Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ake cin zarafin yara a wani asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa a Birtaniya
- Marubuci, Mark Daly and Jax Sinclair
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Scotland Disclosure
- Lokacin karatu: Minti 8
Wasu da aka taɓa kaiwa asibitin kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa mafi girma a Scotland a baya sun shaida wa masu binciken ƙwaƙwaf na BBC irin azabtarwar da ma'aikatan jinya ke yi.
Marasa lafiyan waɗanda matasa ne kuma aka kai su ‘Skye House’, wani ɓangare na musamman na cibiyoyin hukumar lafiya ta Birtaniya (NHS) da ke birnin Glasgow, sun shaida wa BBC cewa wasu ma'aikatan jinyan sun kira su 'abin kazanta' kuma 'abin ƙyama' kuma sukan yi musu izgili kan ƙoƙarin kashe kansu da suka yi.
''Ji nayi kamar an mayar da ni kamar wata dabba,'' in ji wata da ta yi fama da lalurar rashin cin abinci.
Hukumar lafiya ta Birtaniya ta NHS a ya kin Greater Glasgow da Clyde ta ce '' ta na matukar bayar da haƙuri'' kuma ta ƙaddamar da bincike kan zarge-zargen da sashen bincike na BBC ya bankaɗo.
Ƴan jarida sun tattauna da marasa lafiya 28 da suka yi jinya a asibitin a yayin shirya rahoto na musamman na BBC kan 'yaran da su ke asibitin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa'.
Ɗaya daga cikin su ta ce sashen kula da masu lalurar ƙwaƙwalwa mai ɗaukar marasa lafiya 24 wanda ke asibitin Stobhill da ke Glasgow kamar 'jahannama' yake.
''Gaskiya tsarin aikin ma'aikatan jinyan akwai cutarwa. A gaskiya, akasarinsu su na mana mugunta a mafi yawan lokaci,'' a cewar ta.
Matasan da aka kwantar a asibitin tsakanin 2017 zuwa 2024, sun shida wa shirin cewa ma'aikantan jinyar na saurin amfani da karfi, kamar ɗaure su, jan su a ƙasa wanda zai kai ga samun rauni.
Ɗaya daga ciki ta ce ta so ta kira Jami'an ƴansanda bayan cin zarafinta da ta ce an yi, amma sai ta ƙi yin hakan saboda ta ji tsoron muzguna mata da ake yi zai iya karuwa.
Wasu kuma sun ce ana ba su magunguna ba yadda ya kamata ba da yi musu allurar kashe jiki ko ciwo saboda ma'aikatan su yi aiki cikin yanayin da ba hayaniya.
Wasu marasa lafiyan sun ce ana hukunta su ida suka yi rashin lafiya, ciki har da tilasta musu goge jini bayan sun yi yunƙurin cutar da kansu.
Gargaɗi: Za a iya cin karo da bayanai masu tayar da hankali a cikin wannan labari.
‘Skye House’ wanda aka buɗe a shekarar 2009 na karɓar yara ƴan shekara 12 zuwa 18 waɗanda ke fama da lalura daban-daban.
Wasu ana riƙe su ne ƙarƙashin dokar kula da lafiyar ƙwaƙwalwa wanda ke nufin ba za su iya tafiya ba har sai likitoci sun bayar da tabbacin cewa sun samu lafiyar da za a iya sallamar su.
BBC ta fara bincike bayan wata mara lafiya ta kai ƙara kan yadda aka kula da ita a lokacin da ta ke asibitin.
Daga bisani aka fara samun wasu masu ƙorafe-ƙorafen.
Cara ta shafe fiye da shekaru biyu a asibitin ana ba ta kulawa kan lalurar rashin cin abinci.
An ɗaure ta fiye da sau 400 a cikin watanni 18, kamar yadda takardun asibiti da BBC ta duba suka nuna.
A wasu lokutan har takan samu rauni, a wani lokaci kuwa gashin kanta aka tuge.
''Abin zai sa maka damuwa. Ba za ka iya mantawa ba,'' in ji ta.
Ma'aikatan jinya a wasu lokutan har su biyar za su ɗaure mutum a kan gado ko a ƙasa idan mutumin na da hatsari ga kanshi ko wasu.
Tsarin kulawa ya ce ɗauri shi ne mataki na ƙarshe da za a yi bayan an ƙarar da duk wasu hanyoyin.
