Illoli da alfanun kafa sansanin sojin Amurka a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Wasu cibiyoyi da manyan shugabanin arewacin Najeriya sun yi gargaɗin kada a bai wa Amurka da Faransa damar kafa sansanin soji a cikin ƙasar, bayan korar su da aka yi daga wasu ƙasashen Sahel.
Cikin wata wasiƙa da suka aika wa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da kuma shugabannin majalisar dokokin ƙasar, cibiyoyin da shugabannin sun ce kada gwamnatin Najeriyar ta bayar da kai bori ya hau.
A baya-bayan nan ne wasu ƙasashen yankin Sahel suka yanke alaƙarsu da ƙasashen yamma inda suka kori dakarunsu daga ƙasashensu tare da karkata alaƙarsu zuwa ga Rasha.
Tuni Faransa ta kwashe sojojinta kimanin 13,000 daga yankin Sahel yayin da a ɓangaren Amurka kuma, akwai sojojinta kimanin dubu ɗaya da har yanzu suke a Nijar sai dai bayanai daga Amurka na cewa suna son kwashe sojojin daga Nijar zuwa rundunarsu da ke kula da Afirka da matsuguninta ke Jamus.
A makonnin da suka gabata ne, ƙwararrun sojojin Rasha suka isa Nijar domin horas da sojojin ƙasar - wani abu da ke alamta cewa Nijar ta ƙulla yarjejeniyar tsaro da Rashar.
Cikin waɗanda suka sanya hannu a wasiƙar, akwai jami'i a Cibiyar bincike da raya dimokuraɗiyya, Farfesa Jibrin Ibrahim wanda ya ce tun "wurin wata bakwai zuwa takwas muna jin ƙishin-ƙishin cewa mutanen Amurka da Faransa sun nemi izini a bar su su kafa sansani na sojojinsu a Najeriya, yanzu maganar ta fara fitowa fili shi ne muka ce wannan hatsari ne zuwa ga ƙasarmu.
Ya bayyana cewa bai kamata a ce a bari sojojin Amurka da na Faransa su kafa sansani a Najeriya ba har ma su yi abin da suka ga dama kasancewar kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso sun fatattake su daga ƙasashensu.

'Babu taimakon da sojojin Amurka suka yi a ƙasashen Sahel'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Farfesa Jibrin Ibrahim ya ce bisa bayanai daga ƙasashen Sahel da suka kori sojojin Amurka da Faransa, babu taimakon da sojojin ƙasashen suka yi masu a yaƙi da ƙungiyoyin mayaƙa da suka addabe su.
"Kuma duk abin da za su [Amurka da Faransa] iya yi, su tabbatar da cewa duk ƙasashen duniya na ƙarƙashinsu za su yi, domin haka sun zo su mallake mu ne, kuma bai kamata mu mu yarda waɗannan ƙasashen su zo su mallake mu ba." in ji shi.
Ya bayyana cewa duk da Najeriya na da kyakkyawar alaƙa da Amurka da Faransa, amma Najeriya ƙasa ce mai cikakken iko a don haka "babu wani da zai zo daga waje ya ce don muna da alaƙa [a baya] dole ne mu bari su shigo da sojojinsu."
Jami'in ya ƙara da cewa wani ɓangare na yarjejeniyar da ƙasashen suke so a sa hannu a kai shi ne "duk wani laifi da sojojinsu suka yi wa ƴan Najeriya, ba za a iya tuhumarsu ba, za su zo ne da cikakken mulkin diflomasiyya da yake ba za ma a bari a ga abin da suke shigowa da shi ba, ba za a bari a shiga sansaninsu a ga abin da suke yi, wato kamar wata ƙasarsu ce za su kafa a nan."
Shi ma a nasa ɓangaren, lauya mai zaman kansa kuma mai sharhi kan al'amuran tsaro, Barista Bulama Bukarti, yana ganin idan har akwai tabbaci cewa akwai tattaunawa tsakanin gwamnatin Najeriya da takwarorinta na Amurka da Faransa game da kwaso sojojinsu daga Nijar zuwa Najeriya, bai kamata a yi haka ba.
