Matakan da za ku bi don yi wa kanku rajistar zaɓe ta Intanet a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Litinin 18 ga watan Agusta ne hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta fara aikin rajistar masu zaɓe a faɗin ƙasar, ta hanyar intanet gabanin fara aikin a ofisoshinta da ke faɗin ƙasar a mako mai zuwa.

INEC kan bai wa ƴan Najeriya damar yin rajistar zaɓe a duk lokacin da aka tunkari kakar babban zaɓe a ƙasar.

Dama ce da hukumar ke bai wa ƴan Najeriya da suka cika shekara 18, ko waɗanda wasu dalilai suka hana yin rajistar a shekarun baya ko kuma wani tsautsayi ya sa rijistar tasu ta ɓata.

Hukumar za ta ci gaba da aikin ne har zuwa dab da zaɓukan 2027, don haka ne ma take kiran aikin rajistar zaɓen da ''Ci Gaba da Rajistar Masu Zaɓe'', wato ''Continuous Voter Registration'' a Turance (CVR).

Hanyoyi biyu na yin rajistar

Hukumar zaɓen ta samar da mataki guda biyu da mutum zai bi domin yin rajistar.

Intanet: INEC ta ce mutum zai iya fara rajistar ta intanet, sannan ya ƙarasa a cibiyoyin da hukumar zaɓen ta tanada da ke kusa da shi, domin a ba shi katin wucin gadi.

Cibiyoyin rajistar zaɓen: Sannan mutum zai iya yin rajistar a cibiyoyin yin rajistar da hukumar ta tanada domin ya fara sannan ya kammala a can.

Sharuɗan yin rajistar zaɓen

Hukumar zaɓen ta lissafa wasu sharuɗaɗa - a shafinta na intanet - da za ku cika kafin ku samu damar yin rajistar zaɓen.

INEC ta ce duk wanda ke son yin rajistar zaɓen dole ne ya kasance:

  • Ɗan Najeriya da ke zaune a cikin ƙasar.
  • Dole ne ya kai shekara 18 da haihuwa, a ranar da zai yi rajistar ko kafin ranar.
  • Wanda bai taɓa rajistar a shekarun da suka gabata ba
  • Ya kasance mazuni ko mai aiki da ɗan asalin yankin da cibiyar rajistar zaɓen take.
  • Ya kasance ba shi da wani laifi da kotu ta haramta masa yin zaɓe saboda karya wasu dokokin ƙasar.
  • Dole ne ya gabatar da kansa ga jami'an INEC don yi masa rajista, ya kasance kuma zai iya tabbatar da shaidar kasancewarsa ɗan Najeriya da shekarunsa idan aka buƙaci hakan.
  • Wanda yake da katin zaɓe kuma babu sunansa a cikin rajistar masu zaɓe, shi ma zai iya sake rajistar.
  • Shi ma wanda ya samu matsalar tantancewa a zaɓukan da suka zai iya sake rajistar.

Yadda za ku yi rajista ta intanet

Duk mutumin da ya cika sharuɗan yin rajistar zaɓe, to zai iya yin rajistar ta intanet.

Tsarin rajistar zaɓe ta intanet zai bai wa mai yin rajistar dama tura bayansa zuwa shafin hukumar zaɓen.

Hakan zai sauƙaƙa wa jami'an rajistar zaɓen a cibiyoyin da INEC, idan mutum ya je domin ɗaukar hoton yatsunsa a matakin ƙarshe na rajistar.

Abubuwan da za ku yi a lokacin rajista ta intanet

  • Hukumar zaɓen ta ce waɗanda ke son yin rajistar ta intanet za su iya shiga shafinta na yin rajistar wato: www.cvr.inecnigeria.org domin ƙirƙirar shafinsa (Account) ta hanyar amfani da kwamfuta ko wayar hannu.
  • Bayan ƙirƙirar shafin za a aika sama da saƙon imel domin tabbatarwa domin ba shi damar kammala ƙirƙirar shafin nasa.
  • Daga nan mutum zai iya shiga dandalin yin rajistar ta hanyar amfani da shafinsa na sada zumuntarsa kamar yadda yake a shafin.
  • Sai kuma mutum ya cike bayansa da suka ƙunshi suna da jinsi da sauran muhimman bayanai da aka buƙata.
  • Bayan wannan mataki sai ɗaukar hoton mutum da ke rajistar.
  • Daga nan sai mutum ya zaɓi ranar da zai je domin kammala rajistar a cibiyoyin da INEC ta ware domin yin aikin, don kammala rajistar.
  • Bayan haka, mutum zai ciro takardar tabbatar da rajistar intanet ɗin domin gabatar da ita a cibiyar da zai je domin kammala rajistar a matsayin shaida.
  • A cibiyoyin rajistar ne kuma za a ɗauki hoton yatsun mutum wanda shi en mataki na ƙarshe a rajistar.
  • Daga nan kuma sai a fitar masa da katin zaɓe na wucin-gadi, kafin fitowar katin na dindindin.

Mene ne muhimmancin katin zaɓe?

Katin zaɓe wani ginshikin makami ne a tsarin mulkin dimokraɗiyya da Najeriya ke bi, domin kuwa da shi ake amfani domin samun damar zaɓen shugabanni da wakilai a lokacin zaɓukan ƙasar.

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa ƴan ƙasar damar kaɗa ƙuri'unsu a lokacin zaɓukan ƙasar, don haka wannan dama ce a gare su na yin amfani a damar da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba su.

Haka kuma mallakar katin zaɓen, hanya ce da mutane za su bi domin zaɓar shugabannin da suke so ko sauya waɗanda ba sa so.

Baya ga zaɓe kuma katin zaɓe kan taimaka wajen tantance bayanan mutum da suka ƙunshi suna ko shekaru musamman a bankunan ƙasar.