Cara, wadda ta kai shekara 21 a yanzu, a wasu lokutan dole ne a ɗaure ta domin kar ta ji wa kanta ciwo, sai dai ta ce za a iya kauce wa ɗaure ta a lokuta da dama in da ma'aikatan sun yi yunƙurin yin magana da ita kafin a kai nan.
Ta ce wani lokaci da aka ɗaure ta a 2021 ta ji ciwo kuma ta kaɗu sosai.
''Ya riƙe ni ta wuya ya sa ni a ƙasa,'' in ji Cara.
A wani lokacin kuma, bayanai na lafiyar Cara sun nuna cewa ta ji kamar an duke ta bayan wata ma'aikaciyar jinya ta wurgar da ita a ƙasa.
Cara ta so ta kira ƴansanda, daga baya kuma ta sauya tunani.
Ta shaida wa masu binciken cewa ta yi hakan ne saboda tsoron abin da hakan zai janyo.
''Kawai na yi tunanin za su muzguna min fiye da yadda suke yi a yanzu,'' a cewar ta.
A lokacin da Jenna - wadda ta fito daga yankin Inverness - ke shekara 16, ta yi fama da lalurar damuwa da kuma lalurar rashin cin abinci kuma ta fara cutar da kanta.
Asibitin kula da lafiyar kwakwala na matasa mafi kusa shi ne wanda ke Dundee, amma a lokacin babu gado sai aka kai ta Skye House.
"Wurin kamar kurkuku yake'' in ji Jenna.
Jenna ta shafe aƙalla watanni 9 a asibitin.
Ana yi mata magani kan lalurar rashin cin abinci ta hanyar ba ta abinci ta hanci, wani tsarin kulawa da ake yi wa mutanen da ba sa cin abinci mai gina jiki wanda ake saka bututu ta hanci zuwa ciki.
Wasu lokutan sai an ɗaure ta kafin a saka shi, amma ta ce yadda ma'aikatan suka rinƙa yi mata ya bar ta cikin damuwa.
''Wasu lokutan kawai za su zo su fizge ni su tafi da ni'' in ji ta.
''Ma'aikatan jinya da dama za su zo su ja ni''.
Ta ce wasu lokutan ma'aikatan za su ja ta da ƙarfi har ya kai ga jin ciwo da zubar da jini.
''Kamar wani hukunci ne a fakaice suke min domin ya zama izina a gare ni.''
'Ana yawan hukunta ni kan abubuwa'
Yunƙurin cutar da kai wani abu ne da kusan dukkan marasa lafiyan da BBC ta tattauna da su kan lamarin suka yi fama da shi.
Sun yi iƙirarin cewa ma'aikatan jinyar na ƙin zuwa duba su bayan mintuna 15, kamar yadda yake a tsari, wanda hakan zai ba su damar cutar da kansu.
Jenna da Cara sun shaida cewa akwai lokuta da dama da suka cutar da kansu kuma aka tilasta su su goge jininsu daga kasa da kuma bango.
Jenna ta ce : ''na tuna sa’ilin da ma'aikatan ke cewa, ''ke abar ƙyama ce, wannan abin ƙyama ne, dole ki goge shi', hakan ya sa ni jin takaici sosai.''
Cara ta ce wasu lokutan ma'aikatan ba sa kulawa sosai a lokacin da suke ba ta abinci sai su ba ta cikin gaggawa wanda ya ke sa ta yi amai.
Ta ce ana sa ta tsaftace kanta da kanta duk da ba ta da lafiya.
Cara ta ce: ''Za su ba ni tsumma, su ce in goge ƙasa. Nakan ji kamar ana horar da ni ne, kamar da gangan na yi.
''Kawai na ji kamar ana yawan hukunta ni kan abubuwa.''
Stephanie ta kwanta a ‘Skye House’ a lokuta da dama saboda fama da cutar tsananin damuwa daga 2020 a lokacin ta na shekara 16.
Ta ce zaman ta a wurin ya sa mata ƙarin damuwa.
''Ma’aikatan jinyar ba sa kulawa da kai cikin tausayi,'' a cewar ta.
''Maimakon su tambaye ka mene ne ke damun ka, kawai za su danne ka a ƙasa su yi maka allura.''
A wani lokacin, Stephanie ta yi zargin cewa wata ma'aikaciya ta duke ta bayan ta fusata kan cewa ta ƙi yarda ta yi wanka.
