Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kun san jam’iyyun da INEC ta soke?
Hukumar zaben Najeriya INEC ta soke rijistar jam'iyyu 74 a kasar.
Jam'iyyar tsohuwar ministar ilimin kasar, Oby Ezekwasili da tsohon dogarin tsohon shugaban kasar wato Manjo Hamza Al-Mustapha da wasu fitattun 'yan kasar na daga cikin wadana aka soke.
Shugaban hukumar INEC Mahmood Yakubu ne ya sanar da soke rajistar jam'iyyun a lokacin wani taron 'yan jarida a Abuja a ranar Alhamis.
Matakin da hukumar ta dauka ya rage yawan jam'iyyun siyasar kasar daga 92 zuwa 18 a halin yanzu. INEC ta dauki matakin ne bayan nazari a kan jam'iyyun kasar da yadda suka tabuka a zaben da ya gabata.
Jam'iyyun da suka rage
Yanzu jam'iyyun da suka rage a kasar kamar yadda INEC ta sanar su ne:
- Accord (A)
- Action Alliance (AA)
- African Action Congress (AAC)
- African Democratic Congress (ADC)
- Action Democratic Party (ADP)
- All Progressives Congress (APC)
- All Progressives Grand Alliance (APGA)
- Allied People's Movement (APM)
- Action People's Party (APP)
- Boot Party (BP)
- Labour Party (LP)
- New Nigerian People's Party (NPP)
- National Rescue Movement (NRM)
- Peoples Democratic Party (PDP)
- Peoples Redemption Party (PRP)
- Social Democratic Party (SDP)
- Young Progressive Party (YPP)
- Zenith Labour Party (ZPP)
Biyu daga cikin jam'iyyun 18 da suka rage a kasar wato APP da BP na gaban kotu inda suka yi karar hukumar. Hakan ya sa ba a bayar da tabbaci game da matsayin jam'iyyun guda biyu ba.
Me yasa aka soke jam'iyyun?
Dokar kasar ta ba wa INEC damar yi wa jam'iyyu rijista, da kuma soke rijastar jam'iyyu- damar da shugaban INEC ya ce hukumar ta yi amfani da shi wajen soke rijistar jam'iyyun.
Sashe na 225A kundin tsarin mulkin kasar ya na cewa INEC na da ikon soke rijistar duka wata jam'iyya bisa wadannan ka'idojin:
- Idan jam'iyya ta kasa cike sharuddan yin rijista.
- Idan jam'iyya ta kasa samun kashi 25% na kuri'un da aka jefa a zaben shugaban kasa ko a karamar hukuma daya a zaben gwamna.
- Kasa cin zabe a kalla mazaba daya a zaben shugaban karamar hukuma, ko kujera daya ta dan majalisar dokokin jiha ko ta kasa ko kuma kujerar kansila guda daya.
Jam'iyyun da INEC ta soke wa rijista
Cikin jam'iyyun da INEC ta soke wa rijistarsu saboda gaza cika ka'idojin, har da na wasu fitattun mutane a kasar.
Daga ciki akwai jam'iyyar PCP da ta zo ta uku a zaben 2019 da kuma jam'iyyar NCP wadda Gani Fawehinmi ya kafa.
Jam'iyyar ACPN wadda tsohuwar ministar ilimin kasar kuma shugabar kungiyar rajin dawo da daliban makarantar 'yan mata da ke Chibok, Oby Ezekwesili ta kafa kuma ta tsaya takarar shugaban kasa na daga cikin wadanda sokewar ta shafa.
Akwai kuma jam'iyyar PPN wadda Manjo Hamza Al-mustapha (mai ritaya), dogarin tsohon shugaban mulkin sojin kasar Marigayi Sani Abacha, ya yi takarar shugaban kasa.
Sauran sun hada da jam'iyyun PCP da Fresh Party ta fitaccen mai wa'azin addinin Kirista Rev. Chris Okotie, wanda kuma shi ne dan takararta.
Jerin jam'iyyun da INEC ta soke
- AAP - Advanced Allied Party
- ABP - All Blending Party
- ACD- Advanced Congress Of Democrats
- ACPN - Allied Congress Party Of Nigeria
- AD - Alliance For Democracy
- AGA - All Grassroots Alliance
- AGAP - All Grand Alliance Party
- ANDP - Advanced Nigeria Democratic Party
- ANN - Alliance For New Nigeria
- ANP - Alliance National Party
- ANRP - Abundant Nigeria Renewal Party
- APA - African People Alliance
- APDA - Advanced People's Democratic Alliance
- APN - Alternative Party Of Nigeria
- ASD - Alliance Of Social Democrats
- AUN - Alliance For A United Nigeria
- BNPP - Better Nigeria Progressive Party
- CAP - Change Advocacy Party
- CC - Coalition For Change
- CNP - Change Nigeria Party
- COP - Congress Of Patriots
- DA - Democratic Alternative
- DPC - Democratic People's Congress
- DPP - Democratic People's Party
- FDP - Fresh Democratic Party
- FJP - Freedom And Justice Party
- GDPN - Grassroots Development Party Of Nigeria
- GPN - Green Party Of Nigeria
- HDP - Hope Democratic Party
- ID - Independent Democrats
- JMPP - Justice Must Prevail Party
- KP - Kowa Party
- LM - Liberation Movement
- LPN - Legacy Party Of Nigeria
- MAJA - Mass Action Joint Alliance
- MDP - Modern Democratic Party
- MMN - Masses Movement Of Nigeria
- MPN - Mega Party Of Nigeria
- MRDD - Movement For The Restoration And Defence Of Democracy
- NAC - National Action Council
- NCMP - Nigeria Community Movement Party
- NCP - National Conscience Party
- NDCP - Nigeria Democratic Congress Party
- NDLP - National Democratic Liberty Party
- NEPP - Nigeria Elements Progressive Party
- NFD - Nigeria For Democracy
- NGP - New Generation Party Of Nigeria
- NIP - National Interest Party
- NPC - Nigeria People's Congress
- NPM - New Progressive Movement
- NUP - National Unity Party
- PCP - People's Coalition Party
- PDC - People For Democratic Change
- PDM - People's Democratic MovementPPA - Progressive People's Alliance
- PPC - Providence People's Congress
- PPN - People's Party Of Nigeria
- PPP - People's Progressive Party
- PT - People's Trust
- RAP - Reform And Advancement Party
- RBNP - Re-Build Nigeria Party
- RP - Restoration Party Of Nigeria
- SNC - Save Nigeria Congress
- SNP - Sustainable National Party
- SPN - Socialist Party Of Nigeria
- UDP - United Democratic Party
- UP - United Patriots
- UPC - United People's Congress
- UPN - Unity Party Of Nigeria
- UPP - United Progressive Party
- WTPN - We The People Nigeria
- YDP - Young Democratic Party
- YES - Electorates Solidarity
- YP - Youth Party
Zabukan da ke tafe
INEC ta sanar da 14 ga watan Maris a matsayin ranar da za ta gudanar da zaben cike gurbi na dan majalisar tarayya a Magama/Pategi a jihar Neja.
A ranar ne kuma za ta gudanar da zaben dan majisar dokokin jihar Kwara mai wakiltar mazabar Pategi da takwaransa mai wakiltar mazabar Kebbe a majalisar dokokin jihar Sokoto.
Farfesa Mahmood Yakubu ya kuma sanar da cewa hukumar za ta gudanar da zaben gwamnan jihar Edo a ranar 29 ga watan Satumban 2020.