Jorginho ya tsawaita zamansa a Arsenal

Ɗan wasan tsakiyar Arsenal Jorginho ya tsawaita zamansa a ƙungiyar da ke buga gasar Premier League ta Ingila.

Tun da farko ɗan Italiyan mai shekara 32 ya sanya hannu kan yarjejeniyar wata 18 ne lokacin da ya koma daga Chelsea a Janairun 2023.

Sabon kwantaragin nasa na "taƙaitaccen lokaci ne", in ji kulob ɗin.

Ɗan wasan da aka haifa a Brazil kuma mai taka wa Italiya leda ya buga wa Arsenal wasa 35 a dukkan gasa a kakar bana, kuma ya ci ƙwallo ɗaya.

"Ina farin ciki sosai da tsawaita zamana, saboda alfarma ce mutum ya kasance tare da wannan iyalin," a cewar Jorginho.

Ya shafe shekara huɗu da rabi a Chelsea kafin ya koma Arsenal, kulob ɗin da ya ce yana cikin wani "yanayi na musamman" a ƙarƙashin mai horarwa Mikel Arteta.

"Jorgi ɗan wasa ne mai muhimmanci a ƙungiyar nan, abin koyi da ke da ƙwarewa wajen jagoranci da kuma salon wasa na musamman da ke kyautata ƙwarewar sauran abokan wasansa," in ji Arteta.

Arsenal za ta kara da Manchester United a filin wasa na Old Trafford ranar Lahadi mai zuwa, kafin ta fuskanci Everton a gida a wasan ƙarshe na kakar bana ranar 19 ga watan Mayu.