Ya ce: "Sojojin Faransa sun kasance a Nijar har tsawon kimanin shekara 13 tun daga shekara ta 2012, na Amurka kuma sama da shekara biyar tun 2017 zuwa 2018."
Ya ce duk da waɗannan shekarun da suka yi a ƙasashen na Sahel, "ba za ka iya cewa ga wata gudummawa gwaggwaɓa ga ƙasar Nijar da kuma Sahel wajen yaƙar waɗannan ƙungiyoyi ba."
Ya kuma bayar da misali da kasancewar sojojin Amurka a Somaliya inda ya ce a nan ma ba za a iya nuna wata rawa da suka taka ba wajen yaƙar ƙungiyar al-shabab ba kuma suka janye ba tare da sun karya lagon ƙungiyar ba.
Barista Bukarti ya kuma yi bayani cewa samar da irin wannan sansanin sojoji a ƙasashen Afirka, dama ce gare su ta tattara bayanan sirri na tsaro da tattalin arziki su tura ƙasashensu.
Gajiyar da Najeriya za ta iya ci daga sojin Amurka
A cewar Barista Bukarti, akwai rawar da irin waɗannan ƙasashe za su iya takawa wajen taimaka wa Najeriya da sauran ƙasashen Afirka wajen yaƙar ƙungiyoyi masu iƙirarin Jihadi.
Ya ce babbar hanyar ita ce "sayar wa waɗannan ƙasashe makamai da sauran kayan aiki na tattara bayanai da jiragen yaƙi da sauransu."
Ya kuma ƙara da cewa "a maimakon kai sansanin soji, kamata ya yi su kawo tsarin ƙara sojojinmu a kan abin da suke da ƙwarewa wanda sojojinmu ba su da ƙwarewa, amma maganar a kawo sojojin Amurka ko Faransa su zo su zauna a Najeriya ko wata ƙasa a tafkin Chadi ko Sahel, gaskiya ba shi da amfani."
Ya ce ba wai kawai sojojin Amurka da Faransa ba, har sojojin Rasha "ba wani amfanin kawo sojojinsu su zauna a waɗannan ƙasashe, domin ita kanta Rashar ta kai sojojinta ƙasashe daban-daban, wanda har yanzu ba mu ga ribar kai sojojin da ta yi waɗannan ƙasashe da suka zauna ba."
Ya bayar da misali da Syria da Mali inda sojojin Rasha ba su taɓuka wani abin a zo a gani ba kasancewar matsalar tsaro ƙara lalacewa ta yi a maimakon ta gyaru.
Sai dai ya ce a maimakon kawo sansanin sojojin ƙasashen waje zuwa Afirka, kamata ya yi su fi ƙarfafawa wajen horaswa da bayar da kayan aiki inda ya ce "akwai wurare da yawa da muka nemi sayen makamai da jiragen yaƙi daga ƙasashen, musamman ita Amurka, ta ƙi sayar mana, amma yanzu sai su ce za su kawo sojojinsu, ina ga ba shi da wani amfani a yarda su kawo sojojinsu." kamar yadda Barista Bulama ya ce.
Haka shi ma jami'in na Cibiyar bincike da raya dimokuraɗiyya ya bayyana cewa galibi makamai ana saye ne kuma idan Amurka da Faransa ba za su sayar ba, akwai ƙasashe da dama da za su yarda su sayar da nasu makaman.
Game da batun horas da sojoji kuwa, Farfesa Jibrin ya ce "ba lalle sai sun kawo sojojinsu sun kafa sansani za su iya taimakawa wajen wannan aikin ba, idan suna son su yi wannan aikin, sai su ce ga abin da suke son su yi, mu duba idan zai amfane mu, a gayyace su, idan ba zai amfane mu ba, mu ce ba ma so."







