‘Sun yi wa yarana maza huɗu yankan rago’

    • Marubuci, Nicolas Négoce
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
    • Aiko rahoto daga, Nioronigué
    • Marubuci, Abayomi Adisa
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
    • Aiko rahoto daga, Lagos
  • Lokacin karatu: Minti 4

Gargaɗi: Akwai bayanai da za su iya tayar da hankali

Zaune a cikin wani ɗaki mai duhu a wani sansanin ƴan gudun hijira da ke ƙasar Ivory Coast, Aminata Yameoga mai shekara 57 a duniya, na tuna yadda masu iƙirarin jihadi suka kashe mata ƴaƴanta maza hudu a ƙauyensu da ke Burkin Faso.

A shekarar 2022, sa'ilin ba ta gida, ƴan tayar da ƙayar baya masu ɗauke da makamai wadanda suka shafe shekara 15 suna addabar mazauna yankin tsakiyar Burkina Faso, suka kai hari a gidanta.

Dama ‘yan bindigar sun riga sun kwace iko da kauyen da take zaune, inda suka kwace shanu da filayen al’umma, da kuma kashe mutane da dama - ciki har da ‘yayanta mza masu shekara 25 zuwa 32.

”Suka yi wa ‘yayana hudu yankan rago,” kamar yadda ta shaida wa BBC yayin da jikinta ke rawa a lokacin da ta tuna abin da ya faru.

“A lokacin da na dawo gida na iske suna kashe yarona na hudu.”

Aminata ta ce a lokacin sai ta dakko wuka domin far wa maharan, amma sai suka fi karfinta, suka yi mata duka, suka jefar da ita a daji, inda suka bar ta a nan da munanan raunuka a kanta da kafada da kuma wuya.

Ta ce a lokacin wannan harin ne aka raba ta da ‘yarta, kuma har yanzu ba ta kara ganin ta ba.

A shekarar 2023 sai Aminata ta yanke shawarar guduwa zuwa sansanin ‘yan gudun hijira na Nioronigué da ke kasar Ivory Coast mai makwaftaka, inda ta taho da kayanta masu jini a matsayin tunatarwa game da mummunan abin da ya faru da ita.

“Ban san yadda zan yi da rayuwata ba. Ba na da komai,” kamar yadda ta fada wa BBC.

Akalla mutum 10,000 ne aka hallaka a rikicin Burkina Faso, wanda ya tsallaka har kasashen Mali da Ninar masu makwaftaka.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana yankin a matsayin “cibiyar” ayyukan ta’addanci a duniya.

Sojoji sun kwace mulki a dukkanin kasashen uku, inda suka yi alkawarin magance matsalar tsaro.

Sun yanke hulda da kawayensu na Yamma, sannan sun koma wajen Rasha domin neman tallafin soji.

Duk da cewa an kai sojojin Rasha da ke tankin Afirka kasar ta Burkina Faso, amma matsalar tsaron ba ta kare ba, inda babbar kungiyar masu dauke da makamai a kasar ta kasance Jama'at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) mai alaka da kungiyar al-Qaeda.

Kamar Aminata, Hassan Tall, wanda manomi ne mai shekara 60 a duniya ya tsere daga arewacin Burkina Faso a shekarar 2022, tare da matansa umu da yaransa 19 domin tsere wa rikicin.

”Mun tsere wa artabun da ale yo tsakanin kungiyar ‘yan bindiga da jami’an tsaro,” in ji shi. Ya kara da cewa “mun zaci cewa za mu mutu.”

Yanzu yana zaune a sansanin yan gudun hijira na Nioronigué, ya ce barin kasarsu da suka yi na ci masa two a kwarya, amma ya ce bai ga alamar akwai

Yanzu da suke rayuwa a sansanin Nioronigué, ya ce suk da cewa baro gida na masa ciwo, amma ya lura cewa babu alamar sauki a can gida.

Sansanin yan gudun hijira na Nioronigué wanda Aminata da Tall ke zaune, an kafa shi ne tin daga shekarar 2023, kuma yana a kan iyaka ne da Burkin Faso.

Majalisar Dinkin Duniya ce ta kafa sansanin na Nioronigue mai girman eka 12 tare da tallafin gwamnatin Ivory Coast.

An tsara shi ne ya dauki ‘yan gudun hijira 6,000, sai dai yanzu haka wannan sansani da wani mai makwaftaka da shi na Timala na dauke da ‘yan gudun hijira 13,000 - fiye da abin da ya kamata su dauka.

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa fiye da mutum miliyan uku ne rikice-rikice suka tarwatsa a yankin Sahel.

A yanzu haka ‘yan gudun hijarar Burkina Faso sama da 80,000 ne ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira a Ivory Coast.

Lokacin da take nuna jin dadinta, Aminata ta ce “na gode wa gwamnatin Burkin Faso da duk al’ummar kasar.”

“Na tsere daga gidana ne saboda masu ikirarin jihadi sun kore mu. Sun ce so suke yi su kwace kasar,” in ji Aminata.

Labarin kusan iri daya ne tsakanin mazauna sansanin, inda suke alhinin rasa ‘yan’uwansu.

Wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar sun fito ne daga Mali.

Cikinsu akwai wani dan shekara 27 wanda ya kammala karatunsa na digiri.

A kwanakin nan shi da ‘yan’uwansa suka yi wata tafiya mai hadari ta kwale-kwalen katako ta rafin Kwara daga garin Gao na kasar Mali zuwa babban birnin kasar, Bamako, daga nan sai ya hau mota zuwa arewacin Burkin Faso domin neman tsira.

Mai digirin ya ce an tursasa musu baro garinsu ne bayan kashe dan’uwansu mai shekara 24, wanda mayaka ne suka kashe shi.

“Ya kasance mai sana’ar kamun kifi, yana kan hanyar dawowa gida da daddare, kamar yadda ya saba, sai wasu maza a kan babur suka far masa. Wannan abu ne da ke faruwa kusan kullum.

“Mun rika rayuwa cikin firgici, ba mu da tabbaci ko za mu wayi gari a raye “ kamar yadda ya shaida wa BBC.

Tattalin arzikin Ivory Coast na habbaka fiye da na kowacce kasa da ke makwaftaka, sai dai rashin aikin yi da talauci ya kara yawa,