Real Madrid ta ƙwallafa rai kan Saliba, Rashford zai koma United

Lokacin karatu: Minti 2

Chelsea na neman Morgan Rogers, Real Madrid na son William Saliba, yayin da zakarun Premier Liverpool ke neman wasu yan wasa uku, ciki har da biyu daga Bournemouth.

Chelsea na sha'awar dan wasan gaban Aston Villa Morgan Rogers, mai shekara 22, a bazara, yayin da take son dan wasan na Ingila ya kara karfin bayanta. (Independent)

Real Madrid ta sanya dan wasan baya na Arsenal dan kasar Faransa William Saliba, mai shekara 24, a matsayin babban burinta a wannan bazarar. (Marca)

Liverpool na son 'yan wasan bayan Bournemouth Dean Huijsen, mai shekara 20, da Milos Kerkez, mai shekara 21, da kuma dan wasan gaba na Eintracht Frankfurt Hugo Ekitike, mai shekara 22, don karfafa 'yan wasanta da taimakawa wajen kare kofin Premier d ata lashe. (Daily Mail)

Dan wasan tsakiya na Italiya Sandro Tonali yana shirin ci gaba da zama a Newcastle United na dogon lokaci, duk da cewa ana alakanta dan wasan mai shekaru 24 da haihuwa da komawa kasarsa ta haihuwa. (Telegraph)

Manchester City ba ta da niyyar barin dan wasan tsakiyar Ingila Jack Grealish mai shekara 29 ya bar kulob din aro a bazara. (Talksport)

City da Liverpool suna sha'awar sayen dan wasan bayan Italiya Andrea Cambiaso, mai shekara 25, wanda da alama zai bar Juventus a bazara. (Calciomercato)

Marcus Rashford na iya komawa Manchester United da wuri daga aron da yake a Aston Villa bayan dan wasan na Ingila mai shekara 27 ya ji rauni a kafarsa. (Sun)

Rashford a shirye yake a rage masa albashi don samun damar cimma burinsa na komawa Barcelona. (Mirror)

Sai dai ana ganin akwai sarkakiya, domin Barca ba ta son biyan £40m da Villa ta amince a matsayin farashin Rashford. (Independent)

Manchester United da Tottenham duk suna sha'awar sayen dan wasan Faransa Rayan Cherki, mai shekara 21, daga Lyon. (Cought Offside)

Rahotanni sun nuna cewa Villa na sha'awar biyan fam miliyan 21 don siyan golan Espanyol dan kasar Sipaniya Joan Garcia, mai shekara 23. (Cadena)

Fulham ta ce tana sha'awar dauko dan wasan bayan Ingila Ben Johnson, mai shekara 25, yayin da Ipswich ke alhinin nutsewa daga gasar Firimiya. (Sky Sports)

Brazil na tattaunawa da kocin Real Madrid Carlo Ancelotti game da zama sabon kocinta, inda ake ci gaba da tattaunawa game da ma'aikatan da za su dafawa kocin dan Italiya. (Fabrizio Romano)