Harris ko Trump? Wa ƴan China ke fata ya samu nasara a zaɓen Amurka?

Wasu matan ƴan ƙasar China guda biyu sanye da tufafin al'ada da wasu taurari guda huɗu.
    • Marubuci, Laura Bicker
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, China correspondent, Beijing
  • Lokacin karatu: Minti 5

A China, mutane suna bibiyar zaɓen Amurka sosai. Suna fargabar cewa duk wanda ya samu nasara a zaɓen na Amurka, dole nasararsa za ta kawo wani sauyi a ɓangarori da dama na rayuwa a cikin ƙasar, da ma rayuwar ƴan ƙasar mazauna wasu ƙasashe.

"Yaƙi ne ba ma so ya ɓarke," in ji Mista Xiang, a daidai lokacin da waƙa take tashi a wani dandali, wasu kuma suna gefe suna tiƙar rawa.

Ya zo dandalin Ritan ne domin ya koyi rawa da wasu harkokin nishaɗi.

Suna yawan taruwa a dandalin, wanda ke da nisan wasu ƴan ɗaruruwan mitoci daga birnin Beiging, mazaunin ambasadan Amurka da ke China.

Bayan rawar da suke tiƙa, batun zaɓen Amurka ma na cikin abubuwan da suke yawan tattaunawa.

Zaɓen na zuwa ne a lokaci mai muhimmanci ga ƙasashen biyu masu ƙarfin iko a duniya.

"Lamarin zaɓen na damuna matuƙa saboda yana zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin China da Amurka take samun tangarɗa," in ji Mista Xiang, wanda ya kai shekara 60, sannan ya ƙara da cewa shi zaman lafiya yake so.

Mutane sun taru domin su ji me zai ce. Amma da yawansu sun ƙi bayar da cikakken sunansu kasancewar a ƙasar, an amince a tattauna batun shugaban ƙasar Amurka, amma faɗin magana mara daɗi a kan shugaban ƙasar zai iya shigar da mutum matsala.

Sun ce suna fargabar ɓarkewar yaƙi - ba wai yaƙi tsakanin China da Amurka ba kaɗai, har ma da ta'azzarar yaƙin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya da na Ukraine.

Wannan ya sa Mista Meng, wanda ya kusa shekara 70 yake fata Donald Trump zai lashe zaɓen.

"Duk da ya ƙaƙaba wa China ƙarin haraji, amma ba mutum ba ne mai son yaƙi. Mista Biden ya fara yaƙe-yaƙe da yawa, wanda hakan ya sa mutane da dama ba su sonsa. Mista Biden ne ya goyi bayan Ukraine a yaƙinta da Rasha, kuma Ukraine ta yi mummunar rashi," in ji wani mutum.

Ana cikin maganar, sai wasu mata da suke naɗar bidiyo suka tsoma baki, "Donald Trump ya bayyana a muhawara cewa zai kawo ƙarshen yaƙin Ukraine a cikin awa 24 da ɗarewarsa karagar mulki," in ji ɗaya daga cikinsu.

"Ita Harris ban santa ba sosai, amma muna tunanin tana da ra'ayi iri ɗaya da shugaban ƙasa Biden, wanda yake goyon bayan yaƙi."

Masu rawa a Tashar Ritan suna nishaɗi.

China ta buƙaci ƙasashen duniya su tabbatar an tsagaita wuta a Gaza, tare da bayyana alaƙarta da abin da ta kira, "ƴanuwa Larabawa" a Gabas ta Tsakiya, kuma ta soki Amurka bisa goyon bayan da take bai wa Isra'ila.

A daidai lokacin da masu sharhi da dama suke amannar cewa China ba ta da wani gwani a zaɓen na Amurka, da dama suna ganin Kamala Harris ba ta da masoya sosai a tsakanin mutanen ƙasar da shugabanni.

Amma wasu suna ganin za ta fi daidaita al'amura sama da Trump idan aka zo batun babban batun da ke tsakanin China da Amurka wato batun Taiwan.

"Ba na ƙaunar Trump. Ba na tsammanin dangantaka za ta gyaru tsakanin Amurka da China - matsalolin sun yi yawa, irin su batun tattalin arzikin duniya da ma matsalar ƙasar Taiwan," in ji wani mahaifi da zo tashar da ɗansa mai shekara huɗu.

Yana fargabar batun Taiwan zai iya ta'azzara ya riƙiɗe zuwa tarzoma.

Wani yaro sanye da takunkumin fuska a tashar Ritan.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Ba na so ɗana ya shiga aikin soja," in ji shi.

