Afcon: Ko Ivory Coast za ta kai kwata fainal a kan Burkina Faso?

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Talata za a kammala zagaye na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a kara tsakanin Aljeriya da Jamhuriyar Congo da kuma na mai riƙe da kofin, Ivory Coast da Burkina Faso.
Ivory Coast ce ke rike da Afcon, kuma tana da uku jimilla, yayin da Burkina Faso ke fatan ɗaukar na farko a Morocco.
Shin me kuke son sani dangane da wasannin?
Wasan farko Aljeriya da Jamhuriyar Congo

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar Aljeriya da taJamhuriyar Congo za su fuskanci juna a gasar cin kofin nahiyar Turai a karon farko bayan shekara 26, inda za su buga zagaye na biyu a gasar ranar Talata a Prince Moulay Abdellah a Rabat.
Kuma wannan shi ne karo na uku a Afcon, bayan da suka fara haɗuwa a 1998, inda Aljeriya ta yi nasara 1-0 a cikin rukuni.
Sun kuma kara fafatawa a 2000 a wasan farko a rukuni na biyu da suka tashi 0-0 a Kumasi, Ghana.
Jimilla sai bakwai suka kara a tsakaninsu, Aljeriya ta yi nasara uku da canjaras huɗu.
Wasa huɗu baya canjaras suke tashi har da na baya-bayan nan da suka 1-1 a wasan sada zumunta - Wasan karshe da Aljeriya ta yi nasara a kan Jamhuriyar Congo a Afcon tun 1988.
Kuma haɗuwa ta karshe da suka yi ita ce a sada zumunta a Oktoban 2019 da tashi 1-1.
Jimilla sau bakwai aka fafata tsakanin Aljeriya da Jamhuriyar Congo, Aljeriya ta yi nasara uku da cin ƙwallo 10 aka zura mata huɗu a raga da canjaras huɗu.
Ga sakamakon fafatawar da suka yi a Afcon:
1998 – wasan cikin rukuni – 19 ga watan Maris 1998
- Aljeriya 1 - 0 Jamhuriyar Congo
2000 – wasan rukuni na biyu – 24 ga watan Janairu 2000
- DR Congo 0 - 0 Aljeriya
Ƙwazon da Algeria ke yi a wasannin cin kofin Afirka

Asalin hoton, Getty Images
- Aljeriya ta kawo wannan gurbin bayan da ta lashe dukkan wasa ukun rukuni.
- Ta kuma ci ƙwallo bakwai a cikin rukuni, ɗaya ne ya shiga ragarta.
- Idan har Aljeriya ta yi nasara, zai zama karo na huɗu a jere tana cin wasa a Afcon a karo na uku, bayan bajintar da ta yi a 1990 da kuma 2019.
- Wannan shi ne karo na biyu da ta kai zagaye na biyu bayan 2019, wadda ta kasa kaiwa wannan gurbin a 2021 da kuma a 2023.
- Ta lashe wasan zagaye na biyu da doke Guinea 3-0 a 2019.
- Da zarar ta yi nasara a karawar nan za ta kai kwata fainal karo na bakwai jimilla (1996, 2000, 2004, 2010, 2015 da kuma 2019).
- Riyad Mahrez ya ci ƙwallo uku a Afcon a 2025 da Morocco ke shirywa.
- Idan kuma ya kara cin ƙwallo zai zama na farko daga Aljeriya mai huɗu a raga a gasar kofin nahiyar Afirka da ake yi, bayan Djamel Menad a 1990.
- Mahrez shi ne kan gaba a yawan ci wa Aljeriya ƙwallaye a Afcon a tarihi, mai tara jimilla.
Gumurzun da Jamhuriyar Congo ke yi a Afcon

Asalin hoton, Getty Images
- Jamhuriyar Congo ta fara nasara a kan Benin a karawar rukuni a Morocco daga baya ta tashi 1-1 da Senegal, sannan ta cinye Botswana 3-0 a wasan karshe.
- Karo na biyu da ba a doke ta ba a wasa uku a cikin rukuni a Afcon, bayan ƙwazon da ta yi a 2023.
- Tun daga 2013 ba ta yi rashin nasara ba a karawar cikin rukuni a biyar daga Afcon shida, ta yi kan-kan-kan da Morocco da kuma Mali a wanna bajintar.
- Sau biyar kenan tana kaiwa zagayen gaba a jere a Afcon daga fafatawar cikin rukuni (2015, 2017, 2019, 2023 da kuma 2025).
- Ta kuma ci ƙwallo 99 a Afcon da zarar ta kara ɗaya a raga, za ta zama ta takwas da suka zura 100 a raga a babbar gasar tamaula ta Afirka.
- Wannan shi ne karo na uku da ta kai zagayen ƴan 16 a baya-bayan nan.
- Ta kuma haura zuwa kwata fainal a 2023, aka kuma yi waje da ita a 2019.
- Wasa biyu baya da bugun fenariti aka fitar da wadda ta kai zagayen gaba.
- Ta yi 2-2 da Madagascar a 2019 daga baya aka doke 4-2 a bugun fenariti, duk da karin lokaci.
- A 2023 kuwa ta tashi 1-1 da Masar daga baya ta kai zagayen gaba da nasara 8-7 a bugun fenariti har da karin lokaci.
- Idan ta yi nasara za ta buga kwata fainal na 10 kenan a Afcon.
- Garin gasar da ta kai kwata fainal 1992, 1994, 1996, 1998, 2002, 2006, 2015, 2017 da kuma 2023.
Wasa na biyu tsakanin Ivory Coast da Burkina Faso

