Gaskiyar batun da ke cewa an yanke wa mutum 15,000 hukuncin kisa a Iran

Asalin hoton, Getty Images
Firaministan Canada Justin Trudeau ya goge wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta da ke ɗauke da wani ikirarin da ba gaskiya ba da ke cewa hukumomin Iran sun yanke wa wasu masu zanga-zanga 15,000 da ake tsare da su hukuncin kisa.
Ikirarin ya yaɗu kamar wutar daji a Tuwita da Instagram da Reddit da Tiktok a wannan makon.
Zuwa yanzu an yi kiyasin cewa mazu zanga-zanga 15,000 aka kama, inda aka gurfanar da mutun 2,000 tare da yanke musu hukuncin kisa a hukumance.
A ƙalla masu zanga-zanga 20 ne a yanzu suke fuskantar hukuncin kisa, kamar yadda wata ƙungiyar kare hakkin ɗan adam ta Iran mai cibiya a Norway ta faɗa, tana mai ambatar rahotannin hukumomi.
Mafi yawan masu zanga-zangar da ake tsare da su ɗin har yanzu ba a gurfanar da su a gaban shari'a ba.
"Canada ta yi tur da matakin rashin imani na gwamnatin Iran kan yanke hukuncin kisa ga kusan masu zanga-zanga 15,000," wannan shi ne saƙon da aka wallafa a shafin Mr Trudeau na tuwita da safiyar ranar Talata, kafin daga bisani a goge shi.

Asalin hoton, Twitter
Daga baya ofishinsa ya fitar da wata sanarwa da ya aike wa BBC cewa: "An wallafa saon ne bayan samun wasu rahotanni da ba su cika ba kuma marasa cikakkun hujjoji. A don haka, tuntuni aka goge saon."
Da BBC ta tambayi ko daga ina maganar ta samo asali, sai ofishin firaministan ya ce "Ya samo asali ne saboda rahoton da ƙungiyoyin kare hakkin ɗa adam na ƙasa da ƙasa suka fitar kan suna nuna damuwa kan yanayin da ake ciki da kuma yiwuwar ƙara samun wadanda za a yanke wa hukunci kisa."
Wani labari da ya bayyana a kafar yada labaran Newsweek a Talatar da ta wuce ya ce majalisar dokokin Iran ta "kaɗa ƙuri'ar nuna amincewa da yanke wa masu zanga-zangar hukuncin kisa."
Fitattun masu amfani da shafukan Tuwita da Instagram da dama sun ɗauki wannan labari.
Daga baya an sabunta labarin don bayyana cewa majalisar dokokin ta ma fitar da wata takarda da mafi yawan ƴan majalisar suka sanya wa hannu kan neman a yi wa masu zanga-zanga tsattsauran hukunci.
BBC ta tuntuɓi Newsweek don jin ta bakinta a kan gyara kuskuren.
Wani hoto da aka yaɗa sosai a shafukan sada zumunta ya nuna cewa "Iran ta yanke wa mutum 15,00 hukuncin kisa - a matsayin koya wa ƴan tawaye darasi".
Wata ƴar fim ta Amurka Viola Davis na daga cikin fitattun mutanen da suka yaɗa hoton, duk da cewa dai daga baya ta goge saƙon.

Asalin hoton, INSTAGRAM
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Labarin ƙaryar da ke cewa an yanke wa mutum 15,000 hukuncin kisa an alaƙanta shi ne da yawan mutanen da hukumomi suka kama a lokacin zanga-zangar da aka yi a fadin Iran, da kuma irin fassarar baibai da aka yi wa buƙatun ƴan majalisar dokoki masu tsaurin ra'ayi kan tsattsauran hukuncin da za a yanke wa masu zanga-zanga.
An fara zanga-zangar ne sakamakon kisan wata atashiya Mahsa Amini mai shekara 22 a watan Satumba, bayan da ƴan sanda Hisba masu tabbatar da ɗa'a suka kama ta kan zargin taka dokar da ta ce dole mata su dinga sa hijabi.
Iran ta mayar da martani ta hanyar yin wani mummunan samame. Shugabannin Iran sun bayyana zanga-zangar a matsayin bore wanda suka zargi maƙiyan ƙasar da rurutawa.
A ƙalla masu zanga-zanga 326 da suka haɗa da yara 43 da mata 25 ne aka kashe, a cewar ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam na Iran.
Kamfanin dillancin labarai na masu fafutukar kare hakkin ɗan adam HRANA, wacce ba a ƙasar cibiyarta take ba, ta ce yawan waɗanda aka kashe ya kai 344, ciki har da yara 52, sannan ta ce an kama wasu masu zanga-zangar 15,820.
Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam sun yi gargaɗi cewa mai yiwuwa hukumomi suna shirin "gagguta yanke wa mutanen hukuncin kisa" da zaman gidan yari mai tsawo.
End of Karin wasu labaran da za ku so ku karanta
An sha sukar ɓangaren shari'a na Iran kan tayuye wa mutane hakkinsu wajen ƙin yin shari'ar adalci, da hana su damar ganin lauyoyinsu.
A makon da ya gabata ne babban mai shari'a na ƙsar Gholamhossein Mohsen ya ayyana cewa za a gano "manyan masu shirya boren" nan ba da jimawa ba tare da yanke musu hukuncin da zai zama gargaɗi ga ƴan baya.
Ya ce za a yanke hukuncin kisa ga masu mallakar makamai da kawo cikas ga tsaron ƙasa.
Sai dai mafi yawan masu zanga-zangar ba sa ɗauke da makamai.
A farkon wannan watan ne kamfanin dillancin labarai na Iran, Irna ya ruwaito cewa ƴan majalisar dokokin ƙasar 227 daga cikin 290 sun fitar da sanarwa ga ɓangaren shari'a suna buƙatar da ɗauki mataki kan masu tunzura zanga-zanga tare da yanke hukuncin kisa kan masu son jawo yaƙi a ƙasar.
Amma bayan da aka yi ta Allah-wadai a ciki da wajen ƙasar, wani kamfanin dillancin labarai na Iran mai alaƙa da majalisar dokokin ya ƙaryata rahoton da ke cewa ƴan majalisar sun fitar da takardar neman a yanke hukuncin kisa, duk da cewa ƴan majalisa masu tsattsauran ra'ayi sun tabbatar da cewa sun sanya hannu a kan takardar.

Asalin hoton, Getty Images
Takardar ƴan majalisar ta yi sanadin yaɗuwar labaran ƙrya cewa majalisar dokoki ta kaɗa ƙuri'ar cewa a yanke wa masu zanga-zanga 15,000 da ake tsare da su hukuncin kisa.
Bangaren shari'a ne ke da alhakin yanke wa masu zanga-zanga hukuncin kisa.
Iran na daga cikin ƙsashen da ta fi yanke hukuncin kisa a duniya.
Daga shekarar 2010 ta yanke wa mutum 6,885 hukuncin kisa kan laifukan kisan kai da na tu'ammali da ƙwaya, a cewar ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam.











