Me soke yarjejeniyar sojin Amurka da Nijar ta yi ke nufi?

Asalin hoton, ORTN
A ranar Lahadi ne dai gwamnatin mulkin soji ta jamhuriyar Nijar karkashin Janar Abdourahamane Tchiani ta sanar da soke yarjejeniyar soji da ta kulla da Amurka.
Sanarwar dai na zuwa ne 'yan watanni bayan da hukumomin sojin jamhuriyar suka yanke irin wannan alaka da Faransa, inda har ma aka kori dakarun tsohuwar uwar gijiyar tata ta mulkin mallaka da ke yakar masu ikirarin jihadi a yankin daga kasar.
A 2013 ne dai Amurka da Nijar suka kulla yarjejeniyar soji, wadda a karkashinta dakarun Amurka da ke Sahel suke amfani da kananan jiragen sama marasa matuka wajen yakar kungiyoyi masu ikirarin jihadi a yankin.
Da ma dai tun bayna juyin mulkin da sojojin suka yi, sun janye jakadunsu daga kasashen Faransa da Amurka da Najeriya da kuma Togo.
To shin ko me soke yarjejeniyar sojin ke nufi? Wakiliyar BBC Hausa a Yamai Tchima Illa Issoufou ta tambayi wasu masana harkar tsaro da diflomasiyya.
Me soke yarjejeniyar ke nufi?
Masanan dai na nuna mamaki dangane da yadda sojojin jamhuriyar ta Nijar suke sassauya al'amuransu kasancewar a farkon juyin mulkin kasashen Amurka da Togo ne masu shiga tsakani amma kwatsam sai wannan bayani ya fito.
Masanan irin su Mallam Moustapha Abdoulaye wanda masanin tsaro ne da diflomasiyya a jamhuriyar Nijar sun shaida wa BBC cewa Nijar ka iya fuskantar matsaloli kamar guda hudu sakamakon hukuncin da ta yanke.
- Nijar ka iya zama saniyar ware: "Mulki na son sassauci idan dai har ana son 'yan kasa su samu saukin rayuwa domin ba ka yin fada da kowa ka zauna lafiya". In ji Malam Abdoulaye.
- Da wuya Amurka ta zura wa Nijar idanu kasancewar idan ban da kasar Djibouti, Nijar ce kasa ta biyu da Amurkar ta fi zuba kudadenta a ciki.
- Nijar za ta daina samun tallafin Amurka wajen kayan yaki da kudi domin ci gaba da yaki da matsalar tsaro a jamhuriyar Nijar.
- Sojojin Nijar za su daina samun horo daga Amurka
Martanin 'yan jamhuriyar Nijar

Asalin hoton, Getty Images
Ra'ayoyin 'yan jamhuriyar Nijar kan wannan hukunci na gwamnati ya sha bamban, inda wasu ke alasan barka, wasu kuma ke alawadai.
"Yau kimanin watanni takwas kenan da juyin mulki ba tare da wata kasa ta shata mana yadda za mu gudanar da al'amura ba. Yanke wannan alaka ta sojoji da Amurka shi ma abu ne mai kyau". In ji wani dan jamhuriyar Nijar.
Shi ma wannan ya ce bai ga wani abun damuwa ba da janyewar sojojin Amurka daga jamhuriyar ta Nijar.
"Idan da kasashen nan suna iya taimakawa wata kasa da kasar Libiya ba ta tarwatse ba, da Iraqi ba ta lalace ba, da Afghanistan ba ta lalace ba, da kasar Somalia ba ta lalace ba sannan da kasar Mali ba ta shiga cikin halin da ta kasance a baya ba. Yankin Sahel kansa da bai samu kansa a yanyi na rashin tsaro ba." In ji wani dan Nijar.
Martanin Amurka
Tuni dai kasar Amurka ta fitar da zazzafan martani ga hukuncin da shugabancin sojin na jamhuiryar Nijar ta yi, inda ta zargi Nijar da daukar hanya mai hadari da yin makirci cikin sirri.
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta yi allawadai da kulla yarjejeniyar sirri da take zargin jamhuriyar Nijar da yi da Rasha.
Harwayau, Amurkar ta zargi shugabannin na jamhuriyar Nijar da rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin kasar da kasar Iran domin amfani da makamashin Uranium da Nijar din ke da shi.











