Majalisar tsaron Najeriya ta ce ta yarda ƙasar na cikin mawuyacin hali

Shugabannin tsaro

Asalin hoton, Presidency

Rundunonin sojin Najeriya sun sha alwashin fitowa da wasu sabbin dabarun magance matsalolin tsaron da ke addabar kasar nan da makonnin masu zuwa.

Wannan dai na daga cikin abubuwan da aka tattauna yayin taron majalisar ƙoli ta harkokin tsaron ƙasar da aka yi a ranar Alhamis ƙarƙashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari.

Wannan dai na zuwa yayin da lamarin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a ƙasar da har ta kai ƴan majalisar dattawa daga ɓangaren adawa kiran da a tsige shugaban kasar.

Da yake yi wa manema labarai bayani bayan kammala wannan taron, mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Munguno mai ritaya, ya ce majalisar ta amsa cewar ƙasar na cikin mawuyacin hali.

Kuma Shugaba Muhammad Buhari ya fahimci irin damuwar da ƴan kasar ke ciki game da hakan.

“Muna cikin wani hali mawuyaci matuƙa. Kuma majalisa ta fahimci haka.

“Shugaban ƙasa ya fahimci irin damuwar da jama’a ke ciki, ga ƙaruwar rashin tsaro.

"Na san cewa mutane sun gaji har sun soma karkata ga wasu wuraren domin nemo taimakon yadda za su tsare kansu.

“Amma gaskiyar al’amari shi ne taimako kan samu ne kawai idan kowa na taimakon kowa,” in ji shi.

'A ba mu mako shida'

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Presidency

Munguno ya ƙara da cewa hukumomin tsaro sun sha alwashin nan da makonni masu zuwa za su fara aiki kan wasu sabbin dabaru don maganin tashe-tashen hankulan da ke faruwa.

Hukumomin tsaron sun yi wa shugaban ƙasa alkawarin cewa za a samu sauyi a ƙoƙarinsu duk da cewa akwai wani ɗan cikas ta ɓangaren tsare-tsare da za su iya fuskanta.

“Kuma sun fahimci girman irin hakkin da ke wuyansu,” in ji Munguno.

Mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan tsaron ya kuma ce majalisar ta tattauna kan matakin da aka kai wajen bincike kan harin da ƙungiyar ISWAP ta kai wa gidan yarin Kuje a farkon watan nan, wani al’amari da ya girgiza kowa a duk faɗin ƙasar.

“Haka ma majalisar tsaro na daf da kammala bincike na musamman da take kan abin da ya faru a Kuje.

“Manufar ita ce fitowa da wasu shawarwari kan matakin da za a ɗauka kan waɗanda ke alhakin faruwar wannan abin, da kuma tabbatar da irin hakan ba ta sake faruwa ba har abada a ƙasar nan.”

"A daina yaɗa labaran hare-hare"

Sai dai kuma ya ce majalisar ƙoli ta harkokin tsaron ta damu da irin yadda kafafen watsa labarai ke bayar rahotannin tashe-tashen hankulan da ƙasar ke fuskanta.

Kazalika ba ta jin daɗin irin kalaman da ke fitowa daga bakunan wasu shugabannin siyasa da ake ganin kimarsu a ƙasar.

Ya ce “bugu da ƙari kuma, majalisar ta kuma da mu game da irin rahotannin da kafafen watsa labarai ke bayar wa game da rashin tsaro.

Munguno

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, Babagana Monguno ya ce majalisar tsaro na daf da kammala bincike na musamman da take kan abin da ya faru a Kuje

“Yana da muhimmanci kafafen watsa labarai su fahimci cewa wasu rahotannin da suke bayar wa za su iya ƙara dagula wannan mawuyacin halin da ƙasar ke ciki.

Don haka majalisar ƙoli kan tsaro na kira ga kafafen watsa labarai da su yi hankali da irin abin da suke faɗa.”

Duk da cewa dai majalisar tsaron bisa al’ada takan yi taronta ne sau ɗaya a wata, wannan shi ne karo na uku da take yin taro a wannan watan.

Wannan lamari yana alamta irin girman matsalar tsaron da ƙasar ke ciki a halin yanzu, inda har babban birnin ƙasar ke fuskantar barazana daga ‘yan ta’adda.