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wasan karshe a zagaye na biyu a Afcon da Morocco ke gudanarwa za a yi ne tsakanin mai rike da kofin, Ivory Coast da Burkina Faso
Karo na uku da za su kece raini a tsakaninsu a Afcon, bayan da suka kara a cikin rukuni na 2010 da kuma 2012, kenan karon farko da za su fafata a zagayen ƴan 16.
Sai dai 20 suka haɗu jimilla a dukkan fafatawa, Ivory Coast ta yi nasara takwas, Burkina Faso ta ci wasa uku da canjaras tara a tsakaninsu.
An haɗa su tare a wasan neman shiga Afcon a 1996, inda dukkan wasan biyu suka raba maki, sannan suka kai gasar da aka yi a Afirka ta Kudu.
Sun kuma kara a wasan neman shiga gasar kofin duniya a 2010, Ivory Coast ce ta yi nasara 3-2 da kuma cin 5-0 a gida.
Sau biyu suna fafatawa a wasannin neman shiga Afcon, Ivory Coast ta kai bante a 2022, ita kuwa Burkina Faso ta samu gurbin shiga wasannin da aka yi a 2024.
Sau 20 aka kara tsakanin tawagogin biyu, inda Ivory Coast ta ci wasa takwas da cin ƙwallo 28 aka zura mata 17 a raga da rashin nasara uku.
Wannan shi ne karo na uku da za su fuskanci juna a Afcon
2010 – Wasan cikin rukuni na biyu, 11 ga watan Janairun 2010
Ivory Coast 0 - 0 Burkina Faso
2012 – Wasan cikin rukuni na biyu, 26 ga watan Janairun 2012
Ivory Coast 2 - 0 Burkina Faso
Bajintar Ivory Coast a gasar cin kofin Afirka

Asalin hoton, Getty Images
- Ta kawo wannan matakin bayan nasara a kan Mozambique da Gabon da yin canjaras da Kamaru.
- Karo na huɗu kenan a baya-bayan nan da za ta fafata a zagaye na biyu - a baya ta kai wannan gurbin a 2019 da 2023 daga baya aka yi waje da ita a 2021.
- Wadda take rike da kofin ba ta yin nasara a zagayen ƴan 16 a Afcon tun bayan Masar da ta yi wannan bajintar a 2010.
- Tun daga 2010, duk wadda take rike da Afcon ba ta iya zuwa matakin kwata fainal tun daga Zambia (2013) da Ivory Coast (2017) da Kamaru (2019) da Algeria (2021) da kuma Senegal (2023).
- A matakin mai rike da Afcon, karo na biyu kenan da Ivory Coast ke haura matakin karawar cikin rukuni, bayan 2017 da take da Afcon.
- Idan har ta yi nasara za ta kai kwata fainal a Afcon karo na 12 jimilla (1992, 1994, 1998, 2006, 2008, 2010, 2012, 2013, 2015, 2019 da kuma 2023).
- Amad Diallo ya ci ƙwallo biyu a Morocco, watakila ya zama ɗan kasar na farko da zai zura uku ko fiye da haka a gasa, bayan kwazon Didier Drogba a 2012.
- Ba a doke koci, Emerse Faé ba a wasannin Afcon, tun bayan da aka bashi aikin, ya ja ragamar wasa bakawi da cin biyar da canjaras biyu.
Kokarin da Burkina Faso ke yi a wasannin Afcon

Asalin hoton, Getty Images
- Ta kawo wannan gurbin ne, bayan nasara a kan Equatorial Guinea da Sudan, sannan Algeria ta doke ta.
- Ta haura matakin zagaye na biyu a 2021, amma aka yi waje da ita a irin wannan matakin a 2013.
- A wasan farko a zagayen ƴan 16 a 2021 ta fara yin 1-1 da Gabon har da karin lokaci daga baya ta yi nasara 7-6 a bugun fenariti.
- Sai ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Mali a zagayen ƴan 16 a 2023.
- Idan ta yi nasara za ta kara a karo na biyar a kwata fainal (1998, 2013, 2017 da kuma 2021).
- Dukkan wasan da ta buga zagayen ziri ɗaya kwale ba ta tashi 0-0
- Issoufou Dayo da Hervé Koffi da Arsène Kouassi da kuma Edmond Tapsoba sun buga wa Burkina Faso dukkan karawa uku ta cikin rukuni a Afcon a Morocco.










