Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ake kashe masu laifi a ɓoye a Saudiyya tare da barin iyalansu cikin duhu
Ba a bayyana wa iyalai lokacin da za a kashe an uwansu, haka nan kuma ba a ba su gawar domin yi mata jana'iza.
Ƴan uwan fursunoni sun sanar da BBC cewar an aiwatar da hukuncin kisa kan mutane da dama ba tare da an sanar da iyalansu ba kafin lokacin.
Wani rahoton ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama ya ce daga 2015 aiwatar da hukuncin kisa ya kusa ninkawa - shekarar da yarima Mohammed bn Salman ya karɓi iko.
Ba a sanar da iyalan Mustafa al-Khayyat kafin aiwatar da hukuncin kisa a kansa ba.
Ba su ga gawarsa ba, kuma ba su san inda kabarinsa yake ba, balle su je su yi masa addua'a.
Lokaci na ƙarshe da suka ji daga wajensa shi ne ta wayar tarho daga gidan yari, inda kalma ta ƙarshe da ya faɗa wa mahaifiyarsa shi ne: "Shikenan Zan tafi. Na ji daɗi tun da kina lafiya."
Bata taɓa tsammanin cewa wannan ne magana ta ƙarshe ba da za ta yi da shi.
Wata ɗaya bayan nan, aka kashe Mustafa - yana cikin mutane 81 da aka kashe a ranar 12 ga watan Maris din 2022, a wani kisa mafi girma da aka yi Saudiyya a tarihi.
Sunan Mustafa na cikin wani dogon jerin sunayen mutane da kungiyar masu bincike wanɗa ya kunshi lauyoyi suka saka - wanda ya haɗa da kungiyar kare hakkin ɗan adam ta 'yan Saudiyya da ke Turai, da ke saka binciken mutanen da ƙasar ta kashe a cikin wani sabon rahoto.
Alkaluman bincike da aka tattara tun 2010, ya gano cewa:
- Yawan mutanen da Saudiyya ke kashewa ya ninka tun bayan da Sarki Salman ya zo kan iko a 2015, inda ya naɗa ɗansa Mohammed bin Salma a manyan muƙamai.
- An yi ta yanke hukuncin kisa don rufe bakin waɗanda ke adawa da tsare-tsaren gwamnati da kuma masu zanga-zanga wanda ya saɓawa dokokin kare hakkin ɗan adam na ƙasa da ƙasa, wanda ya bayyana cewa za a iya amfani da hukuncin ne kawai kan manyan laifuka .
- An kashe mutane akalla 11 da aka tsare tun suna yara a 2015, duk da cewa Saudiyya ta sha nanata cewa tana koƙarin ganin an rage amfani da hukuncin kisa kan yara.
- Gallazawa mutane babbar matsala ce a gidajen yarin Saudiyya har ga waɗanda ke kare hakkin yara.
Kungiyar ta gano cewa an kashe mutane 147 a Saudiyya a shekara da ta gabata, sai dai, ta ce alkaluman za su iya fin haka. Ta kuma ce ƙasar ta sha yanke hukuncin kisa kan 'yan ƙasashen waje - wanda ya kunshi 'yan aiki da waɗanda aka kama da laifin tu'ammali da kwayoyi wanda ba babban laifi bane.
Kusan shekara ɗaya a yanzu, jami'ai basu faɗa wa iyalan Mustafa ba kan yadda aka kashe shi tare da wasu. Ɗan uwansa mai suna Yasser, ya ce suna cikin tashin hankali.
"Bamu san ko an musu jana'izar da ta kamata ba ko kuma an jefar da su cikin daji da teku ba. Bamu da masaniya."
Yasser na magana ne a bainar jama'a karon farko. A yanzu yana zaune a Jamus, inda aka ba shi mafakar siyasa bayan tserewa daga Saudiyya a 2016, saboda tsoron kar abin da ya faru da ɗan uwansa ya faru da shi.
Yasser ya ce ɗan uwan nasa "mutumin kirki ne mai daɗin zama da mutane". Tun 2011, Mustafa na cikin mutanen da suka gudanar da zanga-zanga ta kullu yaumin - da 'yan Shia a ƙasar waɗanda basu da rinjaye suka jagoranta - kan adawa da gwamnatin Saudiyya.
