Abin da tsarin mulkin Najeriya ya ce kan halascin takarar Jonathan

Lokacin karatu: Minti 4

Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027 a Najeriya, wata sabuwar muhawara ta ɓarke a ƙasar kan halascin takarar tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan.

A ƙarƙashin dokokin Najeriya dai sau biyu ne kawai aka yarje wa mutum ya riƙe muƙamin shugaban ƙasar.

Kan haka ne wasu ke ganin tsohon shugaban ƙasar ba shi da hurumin tsayawa takara saboda ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasa har sau biyu.

To sai dai magoya bayansa na cewa abin da dokokin Najeriyar ke nufi shi ne a zaɓi mutum sau biyu, ba rantsuwa ba.

Wannan batu dai ya haifar da zazzafar muhawara a ƙasar, musamman tsakanin ƴansiyasa da ma wasu masana shari'a.

Kan haka ne muka nemi jin ta bakin lauyoyi masana kundin tsarin mulkin ƙasar domin jin abin da dokokin ke nufi, zaɓe ko rantsuwar kama aiki.

Mulkin da Jonathan ya yi a baya

Dakta Goodluck Ebele Jonathan ya fara shan rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Najeriya a 2010, bayan mutuwar tsohon shugaban ƙasar Umaru Musa Ƴar'adua.

Ya ƙarasa wa'adin shekara biyu da suka rage wa Ƴar'adua, sannan ya tsaya takara a zaɓen 2011.

Bayan nasararsa a zaɓen an sake rantsar da Goodluck Jonathan karo na biyu a matsayin shugaban ƙasar, inda ya yi wa'adin shekara huɗu.

Jimilla kenan tsohon shugaban ƙasar ya mulki Najeriya na tsawon shekara shida.

Me doka ta ce?

Barista Abba Hikima Fagge fitaccen lauya ne masanin kundin tsarin mulkin Najeriya, ya kuma ce abin da dokar ke nufi shi ne wa'adin mulki biyu.

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi tanadin cewa duk wanda ya yi wa'adin mulki biyu, daga kan gwamna da mataimakinsa da shugaban ƙasa da mataimakinsa, ba za a sake zaɓarsa a wannan matsayi ba.

Wa'adi biyu: Rantsuwa ko zaɓe?

Dangane da wuraren da ake ta tababa a kai kuwa, Barista Abba Hikima ya ce sashe na 137 (III) na kundin tsarin mulkin ƙasar, wato gyara na huɗu da aka yi wa kundin a 2017 ya yi tanadin cewa idan aka zaɓi mutum, ya kuma mutu ko wani dalili ya sa aka rantsar da mataimakinsa domin ƙarasa wa'adin.

To shi wanda ya ƙarasa wa'adin za a iya zaɓensa ya yi wa'adi guda.

''Wancan da ya ƙarasa za a ƙirga shi a matsayin ya yi wa'adi guda, koda kuwa bai cika shekara huɗu ba, domin ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin cikakken shugaban ƙasa'', in ji lauyan.

Ya ƙara da cewa sashen yana magana a kan rantsuwa ba zaɓe ba domin kuwa cewa ya yi:

''Mutumin da aka rantsar domin kammala wa'adin wani da aka zaɓa a matsayin shugaban ƙasa, ba za a sake zaɓarsa a matsayin shugaban ƙasa fiye da wa'adi ɗaya ba''.

Jonathan zai iya sake tsayawa takara?

Dangane da yiwuwar tsayawar Jonathan kuwa, lauyan ya ce a tsarin doka idan aka yi sabuwar doka, to ''ba ta waiwaye'', tana duba gaba ne, don haka wannan gyara bai shafi Jonathan ba, kasancewar ya yi mulkinsa tsakanin 2010 zuwa 2015, ita kuwa dokar a 2017 aka yi ta.

''Saboda haka idan aka yi amfani da ƙa'idar da ta tanadi cewa doka ba ta waiwaye, to wannan dokar ba ta shafi Jonathan ba, tun da an yi ta bayan mulkinsa'', in ji Abba Hikima.

Haka kuma lauyan ya ce a 2019/2020 an je wata babbar kotu, kuma ta tabbatar da cewa Jonathan ɗin na da damar tsayawa takara.

Sai dai ya ce da aka je kotun ɗaukaka ƙara, ta kori ƙarar, amma bisa dalilai na rashin cika ƙa'idar shari'a.

Lauyan ya ce har yanzu lauyoyi na ci gaba da muhawara tsakaninsu, inda wasu ke ganin ƙa'idar ''doka ba ta waiwaye'' na aiki ne kawai a kan shari'o'in manyan laifuka.

''Suna ganin cewa a sauran shari'u da suka danganci mu'alama doka na iya yin waiwaye'', in ji shi.

''To amma ni a ra'ayina indai ba dokar ce ta faɗa da kanta cewa za ta yi waiwaye ba, to ba za ta yi ba'', kamar yadda ya bayyana.

Ya ƙara da cewa wannan ita ce ƙa'ida ''domin in za a yi doka mai yin waiwaye, to dokar ce za ta tanadi hakan''.

'Kotun Ƙoli ce kawai za ta tabbatar'

Abba Hikima ya ce shi sashe na 137 (III), bai yi maganar cewa zai yi waiwaye ba, saboda haka Goodluck zai iya yin takara a ƙarƙashin dokokin Najeriyar.

Sai dai ya ce abu guda kawai da zai iya warware wannan dambarwa shi ne hukuncin Ƙotun Ƙolin ƙasa.

''Abin da ya kamata a yi kan wannan dambarwa shi ne a je Kotun Ƙolin ƙasar, domin ita ce kawai za ta yanke hukunci na ƙarshe game wannan batu'', kamar yadda ya bayyana.

Kawo yanzu dai shi Goodluck Jonathan bai bayyana ƙarara cewa zai yi takara a zaɓen 2027 ba.

To sai dai wasu daga cikin makusantansa sun ce yana kan tuntuɓar abokan shawararsa game da matakin.

Idan har ya tsaya takara a zaɓen 2027 zai kasance mutum na farko a Najeriya da aka taɓa zaɓa a matsayin shugaban ƙasar ya kuma sake tsayawa takara bayan ya sauka da shekaru masu yawa.