bincike na 2023 da Cibiyar Nazarin Magungunan Barci ta Amurka (AASM) ta yi, ta ce fiye da kashi uku na wadanda suka amsa a Amurka sun ba da rahoton barci lokaci-lokaci ko akai-akai a dakuna daban-daban saboda samun barci mai inganci.
Binciken ya nuna cewa nazarin ya kasance a tsakanin mutanen da aka haifa a shakarar 1980 da kuma karshen shekarar 1990" (wato mutane da ke da kimanin shekaru tsakanin 28 da 42), inda kusan rabinsu,wato kashi 43 cikin 100 suka amsa cewa ba sa barci a ɗaki ɗaya da abokan zamansu.
Binciken kuma ya nuna cewa a tsakanin mutane da aka haifa a shekarar 1965 da 1980, kaso 33 ne suka amsa cewa ba sa kwana a daƙi ɗaya da abokan zamansu, sai kuma waɗanda aka haifa a shekarar tsakanin 1997 da 2012, kashi 28 cikin 100 sun amsa cewa suna kwana ɗaki daban-daban da abokan zamansu.
Sai dai mutane da aka haifa a tsakanin shekarar 1946 da 1964, kashi 21 cikin 100 ne suka ce ba sa kwana da junansu a ɗaki ɗaya.
“Ko da yake ba a san ainihin dalilin da ya sa matasa suka fi yanke shawarar kwana a ɗaki daban-daban da junansu ba, akwai wani hasashe wanda na daya shi ne cewa akwai karancin kunya da ke tattare da tunanin yin barci a dakuna daban-daban, canji ne na al'ada, Suna tunanin: 'Idan suka yi bacci da kyau sun fi jin daɗi, toh, me zai hana hakan? in ji Dr Collier.

Asalin hoton, Getty Images
A cikin tarihi, wannan ra'ayin ya sauya.
Wasu masana tarihi sun ba da shawarar cewa “gado na aure” (ko gado biyu) ra’ayi ne na zamani kuma amfani da shi ya ƙaru sakamakon juyin-juya halin masana’antu da aka samu, lokacin da mutane suka je zama a wurare daban-daban.
Amma kafin karni na 19, ma'aurata sun saba kwana a daki daban-daban.
“Kuma mafi girman matakin zamantakewar al'umma a wancan lokacin shi ne yadda abokan zaman ke yi. Kuna iya ganin yadda ’yan sarauta suke kwana” in ji Pablo Brockmann, masanin ilimin ƙwararru a makarantar likitanci na Jami’ar Katolika ta Chile.
Amfanin kwanan ma'aurata a ɗaki daban-daban ?
Masana sun yarda cewa akwai fa'idodi da yawa ga ma'aurata waɗanda suka yanke shawarar yin barci a ɗaki daban-daban.
“Babbar fa'idar ita ce, suna iya haɓaka samun barci mai zurfi da iganci. Kuma samun kyakkyawan barci yana da mahimmanci don jin daɗin rayuwa gaba ɗaya, ”in ji Dokta Collier.
“Idan mutum ba ya iya yin barci, yana shafar komai a jikinsa. Ƙari ga haka, ana kuma iya samun saurin fushi kuma da rashin haƙuri. Har ma mutum zai iya samun wani nau'in damuwa," in ji ta.
Likitar ƙwaƙalwar ta yi imanin cewa “ƙauracewa juna wajen barci” na iya taimakawa wajen kiyaye dangantaka “mafi lafiya”.
"Mun san cewa ma'aurata, idan ba su huta sosai ba, suna iya ƙara yin gardama da juna, suna fushi kuma su daina jin tausayin juna," in ji ta.

Asalin hoton, Getty Images
Seema Khosla, masaniya ilimin huhu kuma mai magana da yawun AASM, ta yarda da wannan batu.
"Mun san cewa rashin bacci mara kyau na iya cutar da yanayin ku, kuma waɗanda ba sa samun bacci yadda ya kamata na iya yin gardama da abokan zamansu.
Ana iya samun wasu bacin rai ga mutumin da ke hana ɗaya bacci wanda zai iya yin tasiri ga dangantaka," in ji shi lokacin da AASM ta ƙaddamar da bincikenta kan "ƙauracewa juna wajen bacci".
