Yadda ficewa daga Ecowas zai shafi Mali da Nijar da Burkina Faso

Asalin hoton, Getty Images
A baya-bayan nan ne Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar da Mali - kasashen da ke karkashin mulkin sojoji suka sanar da matakin ficewa daga kungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO.
Kasashen da suka shafe shekara kusan 50 a matsayin mambobin Ecowas, sun ce sun dauki matakin ne saboda yadda manufar kungiyar a yanzu ta sha banbam da manufar da aka kafa ta.
Masana sun ce ficewar da kasashen Mali da Niger da kuma Burkina Faso ke ikirarin sun yi daga kungiyar ECOWAS ko CEDAO na da hadari sosai, saboda za ta yi sanadin rushewar kungiyar, tare da haddasa rikici a wasu sassan nahiyar Afirka.
Matakin na kasashen uku ba ya rasa nasaba da takunkuman da Ecowas ta kakaba musu tare da korar su a matsayin mambobinta tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatocin dimokradiyya a kasashen, lamarin da ya kara dagula al'amuran siyasa a yankin Sahel.
Zuwa yanzu dai Ecowas ta ce ba ta samu sanarwar janyewar kasashen uku ba a hukumance.
Me matakin kasashen uku ke nufi?
Farfesa Jibrin Ibrahim mai sharhi a kan siyasa a shiyyar Afirka ta yamma ya shaida wa BBC cewa tun farko kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso sun yi abin da bai kamata ba saboda mambobin Ecowas sun yarda cewa dimokradiyya za a yi.
Ya kuma ce ita kan ta Ecowas ta yi kuskure kuma a ganinsa babu wani bangare da wannan matakin zai yi wa amfani.
Shi ma Farfesa Tukur Abdulkadir, malami a sashen kimiyyar siyasa a jami'ar jihar Kaduna ya ce matsayar kasashen uku babbar baraka ce a Ecowas saboda a cewarsa ba a taba samun irin haka ba tun kafa kungiyar.
Masanin ya ce a kan samu cece-kuce tsakanin kasashe renon Ingila da Faransa amma "ba na tsammanin ya taba kazancewa ya kai ga irin wannan yanayi da wannan kungiya ta samu kanta a yanzu."
Ya ce abu ne mai yiwuwa a dinke barakar amma gyara irin wannan rarrabuwar kan sai an yi da gaske tare da fahimtar juna da kuma girmama muradun kowane bangare.
Yadda janyewar za ta shafi alakar Ecowas da kasashen musamman Nijar

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun bayan sanarwar da kasashen uku suka yi, jama'a da dama sun yi ta bayyana mabanbanta ra'ayi kan yadda suke tunanin alakar kasashen uku za ta kasance musamman ga al'ummominsu.
Da yake magana a kan haka, Farfesa Tukur Abdulkadir ya ce wannan mataki zai shafi dangantakar kasashen uku da Ecowas kasancewar akwai yarjeniyoyi da dama da suka kulla.
Ya ba da misali da yarjeniyoyin da suka danganci shige da fici da na kasuwanci.
Ya kuma ce duka kasashen uku sun yi iyaka ne da sauran kasashe da suke cikin kungiyar Ecowas "idan aka cire iyakar Nijar da Burkina Faso ko Burkina Faso da Mali da Nijar ko Algeriya da Nijar."
A cewar masanin, wannan matakin na kasashen zai kara wa dangantaka ta shekaru aru-aru illa tare da "cutar da yan kasuwa" na duka bangarorin.
Sai dai ya ce ba ya tunanin duk matakin da za a dauka ba zai kai ga kassara alakar da ke tsakanin kasashen ba kasancewar dangantaka ce ta tsawon shekaru musamman Najeriya da Nijar.
Ya bayyana cewa "dole a yi la'akari da wadannan muradu na mutanen da ke wadannan kasashe, ba kawai bukatun wadanda suke jagoranci ba- gwamnatocin Nijar da Mali da Burkina Faso ko shugabannin Ecowas ba."
A bayaninsa, ya zama dole a tausayawa talakawa musamman wadanda ke fama da kunci na talauci da matsalolin rashin tsaro da ke addabar yankunansu.
Da yake magana kan irin alaka ta kusanci da ke tsakanin Najeriya da Nijar, Farfesan ya ce "Babu wata kasa a yanki na Afirka ta yamma da take da alaka ta kut da kut da na al'ada da yare da addini da haduwar kasa irin Najeriya da Nijar."
Ya ce kasancewar Nijar ba ta da karfin tattalin arziki amma "duk wani abin da ya shafi 'yanci kowa yana son 'yanci saboda dan adam yana da martaba."
Nijar da Najeriya suna bukatar juna kamar yadda masanin ya jaddada.
Makomar dangantaka tsakanin Ecowas da kasashen uku

Asalin hoton, ECOWAS
A cewar masanin, idan har Ecowas tana son ta raya kungiyar ta kuma kawo maslaha ga wannan baraka da ta faru tsakaninta da kasashen uku da a yanzu suke hannun sojoji, dole ne su nisanta daga wasu matakan da suka dauka a kan kasashen - matakan "gallazawa na kuntatawa" da suka jefa dumbin mutane cikin karayar tattalin arziki.
Ya kara da cewa "shugabannin nan kowanne ba wanda ba shi da iko da zai iya tashi ko ya je Nijar da Ouagadougou da Bamako kuma ba wanda za a ce za a harbi jirginsa idan yana hanya ko a tozarta shi."
Ya ce dole Ecowas ta yi iya kokarinta domin ganin ba a samu karin rarrabuwar kai ba tsakanin yankunan.











