TikTok ya koma ƙarƙashin jagorancin Amurka

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images
'Yan kasar China da suka mallaki shafin sada zumunta mai tarin mabiya a duniya Tik Tok sun sanya hannu a wata yarjejeniyar sayar da kadarorin kamfanin ga wata hadaka da 'yan kasuwar Amurka ke jagoranta.
Matakin zai hana gwamnatin Amurka haramta ayyukan shafin saboda kasancewarsa na 'yan China, abin da ya janyo batun nuna damuwa kan tsaro a Amurka.
An dai shafe kusan shekara daya ana kokarin kulla yarjejeniya kan shafin na Tiktok mai farin jini sosai.
Kuma yanzu masu bibiyar shafin, su miliyan 170 a Amurka za su ci gaba da amfani da wani nau'i na shafin.
A cikin wata sanarwa ta cikin gida da aka samu daga babban jami'in shafin na Tik Tok, Shou Chew wanda BBC ta gani, shafin na Tiktok da kamfanin da ya mallake shi Bytedance sun amince su kulla yarjeniya da kamfannonin Oracle da Silver lake na Amurka da kuma MGX wanda ofishinsa ke Abu Dhabi
Kamfanin Bytedance zai rike kashi 19.9 cikin 100 na shafin a karkashin yarjejeiyar da suka kula da Amurka yayin da Oracle da Silver lake da MGx kowannensu zai mallaki kashi 15 cikin 100.
Sannan akwai kashi 30.1 da aka ware wa wadanda suka zuba jari a kamfanin na Byedance.
A yanzu babbar tambayar ita ce shin menene zai faru ga tsarin da TikTok ke amfani da shi wajen mu'amulla da masu amfani da shafin.
A baya Fadar White House ta ce kamfanin Orcale wanda Larry Ellison wani mai goyon bayan Donald Trump ya kafa, shi ne zai bayar da laisisin tsarin karkashin wani bangare na yarjejeniyar da aka cimma.
Majlisar dokokin Amurka ta haramta amfani da shafin TikTok a watan Afirilun 2024 saboda dalilan tsaro.
A ranar 20 ga watan Janairun 2025 ne ya kamata a ce dokar ta fara aiki sai dai an rika jinkirtawa saboda gwamnatin Trump ta rika kokarin kulla yarjejeniya.











