Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya kamata ku sani kan Zakkar Fid-da-kai
A yayin da al'ummar musulmi ke daf da kammala azumin watan Ramadan, wani abu da ya wajaba musulmi mai hali ya yi shi ne fitar da zakkar fid-da-kai.
Ita dai wannan zakkar kamar yadda addinin musulunci ya yi tanadi, tana da matuƙar amfani musamman wajen taimaka wa waɗanda ba su da abin da za su sa a baka a lokacin bikin sallah.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce Zakkar fidda kai kamar yadda Bukhari da Muslim suka ruwaito cewa Manzon Allah ya wajabta zakkar fidda kai, ana ƙare azumin watan Ramadan, kuma za a bayar da sa’i ɗaya ne, za kuma a fitar wa mace da namiji da yaro da babba da ɗa da bawa.
Sheikh Daurawa ya ce ke nan wajibi ne a fitar da ita, idan ba a fitar da ita ba ke nan akwai alhaki.
Malam Abubakar Muhammad Abdussalam Gwale Kano ya ce zakka na ɗaya daga cikin rukunai na addinin musulunci, kuma zakkar fidda kai na wajaba ne daga ranar da aka kammala azumin watan Ramadan.
Jinsin abincin da ake fitarwa a matsayin zakkar
Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce abincin da ake fitarwa a matsayin zakkar fid-da-kai, shi ne abincin da aka fi ci a wannan gari a kuma wannan lokaci.
‘’Kamar a Najeriya a ce an fi amfani da shinkafa da gero da masara, su aka fi amfani da su’’, in ji Sheikh Daurawa.
Malam Abubakar Gwale ya ce ya zo a cikin hadisin Abu sa’idunul-Khudri Manzon Allah S.A.W ya ce an farlanta zakkar fidda kai sa’i ɗaya na abinci ko sa’i ɗaya na dabino’’
Malamin ya ce dogaro da wannan hadisi masara da dawa da shinkafa acca da sauran dangogin hatsi duka sun shiga cikin dangin kayan abincin da za a iya fitar da zakkar fid-da-kai da su.
Waɗanda za su fitar da zakkar
Malam Abubakar Gwale ya ce asali kowa ne zai fitar wa kansa, sannan kuma a ƙarƙashinsa waɗanda ba za su iya ba fitarwa ba sai ya fitar musu.
‘’Kamar misali miji zai fitar a matarsa da ‘ya’yansa da bayi da waɗanda ke ƙarƙashinsa waɗanda shi ne yake ciyar da su’’.
Shiekh Aminu Daurawa ya ce wajibi ne miji ya fitar wa da matarsa zakkar matuƙar tana ƙarƙashin ciyarwarsa komai arzikinta.
Lokacin da ya dace a fitar da zakkar
Dangane da lokaci mafi dacewa na fitar da zakkar fid-da kai, Sheikh Daurawa ya ce za a iya fitar da ita kwana biyu kafin ƙarewar Ramadan, wato ranar 28 da 29 ga watan Ramadana.
‘’Wata kila hakan zai taimaka wa wanda za ka ba wa ya yi tanadin abin cefane na abin da zai dafa a ranar sallah, domin ya samu ya yi girki a kan lokaci’’, in ji Sheikh Daurawa.
Shehin malamin ya ƙara da cewa ‘’lokaci na biyu da ake bayar da zakkar fidda kai shi ne lokacin da aka ga watan ƙaramar salla, to a cikin wannan daren mutum zai iya bayarwa har ya zuwa ketowar alfijir’’.
Ko kuma bayan alfijir ya keto, kafin a tafi sallar idi, idan kuwa ta riga ta zama ramuwa da zama sadaka daga cikin sadakoki.
Shi ma Malam Abubakar Gwale ya ce duk wanda bai fitar da zakkar fid-da-kai ba, sai har da aka dawo daga sallar idi, to ba za a rubuta shi a matsayin waɗanda suka yi zakkar fid-da-kai ba, sai dai a ba shi ladan sadaka.
Hikimomin fitar da zakkar
Sheikh Daurawa ya ce hikimar yin zakkar fida-da-kai ita ce domin a wadatar da talakawa da masu ƙaramin ƙarfi abinda za su samu su yi tuwon sallah su wadata a wannan rana.
Hikimomin zakkar fidda kai shi ne ta zama tsarkakewa ga mai azumi a bisa abin da ya faru na rashin sani ko bisa kuskure ko ganganci, cikin abinda Allah baya so ya faru da azumi, kamar yadda Malam Abubakar Gwale ya bayyana.
‘’Kamar maganganun da ba su dace ba, ko ji ko gani bisa kuskure cikin abin da ba ya karya azumi, amma kuma yana tafiyar da ladan mai azumi, to zakkar sai ta zama kamar nafila ce da ke cika abin da aka samu giɓi bisa aikata kuskuren, za ta zama kankare zunubin da ka samu’’, in ji shi.
Mutanen da zakkar ke faɗuwa a kansu
Malam Abubakar Gwale ya ce da ma Allah ba ya ɗora wa duka wani rai wani abu sai abin da zai iya, saboda haka a cewarsa idan mutum ba shi da halin fitarwa gaba-ɗaya, shi yana buƙatar a ba shi, to zakkar ta faɗi a a kansa.
Haka kuma idan mutum yana da abin da zai ci, amma ba shi da abin da ya ɗoru a kai to a nan sai ya bayar da abin da ya samu, a cewar Malam Abubakar.
Adadin abin da ake fitarwa Malam Abubakar ya ce ana fitar da sa’i ɗaya na abinci, shi kuma sa’i ɗaya ke nan mudunnabi guda huɗu ke nan.
Malamin ya kuma ce mudunnabi shi ne kamar cikon hannu biyu na mutum matsakaici, kusan kilo uku ke nan, a cewar malamin.