Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Qatar 2022: Netherlands ta kori Amurka daga Kofin Duniya
Netherlands ta tsallake rijiya da baya zuwa zagayen semi fayinal a Gasar Kofin Duniya yayin wasan kwata fayinal tsakaninta da Amurka, inda ta cinye wasan da 3-1.
Tawagar mai horarawa Louis van Gaal ta kai hari cikin nasara a minti na 10 da take wasa lokacin da Memphis Depay ya ci ƙwallon da Denzel Dumfries ya bugo masa.
Netherlands ta sake jefa ƙwallo a raga ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, wadda Daley Blind ya ci.
Amurka ta matsa wa Netherlands tun bayan da ta farke ɗaya a minti na 76 da ƙwallon da Haji Wright ya jefa a ragarta.
Ba a tashi daga wasan ba sai da Dumfries ya zira ta uku a ragar Amurka.
Sakamakon na nufin Amurka ta zama ƙasa ta farko da ta fita daga gasar a zagayen kwaf ɗaya.
Argentina za ta fafata da Australiya a ɗaya wasan da za a yi a filin wasa na Al Rayyan da ke Qatar.