Stephanie ta ce: ''Ma'aikaciyar jinyar ta yi fushi da ni.''
''Daga nan ta ja ni ta kafata daga kan gado, ta kai ni banɗaki ta kunna ruwa, ta saka ni ƙarƙashin famfo da kaya a jikina, sai ta juya ta tafi abinta.''
''A lokacin na ɗauka hakan ba komai ba ne, na ɗauka kowa ma haka ake yi masa.''
Jane Heslop, babbar ma'aikaciyar jinya ce a NHS da ta yi ritaya wadda ta shafe tsawon rayuwarta tana kula da yara da matasa kan lalurar rashin lafiyar kwakwalwa kuma ta yi nazari kan binciken BBC.
''Cin zarafi ne, kwata-kwata ba daidai ba ne,'' in ji ta.
''Idan yadda matasan suka bayyana hakan abin ya faru, ba abu ne da za a lamunta ba.''
Ms Heslop ta ce da alama ''wasu daga cikin ma'akatan nan ba su san iyakar su ba''.
Abby na da lalurar kwakwalwa ta autism kuma ta zauna asibitin Skye House ta na da shekara 14 lokacin da ta fara cutar da kanta da kuma yunƙurin kashe kanta.
Ta zauna a asibitin na shekara biyu da rabi kuma ta ce ma'aikata sun musguna mata, wasu da kalaman baki.
A wani lokacin, ta ce sun yi mata izgili kan cutar da kanta.
Ma'aikaciyar jinyar ta zo kusa da ni ta kusa yin dariya, ta yi murmushi, kuma ta ce '' kin zama abin kyama, kalli kanki,'' in ji Abby.
''wasu lokacin sai nake ji kamar tsangwama. Har ya kai ga na so in cutar da kaina.''
''Sai na ji kamar da gaske ne idan mutane na gani na kamar abin kyama, to ni abar kyama ce.
Abby da ƴan‘uwanta na ganin cewa an ba ta magani fiye da yadda ya kamata a Skye House.
Ta ce: ''Da yawa daga cikin marasa lafiyar na jin kansu kamar mutattu a tsaye, ciki har da ni.
''Kamar a lokuta da dama ana ba mu maganin da ke sa mu ji kasala ya kashe mana jiki inda muke ma rasa inda mu ke.''
Jenna ta ce ma'aikatan su na yawan amfani da allurar kashe jiki a lokacin da marasa lafiya ke cikin wani hali.
Amfani da wannan maganai ya kamata ya zama matakin ƙarshe.
Jenna ta ce:" ba tare da ƙoƙarin yi min magana ba, ko kwantar min da hankali, kawai za su tafi kai tsaye su min allura.
''Ina ganin kamar su na hakan ne saboda su samu saukin aikin su idan duka marasa lafiyan ba sa cikin hayyacinsu.''
'Muna matuƙar neman afuwa'
Sashen inshorar lafiya na Birtaniya a yankin Glasgow da Clyde ya ce an sake bita kan magungunansu a 2023, kuma hakan ya sauya yadda a ke bayar da magani.
Dakta Scott Davidson, shugaban asibitin NHS Greater Glasgow and Clyde ya ce zarge zargen abu ne da ma ''su ke da wahalar sauraro'' kuma ya amince cewa akwai lokutan da yadda ake bayar da kulawa '' ya gaza yadda ya kamata a yi ma matasanmu''.
'' A dalilin hakan, an ƙaddamar da cikkaken bincike kan ingancin kulawan da ake bayarwa,'' inji shi.
Hukumar ta kuma ce ta ƙara inganta kula da marasa lafiya ciki har da ɗaukar sabbin ma'aikata da horar da su kan kula da marasa lafiya yadda ya kamata.
Ta kuma amince da cewa Skye House ta fuskanci matsalar ƙarancin ma'aikata a baya wanda ya sa ma'aikatan banki da wata hukumar su kayi aiki a asibitin.
Wata sanarwa da aka fitar ta ce : '' Hakan bai kamata ba saboda ba su da ƙwarewa a fannin kula da marasa lafiya da kuma sarkaƙiyar da marasa lafiyan da ake kula da su a Skye House ke da shi''.
Ta ce tuni aka ɗauka mataki domin magance matsalar ƙarancin ma'aikata.
Hukumar kula da lafiyar kwakwalwa ta Scotland ta ziyarci Skye House so shida tun daga 2017.