Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Za mu tare a Sokoto har sai mun ga bayan ƴanbindiga'
Ƙaramin ministan tsaron Najeriya Bello Matawalle ya ce shi da manyan hafsoshin tsaron ƙasar za su tare a jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin babban hafsan tsaro, har sai sun ga bayan su Bello Turji da fatattakar yanbindigar da suka addabi jihohin arewa maso yammaci.
Sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar ta kuma tabbatar da cewa ƴan bindiga sun ƙona wasu manyan motocin sojin ƙasar masu sulke sun maƙale a wani daji a jihar Zamfara, lokacin da suke kan hanyar su ta yaƙi da ƴanbindiga a jihohin arewa maso yamma.
Wannan kuma na zuwa bayan wani bidiyo da ke yawo a kafofin sada zumunta na intanet da ke nuna ƴanbindiga suna iƙirarin ƙwace motocin yaƙi na rundunar sojin Najeriya.
Bidiyon ya nuna ƴanbindigar riƙe da makamai tare da nuna riƙaƙƙen ɗanbindiga Bello Turji da yaransa suna murna a cikin daji, kusa da wasu manyan motocin sulke na dakarun Najeriya.
Sai dai ma’aikatar tsaron ƙasar ta yi martani inda ta ce motocin sun maƙale ne a cikin laka, a lokacin da suke ƙoƙarin shiga daji domin aikinsu na kawar da ƴanbindiga.
Sanarwar da daraktan yada labaran da hulɗa da jama’a na ma’aikatar tsaron Najeriya, Henshaw Ogubike ya fitar ta ce ‘‘bayan maƙalewar motocin ne aka umarci sojojin da ke cikinsu, su ja da baya domin gudun kada a yi masu kwanton ɓauna.
"A cikin wannan yanayi ne ƴa bindigar suka samu kai wa ga motocin har suka naɗi bidiyon da suka yaɗa," a cewar sanarwar.
Ma’aikatar tsaron ƙasar ta ce gwamnati na takaicin ayyukan ƴanbindiga da suka addabi yankin Arewa maso Yamma.
Ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle, wanda daga ofishinsa ne aka fitar da sanarwar, ya ce shi da hafsan hafsohin tsaro, da sauran manyan hafsohin sojin Najeriya za su koma Sokoto su tare, har sai an fatattaki Bello Turji da sauran ƴanbindiga daga yankin.
Sanarwar ta ayyano ƙaramin ministan tsaro na bai wa jama’ar jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina da kuma Kebbi tabbacin cewa a wannan karo, babu ja da baya har sai an yi nasarar kawar da ƴanbindigar yankin da kuma wanzar da tsaro a yankin da ƙasa baki ɗaya.
Shi dai bidiyon da ake yaɗawar ya nuna motocin sojin Najeriyar a maƙale cikin laka, kuma babu inda a cikin bidiyon aka ga motocin na tafiya, sannan babu alamar wani jami’in soji a wajen.
Ma'aikatar tsaron Najeriya ta ce motar yakin ta maƙale ne a garin Kwashabawa da ke yankin ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.
Matsalar tsaro, musamman ta ƴanbindiga a yankin Arewa Maso Yamma ta daɗe tana addabar yankin, duk da cewa gwamnatoci da hukumomin tsaro sun sha cewa suna bakin ƙoƙarin su wajen magance matsalar, amma da alama akwai sauran aiki a ƙasa domin kuwa mutanen wannan yanki dai sun sha fitowa suna cewa ƙoƙarin da gwamnati ke magana a kai, su fa har yanzu ba su gani a ƙasa ba.