Bunƙasar harkokin yawon buɗe ido na Halal a duniya

    • Marubuci, Emb Hashmi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

"Ina matuƙar son shaƙatawa cikin hasken rana, ina son samun nau'in bitamin D sannan ina son fatar jikina ta ci gaba da zama yadda take da duhunta duk tsawon shekara.

Don haka ina matuƙar son yawatawa wurare da yawa masu sirri da damar shaƙatawa a wuraren da suka halatta", in ji wata mai suna Zahra Rose.

Matashiyar mai tashe ta bayyana cewa tana son zama yadda take, kuma tana son riƙe addininta na Muslunci.

A harshen Larabci kalmar halal na nufin abin da aka yarda Musulmi ya yi.

Wuraren shaƙatawar halal su ne inda mabiya addinin Musulunci kan je ba tare da hakan ya shafi imaninsu da al'adun addininsu ba.

Sirri

Musulmi su ne na biyu a duniya baya ga Kiristoci a yawan mabiya.

A kowacce ƙasa ta Musulmai, za a ga mutanen da ke da rufin asiri ne ke ci gaba da bunƙasa sannu a hankali a rayuwa.

Yayin da a Yammacin Turai da Amurka ta Arewa, musulmi matakin na ƙasa da masu rufin asiri sun fi yawan almubazzaranci wajen kashe kuɗi idan aka kwatanta da iyeyensu da ke zaɓar muhimman lokutan da suka dace domin kashe nasu kuɗin.

Kasuwar na ci gaba da bunƙasa.

"A wurina babban sauyi tsakanin sauran wuraren shaƙatawa da waɗanda suka halasta shi ne sirri" in ji Zahra Rose lokacin da ta ke tattaunawa a cikin shirin kasuwanci da Sashen turanci na BBC ke gabatarwa kullum, inda ta ƙara da cewa a yanzu haka ta na neman duk inda ake samun abincin halal.

Abinci na cikin muhimmin abinda ke haɗa musulmi matafiya.

Kasancewar an haramta musu cin naman alade da shan barasa.

Hacer Sucuoglu Adiguzel 'yar shekara 36, wata uwa ce mai yara uku da ke zaune a birnin Santambul.

Ba ta da wata damuwa wajen samun wuraren sayar da abincin halal a lokacin hutu a Turkiyya.

Amma duk lokacin da 'ya'yanta suka yi tafiya zuwa ƙasashen da ba na Musulmi ba, dole sai sun yi cikakken bincike da tsari domin iya tafiyar da rayuwarsu ta dace da can.

"A kwanan nan mun ziyarci Masadoniya da Kosobo.

Mun yi karin kumallo a otel ɗin da muka sauka, daga baya muka ci abincin rana. Mun samu wurare da dama inda ake sayar da abincin halal ba tare da cakuɗa da wani kayan sa maye ba".

Takan yi sallah sau biyar a rana kuma mace ce mai riƙo da addinin Musulunci.

"Otel ɗin da ake samun abincin halal sun yi tanadin tabarmin zama ga baƙi. Kan haka idan ya zama dole mu zauna a sauran otel-otel nakan tafi da tabarmata domin yin sallah", in ji ta.

"Muna son yaranmu su kasance masu bin tsarin addini da al'adarmu. Ba ma buƙatar kai su gaɓar teku, inda mutane ke wanka da ɗan kamfai a jikinsu."

Hacer, kan koyar da mata sana'o'in dogaro da kai a shafukan sada zumunta.

A ganinta ɓangaren da ya shafi yawon buɗe ido bai shafi wuraren sayar da abincin halal ba kai tsaye.

Babbar kasuwa

Wani rahoton da Hukumar Yawon Buɗe ta Musulmi ta Duniya ta fitar ya nuna cewa ribar da aka samu a yawon buɗe ido na musulmi kawai a 2022 ta kai dala biliyan 220.

Wasu kamfunna sun ƙware a sha'anin yawon buɗe ido da ya yi daidai da rayuwar musulmi, amma wasu na saka tsarin ne a matsayin zaɓi kawai.

A ƙasa mai zafi kamar Tsibirin Maldives, na daga cikin wurare da ke da yawan ɗakunan otel da dama da su ka yi daidai da al'adun ƙasashen yamma, amma a yanzu akwai sauyi inda ake samun ƙaruwar musulmi ma su yawon buɗe ido daga ko'ina a duniya, ma su kai ziyara a waɗannan wuraren.

"Tsibirin Maldives ƙasa ce ta musulmi. A kan haka mun samu ƙasar da ta dace da muslmi", a cewar Ministan yawon buɗe ido, Dakta Abdulla Mausoom. wanda ya ƙara da cewa, "ɓangaren na ci gaba da bunƙasa cikin gaggawa".

A doka dole ne a samu masallaci a kowane otel domin ma'aikatansa su samu wurin ibada. Dakta Mausoom ya ce su ma masu yawon buɗe ido da ke ƙaruwa na amfani da waɗannan masallatai.

"Galibin wuraren shaƙatawar sun dace da da rayuwar musulmi, kama daga tsari da fasalin ɗakuna da kuma abinda ya shafi abinci", in ji shi.

Yawon buɗe ido na cikin na gaba-gaba da ke bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.

Sauye-sauye

Galibin ƙasashen musulmi sun fi yawan masu yawon buɗe kamar yadda Hukumar da ke ƙididdigar Musulmi masu yawon buɗe ido a 2023. Inda kasashen Indunusiya da Malesiya ke sahun gaba.

Ƙasashe biyu ne kawai a duniya da ba na musulmi ba da suka samar da shi. Yayin da Singafo ke da 11 akwai kimanin 20 a Burtaniya.

An buɗe wannnan babban otel na Landmark da ke Landan a 1899, kuma yanzu haka ya na sayar da halastacen nama. An kuma horas da ma'aikatansa tsarin al'adu da addini tamkar dai na yankin Gabas ta Tsakiya.

"Muna da barasa da kuma kayan sha da ba na maye ba. A masahaya a na iya samun duk abinda ake so da ba ya bugarwa", a cewar Magdy Rustum, wanda shi ne daratan kasuwanci na ɓangaren Gabas ta Tsakiya.

"Akwai hanyoytin shiga guda biyu. Ɗayan da ke sashen arewa da otel ɗin an yi shi ne musamman domin wasu".

"Galibijn iyalan da mu ke da su daga Gabas ta Tsakiya, musamman mata, ba su buƙatar a gan su, wanda ya sa su ke amfani da ƙofar da ke arewa".

"Akwai kuma na'urar lifta ta musamman da aka samar da kan ɗauke su kai tsaye har zuwa cikin ɗaki, ta yadda babu wanda zai iya ganin su."

Akwai katafaren ɗaki da a ka ware domin bukukuwan da suka shafi ɗaurin aure, kuma a na iya ware maza daban mata daban kamar dai yadda addinin musulunci ya tanada.

Amma fa duka waɗannan sauye-sauyen a kan kashe kuɗi da yawa, abinda kuma a wurin Zahra ba abin damuwa ne ba.

"Na riga na san cewa tsari mai cikakken sirri na buƙatar kashe kuɗi fiye da kowane irin hutun shaƙatawa", in ji ta.

"Babu wata wahala samun wurin shaƙatawa mai kududdufin wanka haɗe ko wanda ba ka da wani sirri naka ko ɗakinka."

"Eh, dole ne kuwa in ce za a iya samun bambancin farashi"