Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yunwa na ƙara ta'azzara a arewa maso gabashin Najeriya - ICRC
Hauhawar farashin kayan abinci da faɗuwar darajar naira a Najeriya sun ta'azzara matsalar yunwa a arewa maso gabashin ƙasar, a cewar rahoton ƙungiyar agaji ta International Committe of the Red Cross (ICRC).
Rahoton da ta fitar ranar Litinin ya ƙara da cewa rashin wadatar abinci da ake fama da shi a yankin wanda rikicin Boko Haram ya tagayyara ya ƙara jefa miliyoyin mutane cikin ƙarancin abinci mai gina jiki.
'Yan Najeriya na fama da hauhawar farashi mafi muni cikin shekara 18 ne tun bayan sanarwar da Shugaba Bola Tinubu ya bayar a watan Mayu ta cire tallafin man fetur, abin da ya sa farashin litar man fetur ya zarta naira 600 - maimakon ƙasa da naira 200 da ake sayar da shi.
Alkaluman hukumar ƙididdiga ta ƙasa na baya-bayan nan sun nuna cewa hauhawar farashi ta kai kashi 26.72 cikin 100, wadda ita ce mafi muni cikin shekara kusan 20.
"Kafin yanzu, ana sayar da buhun masara kan naira 40,000, amma yanzu ya kai naira 70,000," kamar yadda wani ɗan kasuwa a garin Gwoza na jihar Borno, Abubukar Isa, ya faɗa wa ICRC.
"A da muna sayar da kwano ɗaya kan naira 400 zuwa 500 amma yanzu ana sayar da shi naira 1,000 zuwa 1,200. Dalili shi ne ƙarin farashin man fetur."
Sakamakon cire tallafin na fetur, ICRC ta ce farashin kayan abinci na tsakatsaki ya ƙaru da kashi 36 cikin 100, yayin da kuɗin sufuri ya ƙaru da kashi 78.
"Sakamakon haka, dubban iyalai, musamman 'yan gudun hijira, ba su iya sayen abinci mai yawa da inganci da suka saba saya a baya, abin da ke jawo ƙaranci da rashin inganci na abincin da suke ci," in ji rahoton.
Kazalika, kuɗaɗen da suke samu daga ayyukan ƙwadago ma da kuma su kansu ayyukan yin "sun ragu ko kuma ba su ƙaru ba a kan yadda suka saba samu tun bayan cire tallafin man".
Abubakar Isa ya ƙara da cewa: "A da muna iya cin abinci sau biyu ko uku a rana, amma yanzu da kyar muke samun karin safe, ba a ma maganar ruwan sha. An koro 'ya'yanmu daga makaranta saboda ba mu saya musu litattafai ba."
Rikicin Boko Haram ya kashe aƙalla mutum 35,000 a Najeriya kuma akasarinsu a arewa maso gabas, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya. Kazalika wasu 315,000 sun mutu sakamakon rikicin amma ba kai-tsaye ba, inda kuma ya raba fiye da 3,600,000 da muhallansu.
Lamarin ya fi shafar masu ciki da ƙananan yara
Shekarun da aka shafe ana rikicin ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi a arewa maso gabas na ci gaba da shafar hanyoyin samu da kuma kasuwanci, abin da ke jawo hana ayyukan noma.
Rahoton ICRC ya ce har yanzu akwai mutum miliyan 2.2 da ke gudun hijira a yankin, yayin da miliyan 4.3 ke buƙatar tallafin abinci.
"Ya zuwa watan Agustan 2023, yara 'yan ƙasa da shekara biyar miliyan 1.53 ne suka fuskanci lalurar tamowa mai tsanani a jihohin Borno da Yobe da Adamawa," a cewar rahoton.
ICRC ta lura da yadda ake samun ƙaruwar yara 'yan ƙasa da shekara biyar da ke fama da tamowa mai tsanani. Daga 2020 zuwa 2023, adadin yaran da ake kwantarwa a asibiti sun ninka fiye da sau biyu.
Daga Janairu zuwa Satumban 2023, yaran da ke fama da tamowa 'yan ƙasa da shekara biyar sama da 6,000 ne da kuma mata masu ciki fiye da 10,000 suka samu kulawa a cibiyoyin da ICRC ke ba da tallafi.
"Yau da gobe, adadin masu fama da yunwa na ƙaruwa saboda yanzu mutane ba su iya samun abinci mai gina jiki," in ji mataimakin shugaban sashen ayyukan tattalin arziki na ICRC a Najeriya.