An tsare shi a 2014. Bayan rasuwarsa, wata sanarwa a hukumance ta ce an kashe shi tare da wasu mutum 30 saboda aikata laifuka iri ɗaya - da ya haɗa da yunkurin kisan jami'in tsaro da fyade da fashi da haɗa bam da tayar da zaune tsaye da kuma sayar da makamai da kwayoyi.
"Basu taɓa gabatar da wata hujja ba. Wannan karya ce,'' in ji Yasser - wanda ya ce ɗan uwansa na ƙoƙarin ɗaukaka ƙarar hukunci da aka yanke masa lokacin da hukumomi suka kashe shi tare da wasu maza 80.
"Ba kashe su kaɗai suka yi, sun ɓata musu suna dagan-gan da kuma zarginsu da abubuwan da basu aikata ba."
Bayan samun iko, Yarima Mohammed bin Salman, wanda ainihi yake iko, ya yi alkawarin zamanantar da masarautar ƙasar - inda a wata tattaunawa a 2018 ya bayar da shawarar cewa ƙasarsa, wanda babbar ƙawar ƙasashen yamma, na ƙoƙarin rage amfani da hukuncin kisa.
Sai dai, kusan shekara biyar bayan nan, Saudiyya na cikin ɗaya daga cikin ƙasashen duniya duniya masu yanke hukuncin kisa - duk da jinkirin da ya yi daidai da shugabancin Saudiyya na G20 da kuma farkon barkewar cutar korona.
Yarima bin Salman - wanda ake kira da MBS - ya yi abubuwa saɓanin alkawari da ya yi, a cewar darektan kungiyar ta Reprieve, Maya Foa, lokacin da take magana daga ofishinta na gabashin Landan.
"An zartar da hukunce-hukuncen kisa da dama a kan idonsa da kuma taka masu zanga-zangar son dimokuradiyya."
Ta ce me za mu kira hakan, ban da gwamnatin sirri da ya ta'alaka kan hukuncin kisa, inda ta ce a yawancin shari'o'i da ta gani, babu wanda ya san cewa ma yana kan jerin waɗanda za a kashe.
"Iyalansu basu sani ba. Akwai mutanen da aka kama da waɗanda aka gabatar da su a kotu da kuma waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa da kuma kashe su a cikin sirri."
Ms Foa tace wasu iyalai a kafafen sada zumunta ne suka san cewa an kashe 'yan uwansu - inda ta kwatanta rashin samun bayanai daga wajen hukumomi a matsayin ɗaya daga cikin abin tayar da hankali na kowane ƙara.
Fille kan mutane ita ce hanyar kashe mutane a al'adance da ake amfani da shi a Saudiyya - a baya ana kashe mutane ne a bainar jama'a -inda ake wallafa sunayen waɗanda aka kashe da laifukansu a kan shafukan intanet na gwamnati.
Sai dai, masu fafutukar kare hakkin ɗan adam sun ce amfani da hukuncin kisa ya zama abin da ba a faɗar gaskiya a kai.
Babu wanda na yi magana da shi da ya san yadda ake kashe mutane a yanzu, duk da cewa ana tunanin cewa ana amfani da jami'an harbi.
Hukuncin kisa dai na cikin bangaren tsarin shari'a a Saudiyya wanda Ali Adubisi, darektan kungiyar kare hakkin ɗan ta Saudiyya a Turai, ya ce wasu abubuwa basu kamata ba
"Babu wata kungiyar farar hula ko ta kare hakkin ɗan adam da za ta yi aiki a nan. Idan bamu mayar da hankali kan waɗanda ake kashewa ba, za a yi ta kashe mutane a cikin ɓoye."
Kungiyar kare hakkin ɗan adam ta Human Rights Watch, ta ce maza 41 cikin 81 da aka kashe a watan Maris cikin 'yan Shia marasa rinjaye da kuma "rashin tsari a shari'ar Saudiyya, ya bayar da shawarar cewa akwai alamun ba a yi wa mutanen adalci ba". Sun kuma samu labarin musgunawa mutane da dama.
Karon farko da aka bar Yasser ya ziyarci Mustafa watanni 12 bayan kama shi a 2014, ya kaɗu da abin da ya gani.