"Samun kyakkyawan barcin dare yana da mahimmanci ga lafiya da farin ciki, don haka ba abin mamaki bane cewa wasu ma'auratan sun zaɓi su yi bacci a ɗakuna daban-daban don jin daɗin rayuwarsu baki ɗaya," in ji ta.
Ga Cecilia, bacci a wani ɗaki daban da abokin zamanta na yanzu "ya canza rayuwarta".
“Ya fi dadi. mutum na samun damar yin bacci mafi kyau, ko kuma samun ƙarin sarari a kan gado, mutum kuma na iya juyawa ba tare da damun wani ba..." in ji ta.
“Haka kuma, ba dole ba ne ka tashi a lokaci guda da abokin zamanka.
Illolin rashin kwanan ma'aurata tare
To, babban rashin amfanin shi a bayyane shine cewa hakan na buƙatar ƙarin gado kuma mai yiwuwa ƙarin ɗaki, don haka ga yawancin ma'aurata ba ma zaɓi ba ne.
Amma ko da mai yiyuwa ne, wannan shawarar kuma tana iya yin wasu munanan sakamako. Yawancin ma'aurata, in ji masana, suna damuwa game da rasa kusanci da juna.
"Ina tsammanin cewa a matakin dangantaka da mijina, wani abu ya canza," Cecilia ta yarda.
"Dangantaka da kusanci na wahala. Amma hakan ba ya wani tasirii. Ina tsammanin fa'idodin kwana a ɗakuna daban-daban sun fi girma, ”in ji ta.
Dokta Collier ta bayyana cewa ga ma'aikata, lokacin da suke hulɗa da abokan zamansu shine daidai lokacin kwanciya.
"Saboda haka, daya daga cikin mafita shi ne su inganta lokacin da suke tare," in ji ta.
Tsarin ba ga kowa yake aiki ba
Dr Brockmann, a halin da ake ciki, ya ce ƙwanan ma'aurata a ɗakuna daban-daban ba ya aiki ga dukkan ma'aurata.
“Akwai wasu fa'idojin ilimin halitta na yin barci tare a matsayin ma'aurata. Ga mutane da yawa, ana haifar da ƙarin kusanci da danƙon soyayya. Wannan kuma shi ne abu na farko a cikin nau'in ɗan adam.
Uwa da ɗanta, alal misali, yawanci suna haifar da wannan kusanci da ƙarin soyayya yayin shayarwa kuma suna da yanayin barci iri ɗaya.
“Akwai binciken da ya nuna cewa akwai ma’auratan da suka shafe shekaru suna kwana tare da su kan ƙara zurfafa matakan barcinsu tun lokacin da suka yi aure."in ji masanin ilimin soso.
Duk da haka, idan ma'aurata sun yanke shawarar gwada "barci a daki daban-daban", akwai wasu shawarwarin da ya kamata su bi, in ji kwararru.
"Idan mutum ɗaya ya yanke shawarar kwana a dakin daban ba tare da amincewar daya ba, hakan na iya haifar da fushi," in ji Dokta Collier.
Saboda haka dole ne ma'aurata su amince da shawarar a tsakaninsu kafin aiwatarwa.
A cikin Burtaniya, kungiyar Kula da yanayin barci ta al'ummar Kasa ta gano cewa a cikin 2020 kusan daya cikin shida na ma'auratan Buritaniya da ke zaune tare yanzu suna kwana a daban-daban - tare da kusan tara cikin 10, kaso 89 na yin hakan ne a cikin dakuna daban-daban
Wani bincike da kungiyar ta Barci ta yi a shekarar 2009 ya nuna cewa kasa da ma'aurata guda cikin 10 (kaso 7) suna da gadaje daban-daban. "Wannan yana nuna adadin barci daban-daban ya ninka sau biyu a cikin shekaru goma da suka gabata," in ji Hukumar Kula da yanayin bacci ta Kasa..
*Cecilia ba sunanta na gaskiya bane saboda wadda aka yi hira da ita ta gwammace kada ya bayyana ainihin sunanta.










