Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid na sanya ido kan Guehi, Chelsea na kan gaba a zawarcin Rogers
Real Madrid ta zayyana sunayen ƴan wasan baya guda uku waɗanda za ta yi ynnƙurin ɗauka a kyauta a bazara mai zuwa, kuma sun haɗa da ɗan wasan Crystal Palace da Ingila Marc Guehi, mai shekara 25, da ɗan wasan baya na Bayern Munich da Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 26, da kuma ɗan wasan Liverpool da Faransa Ibrahima Konate mai shekara 26. (Talksport)
Ana yi wa Chelsea kallon ƙungiyar da ke kan gaba wajen fafutukar siyan ɗan wasan tsakiyar Ingila Morgan Rogers mai shekara 23 daga abokiyar hamayyarta Aston Villa. (CaughtOffside)
Manchester City da Chelsea da Liverpool da Arsenal duk sun shiga jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan gaban River Plate ɗan ƙasar Argentina Ian Subiabre mai shekara 18, wanda ake sa ran zai koma gasar Premier shekara mai zuwa. (TBR Football)
Nottingham Forest ta na nazari kan kocin Fulham Marco Silva da Sean Dyche da Roberto Mancini - a matsayin waɗanda za su iya maye gurbin Ange Postecoglou. (Guardian)
Ɗan wasan gaban Real Madrid ɗan ƙasar Brazil, Endrick, mai shekara 19, na sha'awar komawa Marseille sakamakon rashin samun gurbin buga wasa a ƙungiyar ta La Liga. (L'Equipe)
Tottenham ta shige gaban Chelsea da Manchester United a fafatukar sayen ɗan wasan gaban Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 25 daga Juventus. (Football Insider).
Chelsea na iya tayar da batun sake siyan ɗan wasan tsakiyar Belgium Diego Moreira, mai shekara 21, daga Strasbourg. (TBR Football).
Real Madrid na sa ido kan ɗan wasan tsakiyar Mexico Gilberto Mora, mai shekara 17, wanda ke taka leda a kulob din Tijuana na Mexico. (AS)