"Duk da cewa ya kai shekara ɗaya rabon da mu gan shi, ya kasa tsayawa ya gaishemu.
"Da zarar ya yunkura zai tashi, sai ya faɗi - sannan idan muka tambaye shi, sai ya ce saboda irin gallazawa da aka yi masa ne.
"Mun ga raunuka a jikinsa, inda ya faɗa mana cewa an sanya masa wayoyin wutar lantarki.''
'Yar uwan wani wanda aka tsare, ta faɗa min cewa an musgunawa ɗan uwanta.
"Ya ce a ɗaure kafafunsa tare da lakaɗa masa duka. Bai taɓa tsammanin cewa za a yi amfani da maganar da aka tirsasa mutum yi ba a cikin kararsa,'' a cewar Zainab Abu Al-Khair, wadda ɗan uwanta Hussein ke gidan yari tun 2014.
Hussein - wani direba ɗan ƙasar Jordan da ke wa wani hamshakin ɗan Saudiyya aiki - an kama shi da kwayoyi a cikin motarsa a kan iyaƙar Jordan da Saudiyya. Zainab ta ce ta sane cewa kwayar ba tasa bace.
Da take magana daga gidanta a Canada, ta bayyana yadda iyalan Hussein suke cikin wahala na samun abin kai bakin salati tun bayan kama shi. Yana wani yaro mai buƙata ta musamman, inda bayan jefa shi gidan yari, aka yi wa 'yarsa mai shekara 14 auren dole a Jordan.
A watan Nuwamban bara, Saudiyya ta dakatar da yanke hukuncin kisa kan masu tu'amalli da kwayoyi - matakin da kungiyar kare hakkin ɗan adam ta Majalisar DinkinDuniya ta kira da "abin da ba za a manta ba".
Majalisar Dinkin Duniya ta ce cikin makonni biyu, an kashe maza 17 waɗanda aka kama da irin wannan laifi.
Zainab ta ce mazan da ake ɗaukawa a gidan yarin da Hussein yake, ba a taɓa dawo dasu.
Hakan ya sanya fargaba a zukatan Hussein da 'yar uwarsa Zainab. "Bana iya magana a kansa ba tare da zuciyata ta buga ba,'' in ji Zainab.
"Ina tunaninsa dukkan tsawon rana da kuma dare, ina muggan mafarke-mafarke. Suna tunanin fille kansa - abin na da firgitarwa.
"Ba za ka taɓa sanin wahalar ba. Wasu lokutan ina zama ni kaɗai in yi ta carɓa kuka."
Cikin raɗaɗin da take ciki ya haɗu da yanda wasu ƙasashe suka bar Saudiyya ba tare da kamata da laifi ba.
A watan Maris din bara - kwanaki huɗu bayan kashe maza 81 - Firaministan Birtaniya a lokacin, Boris Johnson, ya haɗu da Mohammed bin Salman don ya yi kokarin karkatar da hankalinsa wajen ganin ya samar musu da mai don maye gurbin shigo da na Rasha.
Fadar Downing Street ta ce mista Johnson ya yi magana kan batutuwan take 'yancin ɗan adam na Saudiyya.
Tun bayan samun iko, Yarima bin Salman ya yi sauye-sauye a bangarorin zamnatakewa da kuma na tattalin arzikin ƙasar - wanda ya haɗa da bai wa mata damar yin tuki - sai dai an biyo bayan hakan da sharuɗan siyasa.
Ofishin Majalisar Dinkin Duniya, ta faɗa wa BBC cewa ta damu matuka kan yadda ake aiwatar da hukuncin kisa a Saudiyya.
"Mun damu kan ƙaruwar alkaluman mutanen da ake yanke wa hukuncin kisa wanda ya haɗa har da yara da kuma kan waɗanda suka aikata ƙananan laifuka kamar na kwayoyi.
Ga waɗanda 'yan uwansu ke gidajen yari, yanzu lokaci ne na fargaba.
'Yar uwan Hussein, Zainab, na zuba ido kan shafin sada zumunta na iyalinsu.
"Wannan ba lokaci bane na hutawa a rayuwa,'' in ji ta. "kowace safiya da kuma yammaci, dole mu duba ko yana raye."