Yadda za ku kare kanku daga cutar murar da ke barazanar mamaye duniya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Kate Bowie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Health, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 3
Ƙasashen duniya da dama na fama da wata matsananciyar mura a daidai wannan lokaci, sakamakon nau'in wata ƙwayar cuta, inda ƙwararru suka yi gargaɗin ɗaukar matakai.
Ƙwayar cutar wadda ake alaƙanta ta da ƙaruwar alamomin mura a ƙasashen Japan da Birtaniya, a yanzu an fara ganin yanayinta a faɗin nahiyoyi da dama.
Mutane ba su ga irin na'uinta na yanzu ba cikin tsawon shekaru - hakan na nufin akwai rashin garkuwa a kanta.
Mece ce nau'in murar ta H3N2?
Ƙwayoyin cutar mura suna sauyawa lokaci zuwa lokaci kuma masana kimiyya sun yi duba kan yadda lamarin ya faro saboda a sake inganta allurorin riga-kafin daƙile ta.
A yawan lokuta ƙwayoyin cuta na sauyawa kaɗan - sai dai a wasu lokutan suna sauyawa baki-ɗaya nan take.
An ga sauyi har bakwai kan na'uin murar ta H3N2 da aka cika samu kowace shekara, abin da ya janyo "karuwarta", a cewar Farfesa Derek Smith a jami'ar Cambridge da ke Birtaniya.
"Murar na dab da karaɗe faɗin duniya," kamar yadda ya shaida wa BBC.
Shin wannan nau'i na cutar ce mafi tsanani?
Wannan cuta ta mura da aka fi sani da H3N2 "subclade K", nau'i ne da ake samu kowace shekara, wanda mutane ba su cika kamuwa da shi ba a ƴan shekaru da suka wuce.
Don haka, yayin da alamomin cutar ba za su yi tsanani kamar wasu ba, wannan rashin garkuwa na nufin cewa akwai yiwuwar mutane za su iya kwanciya rashin lafiya da kuma yaɗa ta.
Akwai buƙatar a tuna cewa wasu mutane za su kamu da mura ba tare da sun nuna wasu alamu ba, yayin da wasu ke kamuwa da mura nan take da ciwon jiki da kuma gajiya - sai dai cutar za ta fi tsanani a jikin tsofaffi da kuma mutane marasa galihu.
"Ba mu ga irin wannan ƙwayar cuta ba na tsawon lokaci, ba a cika ganin abubuwan ba," a cewar Farfesa Nicola Lewis a wata cibiyar lafiya a Birtaniya.
"Abun yana damuna, matuka da gaske," kamar yadda ta ƙara da cewa. "Ba na cikin fargaba, amma ina cikin damuwa."
Shin sanyi ne, ko mura ko kuma korona?
Alamomin da dama tsakanin sanyi, mura da kuma ƙwayoyin cuta irin covid, na ɗaukar lokaci, sai dai akwai wasu alamomi da za su sa ka gane wane me kake ɗauke da shi.
Sanyi ya kan zo sannu a hankali, inda zai shafi hancinka da kuma maƙogoro.
Mura kuwa tana zuwa nan take haɗe da ƙarin ciwuka, atishawa da gajiyar jijiyoyi.
A ɗaya gefen, korona na da alamomi iri ɗaya da mura, amma abu ɗaya da ya bambanta su shi ne rashin jin wari ko ɗanɗano. Wani ƙarin bambancin shi ne "jin zafi" a maƙogoro. Wasu lokutan har da amai da gudawa.
Ta yaya zan kare kaina daga ƙwayar cutar?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Samun riga-kafin cutar mura na ɗaya daga cikin hanyoyi da suka fi dacewa wajen kare kai daga kamuwa da cutar, duk da cewa babu allurai a ƙasa da za su iya magani nan take kan nau'in cutar da ke sauyawa.
"Wata kariyar ta fi babu ita kwata-kwata, sai dai a wannan shekara akwai yiwuwar ita ce shekarar da ba za a samu kariyar da ta kamata ba, kamar na sauran shekaru," a cewar Farfesa Christophe Fraser daga jami'ar Oxford a Birtaniya.
"Lamarin ba shi da kyau," ya shaida wa BBC.
"Nau'in cutar ta subclade K da ke yawo a yanzu yana da bambanci da irin wanda aka saba gani a baya, don haka idan ba ka yi riga-kafi a wannan shekara ba, akwai yiwuwar za ka kamu da mura mai tsanani," in ji Nicola Lewis.
Babban alfanun riga-kafin shi ne ana hasashen zai daƙile tsananin cutar maimakon dakatar da kai kwanciya rashin lafiya ko kuma rage yaɗuwarta.
Akwqai alluran riga-kafin mura a faɗin duniya - sai dai samun damar kai wa gare su ya bambanta daga yanki zuwa yanki.
A Birtaniya, ana bayar da su kyauta ga mutanen da suka haura shekara 65, da masu juna biyu ko kuma waɗanda suke nau'o'in cutuka na daban. Wasu na da zaɓin biya.
Dakatar da yaɗuwar cutar wata hanya ce mai kyau. An rufe wasu makarantu a Japan da Ingila domin daƙile yaɗuwarta - waɗanda ƙasashe ne da suka fara fuskantar murar.
Rufe baki yayin tari da kuma atishawa da wanke hannu akai akai da sabulu da ruwa mai ɗumi yana da mtukar muhimmanci, a cewar Dakta Susanna McDonald, shugabar kula da wani shiri kan ƙwayoyin cutar mura a Birtaniya.
Mutanen da ke ɗauke da murar su zauna a gida, amma idan za su fita, kada su riƙa shiga cikin taron jama'a, kamar yadda ta faɗa wa BC.
"A bayar da tazara daga sauran mutane idan kuma ka buƙaci saka takunkumin fuska, hakan zai taimaka wajen kaucewa yaɗuwar cutar zuwa ga wasu," in ji ta.











