Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hatsarin jirgin Nepal: 'Direban jirgin bai bayar da rahoton komai ba kafin hatsarin'
Direban jirgin saman Nepal da ya yi hatsari bai bayar da rahoton komai ba a lokacin da jirgin saman ke kaiwa kusa da filin jirgin, kamar yadda wani mai magana da yawun filin jirgin Pokhara ya bayyana.
Anup Joshi ya bayyana cewa tsauninkan wurin a bayyana suke kuma ana ganinsu inda ya ce hasali ma akwai fitila ta iska kuma babu wata matsala ta yanayi.
Fasinjoji 72 ne a cikin jirgin na Yeti Airlines wanda ya yi hatsari a ranar Lahadi wanda ya taso daga Kathmandu zuwa garin da ake zuwa yawon buɗe ido na Pokhara.
Babu wanda ya tsira a hatsarin jirgin. Wani bidiyo da aka ɗauka da waya ya nuna yadda jirgin yake ta juyawa a yayin da yake tunkarar filin jirgin.
Daga nan sai ya daki wani bango na tsauni da ke gefen kogin Seti, wanda ke da nisan kilomita guda daga filin jirgi na birnin.
Direban jirgin ya nemi a sauya masa titin saukar jirgi daga na ɗaya zuwa na uku wanda aka amince masa da hakan, kamar yadda Mista Joshi ya bayyana.
"Abu ne mara daɗi" kan cewa an buɗe wannan filin jirgin bayan kwanaki 15 domin kasuwanci, in ji Mista Joshi.
Wannan hatsarin shi ne mafi muni a cikin shekara 30. Masu kai ɗauki tun da farko sun bayyana cewa sun haƙura da neman waɗanda suka tsira.
Jami'in yankin Tek Bahadur ya ce "babu yiwuwar samun ko mutum guda a raye".
Sai dai an gano bayanai kan jirgin da kuma rikoda ta cikin jirgin, in ji shi.
"Mun karɓi gawarwaki 68 zuwa yanzu," in ji shi.
Firaiministan Nepal ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu domin makoki haka kuma tuni gwamnatin ƙasar ta kafa wani kwamiti domin a gudanar da bincike a kan wannan hatsarin jirgin saman.
Wata mazauniniyar yankin da lamarin ya faru Divya Dhakal ta shaida wa BBC cewa ta yi sauri ta garzaya wurin da lamarin ya faru bayan ta ga jirgin yana ƙasa daga iska da misalin 11:00 na safe.
"Zuwa lokacin da na isa can, wurin da aka yi hatsarin ya cika da mutane. Akwai hayaƙi mai yawa da ya rinƙa fitowa daga jirigin. Daga nan jirage masu saukar ungulu suka zo nan take," in ji ta.
"Direban jirgin ya yi iya ƙoƙarinsa kada ya faɗa cikin wani gini ko kuma gida," in ji ta.
Hatsarin jirgin sama ba sabon abu bane a Nepal akasari saboda yanayin filayen jirgin da ke cikin daji da kuma yawan sauyin yanayin da ake samu.
Ƙasar dai tana da tsaunuka da dama kuma mafi wahalar bi ga matuƙa jirgi a duniya.
Haka kuma ƙarancin zuba jari kan sabbin jiragen sama da ƙarancin sa ido kan su na daga cikin matsalolin da aka rinƙa alaƙanta hasatin jirgi da su a ƙasar tun a baya.
Tuni dama Tarayyar Turai ta haramta wa jiragen Nepal ratsawa ta sararin samaniyarta kan fargabar ƙarancin horo na direbobin jirgin da kuma kula da jiragen kansu.