China tana cewa tsibirin Taiwan tana cikin yankinta ne, sannan shugaban ƙasar, Xi ya ce "dawo da ita cikin ƙasarsa tilas ne," inda ya bayyana yunƙurinsa na dawo da ita da ƙarfi da yaji.

Amurka tana da alaƙa da China a hukumance, amma kuma tana cigaba da zama babbar ƙasar da ke goyon bayan Taiwan a duniya.

A doka, Amurka tana da alhakin taimakawa Taiwan da makaman kare kanta, sannan Joe Biden ya bayyana cewa ƙasarsa za ta kare Taiwan, inda wannan maganar ta kawo ƙarshen raba ƙafar da ake zargin Amurka da yi.

Har yanzu Harris ba ta nuna amincewarta da maganar ta Biden ba, da aka tambaye ta a wata tattaunawa a ƴan kwanakin nan, sai ta ce, "za su tabbatar da tsaro da amincin kowace ƙasa."

Shi kuma Donald Trump yarjejeniya ya nema a shiga, maimakon diflomasiyya, inda ya ce Taiwan ta biya kuɗi idan tana son kariya daga Amurka.

Ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke damun ƴan China a game da batun tsohon shugaban ƙasar shi ne, ya bayyana cewa zai ƙaƙaba harajin kashi 60 a kan kayayyakin ƙasar China.

Wannan kuma abu ne da ƴan kasuwar China ba sa so a yanzu, a daidai lokacin da ƴan kasuwar ƙasar suke ƙara ƙaimi wajen fitar da kayayyakin da suka haɗa zuwa ƙasashen waje.

Shi ma shugban ƙasa Biden ya ƙara haraji a kan motoci masu amfani da lantarki. Ita kuma China ta yi amannar cewa wannan wani mataki na dusashe haskenta na ƙara girma a fagen tattalin arziki a duniya.

Xi da Trump a Beijing a 2017 suna tsaye a gaban wasu fulawoyi suna nuna wani abu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban ƙasa Trump ya gana da Xi na China a Beijing a shekarar 2017

"Ba na tunanin zai amfani Amurka idan shugabanta ya ƙara wa China haraji," in ji Mista Xiang, wanda kuma haka ne ra'ayin wasu da dama da muka zanta da su. Takunkumin zai shafi mutanen Amurka, in ji shi.

A dandalin, Lily da Anna, masu shekara 20 da 22, waɗanda suke samun labarai daga kafar TikTok, sun ce, "ƙasarmu babbar ƙasa ce mai ƙarfi," in ji su. Sun nuna alamar ƙaunar ƙasarsu ta China.

Wata mata tana ɗaga wa wani hannu a dandalin Ritan.
Bayanan hoto, Wani wajen sayar da abinci a dandalin Ritan

Wasu kuma, kamar Lucy mai shekara 17, suna da sha'awar zuwa Amurka karatu ne watarana.

Lucy ta ce tana farin cikin ganin ƴar takara mace. "Takarar Harris ta fito da wata nasara ga mata da daidaton jinsi."

Ba a taɓa samun shugaba mace ba a China, sannan babu mace ko ɗaya a cikin kwamitin ministocin ƙasar, wadda ake kira da Politburo, wadda mafi yawansu ƴan jam'iyyar Communist ne.

Haka kuma Lucy na fargabar adawar da ke tsakanin ƙasashen guda biyu matsala ce, inda ta ce zai fi kyau ƙasashen biyu su gyara alaƙarsu.

Jaririya tana rarrafe a cikin dandalin, tare da wata babbr mace a bayanta.

Xi yana da burin ba ƴan Amurka 50,000 damar zuwa karatu a China nan da shekara biyar masu zuwa. Amma a wata tattaunawa da BBC na kwana-kwana nan, ambasadan Amurka a China, Nicholas Burns ya zargi wasu daga cikin jami'an gwamnatin da yi wa shirin ƙafar rago.

A ɗaya gefen kuma, ɗaliban China da malamai da suke Amurka, sun yi zargin ana muzguna musu a iyakokin shiga Amurka.

Sai dai duk da haka, Lucy tana da ƙwarin gwiwar watarana za ta je Amurka, domin tallata al'adun China. Sannan ta buƙaci ƴan Amurka su riƙa zuwa ziyara China.

"Wataƙila ba mu cika magana da fita sosai kamar mutanen Amurka ba, amma muna maraba da baƙi," in ji ta a daidai lokacin da take tafiya wajen ƴanuwanta.

BBC photographs by Xiqing Wang