Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wacce irin dangantaka za a kulla tsakanin Liz Truss da kasashen Afirka?
Batutuwa kamar siyasa da kasuwanci da muhalli da agaji da tsaro na sauyawa a nahiyar Afirka. Sauyin cikin sauri.
Masu sharhi sun yi amanna cewa dangantaka tsakanin Afirka da gwamnatin Birtaniya karkashin Liz Truss ka iya zama ta ba yabo ba fallasa, sakamakon yadda za ta mayar da hankali kan farfado da tattalin arzikin kasarta da dambarwar da ta mamaye jam’iyyar Conservative da ta fuskanci matsaloli karkashin Boris Johnson.
“Babu tabbaci kan manufofin Birtaniya a kasashen da za su nuna karara kasar na da wata manufa misali ta siyasa a halin yanzu,” in ji wani farfesa kan kimiyyar siyasa a Najeriya.
An sanar da Liz Truss a matsayin sabuwar firaiministar Birtaniya bayan fafatawa a neman shugabancin jam'iyyar Conservatives da tsohon Ministan Kudin kasar Rishi Sunak.
Shugaban kwamitin jam’iyyar a shekarar 1922, Sir Graham Brady, ne ya ba da sanarwar nasarar sabuwar shugabar jam’iyyar Conservative a ranar Litinin.
Ya ce Truss ta yi nasara da kuri’u 81,326 da aka kada, yayin da shi kuma abokin takararta Sunak ya samu kuri'a 60,399.
Abin da ya sa Afirka za ta damu
Duk da cewa ba a ji wasu abubuwa da Truss ta sanar kan shirin gwamnatinta ga Afirka ba zuwa yanzu, ana fargabar cewa manufofinta ka iya mayar da nahiyar saniyar-ware.
Farfesa Eme Ekekwe, na Tsangayar Kimiyyar Siyasa a Jami'ar Fatakwal, ya ce za a tilasta wa Truss fara shawo kan matsalolin cikin gida da ta gada, kafin ta waiwayi kasashen waje.
"Tuni ayyuka suka mamaye lokacinta tun kafin ta fara sabon aikinta. "Ina fatan za ta yi amfani da shekarar aiki ta farko a ofis don magance matsalolin da ke damun 'yan Birtaniya kamar tsadar rayuwa, matsalar makamashi da matsalar cikin gida a jam'iyya mai mulki ta Conservative da sauransu.
"Wadannan su ne abubuwan da za su sha kanta da zarar ta fara aiki gadan-gadan. Da duba hanyar da za su shawo kan 'yan kasar su aminta da su," in ji shi.
Ya bayyana cewa bai kamata nahiyar Afirka ta saki jiki da tunanin sabuwar gwamnatin Birtaniya za ta dama da ita ba, saboda a yanzu haka kasar ta janye jiki daga wasu kasashe ba kamar a baya ba - za ta bar Afirka ta magance matsalolinta na cikin gida musamman na siyasa.
Shin nasarar Truss barazana ce ga Afirka?
Sabuwar firaiministar za ta fara aiki ne a daidai lokacin da 'yan Birtaniya ke fama da matsin tattalin arziki mafi muni a tarihi da yaki tsakanin Rasha da Ukraine ya kara haddasawa. -Akwai kuma wasu dalilan na daban kan hakan. Wani malamin kimiyyar siyasa, Dr Anthony Egobueze, a jami'ar jihar Rivers a kudancin Najeriya, ya ce ya kamata Afirka ta damu da duk wani sabon firaiministan da Birtaniya za ta yi saboda ci-gabanta.
Ya tuna lokacin da tsohon firaiminista, Boris Johnson, ya nuna aniyar gwamnatinsa ta taimaka wa Afirka a lokacin taron koli tsakanin Birtaniya da Afirka da aka yi a birnin Landan a shekarar 2020, wanda hakan ya kara yaukaka alaka tsakanin Birtaniya da Afirka.
"Kasancewar Liz Truss sabuwar firaiministar Birtaniya, ya sanya Afirka samun 'yar kwanciyar hankali, ganin cewa ita ce za ta ci gaba da manufofin wanda ta gada Boris Johnson, kan harkokin waje," in ji shi.
Liz Truss ta jinjina wa Boris Johnson, lokacin ganawa da jawabi ga Sarauniya Elizabeth.
Farfesan ya yi bayanin Birtaniya za ta ci gaba da ayyukan ci-gaba da bunkasa Afirka.
