Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kuɗin fansa da aka bai wa ƴan bindiga ya haura naira tiriliyan biyu a Najeriya - NBS
Wani rahoto da hukumar tattara alƙaluman Najeriya, NBS ta fitar ranar Litinin ya nuna irin girman matsalar tsaro a Najeriya musamman abin da ya shafi garkuwa da mutane.
Rahoton mai taken Laifukan da aka fuskanta da kuma jin ra'ayin mutanen kan sha'anin tsaro na 2024, ya ce tsakanin watan Mayun 2023 da Afrilun 2024, an kashe ƴan Najeriya 614,937 sannan an yi garkuwa da mutum miliyan 2,235,954.
Rahoton ya kuma bayyana cewa an biya masu garkuwa da mutane kuɗin fansar da suka kai yawan naira tiriliyan 2.2, kuma hakan na nufin akan biyu naira miliyan 2.7 ga kowane mutum.
Rahoton ya ƙara nuna yadda matsalar ta fi shafar yankunan karkara inda aka samu kisan mutum 335,827 idan aka kwatanta da mutum 279,110 a birane.
Dangane kuma da yankin da ya fi fuskantar matsalar, rahoton na NBS ya nuna cewa yankin arewa maso yammacin Najeriya ne ya fi fuskantar matsalar inda yake da alƙaluman mutanen da aka kashe mafi yawa na 206,030, sai kuma yankin arewa maso gabashi da ke biye masa da 188,992, yayin da yankin kudu maso yammaci ke da alƙluma mafi ƙaranci na 15,693.
Yankin na arewa maso yammacin Najeriyar dai shi ne a kan gaba wajen yawan mutanen da aka yi garkuwa da su inda aka sace mutum 1,420,307 a yankin, sai kuma yankin arewa ta tsakiya da ke biye da sace mutum 317,837 sannan yankin kudu maso gabashi na da alƙaluma masu yawan 110,432 da aka yi garkuwa da su a tsawon watannin 12.
Dangane kuma da yankin da ya fi biyan kuɗin fansa masu yawa, rahoton ya nuna cewa a arewa maso yammaci jama'a sun biya tsabar kuɗi har naira tiriliyan 1.2, sai kuma kudu maso gabas da aka biya naira biliyan 85.4.
Kuma abin da hakan yake nufi shi ne arewa maso tsakiya ne ya yi zarra a fagen biyan kuɗin fansa.