'An samu raguwar kuskuren VAR da kashi 80'

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban alƙalan wasa Howard Webb ya ce an samu raguwar kuskuren na'urar da take taimakawa alkalan wasa da kashi 80 ciki 100 a wannan kakar.
Yanzu an cika shekara biyar kenan da aka fara amfani da VAR a Premeir Lig, yadda take aiki na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce.
A cewar rahoton wata ƙungiya da ke bibiyar wasanni mai zaman kanta (KMI) akwai kuskure 31 da VAR ta yi a kakar 2023-24.
A watan Yuni ƙungiyoyin Premier 19 suka zaɓi a ci gaba da amfani da VAR bayan da Wolverhampton Wanderers ita kaɗai ta nemi a daina amfani da ita.
Wani bincike mai zaman kansa da Hukumar Premier Lig ta sa aka yi, ta nuna huɗu cikin biyar na magoya bayan kwallon ƙafa na son a ci gaba da amfani da ita.
Premier Lig ta fara yin bayani kan VAR a kafar sada zumunta da aka samar domin hakan, amma an jinkirta fara amfani da na'urar da za ta riƙa kama satar gida da kanta da ake tsara farawa a tsakanin watan Nuwamba zuwa Oktoba har sai shekarar 2025.
Webb wanda shi ne shugaban alƙalan gasar ya bayyana cewa yanzu an samu ci gaba wajen amfani da na'urar VAR inda kuskuren da take yi ya ragu da kashi 80.
"Bana tsammanin mun kai inda mutane ke zato wajen amfani da VAR," tsohon alƙalin wasan ya shaida wa Podcast ɗin shirin Stick to Football.
"Webb ya ce an ƙarfafa aiki wajen kawar da kurakuran da ake yi a baya da na'urar.
"A wajena mafi muhimmancin abu shi ne yadda aka cimma abubuwa cikin sauri. Jinkirin da ake samu a bara a duk hukuncin da VAR take yi yana kaiwa sakan 70 amma a bana sakan 25 ne. Wannan ba ƙaramar nasara ba ce."
Duk da cewa an samu raguwa a kurakuran, amma Webb ya amsa cewa VAR ta gaza yin abin da ya dace lokacin da aka kori kyaftin ɗin Manchester United Bruno Fernandes jan kati a wasan da suka yi da Tottenham a watan jiya.
Alƙalin wasan Chris Kavanagh ya bai wa Fernandes jan kati kai tsaye a minti na 42 bayan ya kai wa James Maddison taku da bai cancanci katin ba.
A ƙarshe Manchester United ta yi rashin nasara a wasan da ci 3-0 wanda suka ɗora laifin hakan kan kuskuren da aka yi.