'Manufofin ci-gaba ga Afirka'
Mista Olufemi Hassan, wani kwararre kan tattalin arziki a Cibiyar Hatytude Consulting da ke birnin Lagos ya yi amanna cewa yawan 'yan Afirka da ke zaune a Birtaniya, na daya daga cikin abubuwan da ke nuni da ayyukan kasar a nahiyar.
"Matsayin Truss ka iya hawa ma'auni biyu. Yayin da Afirka ke da aniyar mu'amala da kasarta, ita ma ya kamata ta fara tunanin karuwar da Birtaniya za ta yi ga ayyuka a nahiyar Afirka," in ji Mista Hassan.
Ya ce ficewar Birtaniya daga tarayyar turai ta bude dama ga kasar ta fadada damarmaki a sassan duniya da wasu kasashen da suka ci gaba.
Mista Hassan ya kara da cewa yayin da nahiyar Afirka ta kammala tsare-tsare kan shirin kasuwanci maras shinge, kamata ya yi ita kuma Birtaniya ta fara tunanin kudurinta kan nahiyar, ta fara karfafa wa Afirka gwiwa, kan fannin kasuwanci da hadin gwiwa tsakaninsu da shimfida manufofin yaukaka dangantakar da za ta kawo ci-gaba."
Ya kara da cewa " Shirin amfani da kudin bai daya na AfCFTA, zai fadada damar kasuwanci da samun kudaden shiga a nahiyar ga Birtaniya."
Abin da ya kamata Truss ta bai wa muhimmanci a Afirka
Duk da cewa tsohon firaiminista, Boris Johnson, ya bayyana aniyar Birtaniya na sanya jari a taron koli tsakanin kasarsa da Afirka, bai yi bayani dalla-dalla kan hakan ba, sai dai ya kamata yanzu a dora daga inda ya tsaya. Barkewar annobar korona ta sanya da wuya a gudanar da yarjejeniyoyin da aka cimma a aikace, da sanya tattalin arzikin duniya cikin mawuyacin hali, ciki har da tsakanin Birtaniya da Afirka na shekarar da suka yi taron kolin. Duk da hakan, duba da halin da ake ciki, kwararru a Afirka sun ce ana bukatar mayar da hankali kan abubuwan da suka hada da; • Kasuwanci maras shinge • Tsaro, da magance tashe-tashen hankali • Fasaha • Inganta shugabanci na gari • Kare hakkin dan-Adam • Magance sauyin yanayi • Batutuwan da suka shafi ci-gaba • Magance bakin talauci tsakanin al'umma.
Dakta Egobueze ya ce "sai ko idan Truss na da aniyar kin amfani da koyarwar Birtaniya na kasuwanci maras shinge, dimokuradiyya da kare hakkin dan adam, da sanya matakan da za su karfafawa Afirka gwiwar bunkasa nahaiyarta." Shi kuwa Mista Hassan, ya yi amanna baya ga abin da Mista Johnson ya bari, sabuwar firaiministar ba lallai ta wargaza abin da ta taras ba, musamman manufofin kasarta kan Afirka - "Ina tunanin za ta yi duba na tsanaki ta fuska daban da wadda Boris da gwamnatinsa suka yi wa Afirka."
Magance matsalolin kasashe rainon Ingila
CBatun kasuwanci da tattalin arziki ga kasashe 56 na ommonwealth na daga cikin masu muhimmanci ga Truss.
A farko gasar wasannin kasashen Commonwealth a Birmingham sabuwar firaiministar ta yi jawabi da tabbacin kasashen na daga cikin abubuwa muhimmai da shiri mai inganci da Birtaniya za ta yi.
Dakta Egobueze ya ce bambancin siyasa da akida ga kasashen ka iya sanya aikin Truss da manufarta ga nahiyar su fuskanci cikas.
"Kasancewar Truss sabuwar firaiminista na nufin sabon zamani, sabuwar rayuwa, kuma sabuwar dama ga shugabannin kasashen Afirka, da gaggauta sanin inda aka nufa da gabatar da bukatu masu inganci da Birtaniyar za ta yi gare su da yaukaka dangantaka tsakani. 'Abubuwan da babu tabbas a kai'
Farfesa Ekekwe ya ce manufar Birtaniya a Afirka na da yawan gaske.
Ya yi bayani kan yadda Truss ta jaddada manufar kasarta da fadada shirinta na Rwanda duk da sukar hakan da Majalisar Dinkin Duniya ke adawa da shi na girke masu neman mafakar shiga Birtaniya kafin a ba su wannan damar.
Sannan abin da zai dauki hankalin Birtaniya a Afirka shi ne janyo hankalinsu ta fuskar kasuwanci, domin doke abokan hamayyarsu ta wannan fannin irinsu China da Turkiyya da Rasha.