Yadda TikTok ya sauya kasuwancin waƙoƙi a ƙasar Hausa

TikTok na da masu amfani da shi sama da biliyan daya da rabi

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Buhari Muhammad Fagge
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa, Abuja

TikTok na daya daga cikin manyan manhajoji kafafen sada zumunta da suke haskakawa a duniya yanzu.

Manhajar na da masu amfani da ita sama ba biliyan 1.5 a fadin duniya sakamakon haka tasirinsa ya zama gagarumi kan yadda ake yin kida da waka da kuma yadda ake kasuwancinsu.

Tun farkon shigowar manhajar TikTok babu abin da ake yi a cikinta sai waka rawa da sanya muryoyin mutane ko dai fitattu ko kuma wadanda ake zolaya.

TikTik ya sauya yadda mawaka suke sakin wasa da yadda suke tallata su, mafi mahimmanci shi ne yadda manhajar ke fito da sabbin mawaka da ba a sansu ba a baya cikin kankanin lokaci.

Mutane na amfani da murya ko waka ko kida a matsayin sautin da za a rika ji su kuma suna taka rayawa, ko kuma yin wani abu na nishadantarwa.

Mawaka da dama kan hawa wakokin da kansu, wani lokacin su bai wa masu shafukan da ke da mabiya da yawa, a wani loton 'yan fim ke hawa wakokin domin taimaka wa wajen yada su cikin hanzari, ko kuma a kirkiri hashtag na Challenge domin kowa da kowa.

Yawan yadda ake amfani da sautin yawan yadda zai karade manhajar cikin gaggawa, da yawan adadin wadanda suka yi amfani da shi.

Mawakan na nuna soyayya ga wadanda suka yi bidiyo da sautin wakokinsu

A yanzu da aka daina cinikin wakoki a faifan CD ko yaya mawakan suke kasuwancin wakokin nasu?

BBC ta tattauna da wasu mawaka domin jin yadda suke samun kudi, ganin cewa hanyar da suke kamun kudi da ita a baya ta zama tsohon yayi.

Sadeek Sale shi ne mawakin da ya raira wakar "Abin ya motsa" wadda ta shafe watanni tana tashe a TikTok, kuma dubban matasan da ke TikTik ne suka hau kan wakar. Sadeek ya ce "kamar ni idan na yi sabuwar waka sai na fara kaita TikTok kafinn na sake ta da mako biyu ko uku, a can za ta fara tirendin saboda yawan yadda ake amfani da ita. "Da zarar an jita da yawa za a rika biyo wakar a YouTube domin kallonta wanda cikin kankanin lokaci wakar za ta samu wadanda suka kalle ta da dama.

Wakar Sadeek na cikin wakokin da aka kalla da yawa a shafin YouTube, kuma matashin mawakin yace sanadin wannan wakar ne mutane suka san shi da dama.

An kalli wakar Abin ya motsa a shafin matashin na YouTube sama da miliyan daya

"Wani lokacin masoya ne ke sa wakokinmu a TikTok"

Mata mawaka sun fi samun mabiya a TikTok musamman idan suna kula mabiyansu

A wasu lokutan ba wadanda suka raira wakokin ba ne ke sanya su, sai dai daga baya su hau su ma domin nuna cewa su ne asalin masu wakar in ji Maryam Aliyu Muhammad.

Wakarta da ta fi karbuwa ita ce "Murmushi ko kuma Kowa ya kauce" kamar yadda aka fi saninta da ita.

Maryam Bakasee ta ce ba ita ce ta dora wakar ba a TikTok daga baya taga wakar tana tashe sai itama ta bi yayi.

"A nan ne aka fahimci ni na raira wakar, na kara samun mabiya da masu nunan kauna ta hanyar laikin.

"Dalilin wakar na je bikin da aka yi min likin kudi masu yawa, wadanda ko da kundin wakoki na fitar bai zama dole na samu kudi masu yawa ba kamar haka".

Yawancin bukukuwan da mawakan ke zuwa su yi waka a cewarta za ka ga mahalarta na cewa a TikTok na fara ganinki na ji ina sha'awar mu gayyace ki.

Don haka "TikTok nan ne manhjar da na fi sha'awar kai hajata domin a saya".

"Ba haka kurum ake biyan mawaka kudi ba"

Wakokin matashiya Khairat sun dade suna tashe a TikTok

Ma fi yawan wadannan mawaka ba su samun kudi ta manhajar TikTok kai tsaye, amma dalilin manhajar su kan samu kudi a wasu wuraren, kamar Youtube da Boomplayer da Audiomac da Applemusic da kuma Shazam da dai sauransu.

Khairat Abdullahi ta ce "kowaye kai sai kana da asusu da wadanda suke biyan tukunna za su biya ka.

"Ko ka sanya wakarka a shafinsu idan ba a jinta ko ba ta tashe ba za ka samu kudi ba kamar yadda kake zato, da sanya su da ake yi a Youtube yana kara musu tashe da karade ko ina." in ji ta.

Akwai manhajoji da suke biyan mawaka kudi idan suka dora a shafukansu kuma ake kalla

Asalin hoton, Getty Images

Mawaka na fahimtar abin da mabiyansu ke so a TikTok, ta hanyar tattaunawa da su kai tsaye (Live) a manhajar.

Manyan mawaka irinsu Ado Gwamja, Hamisu Breaker, Aminu Ala Abdul D one da dai sauransu dukkansu babu wanda wakarsa ba ta zama ruwan dare ba a wannan manhaja ta Tiktok.

To sai dai wasu masoyansu na da ra’ayin cewa babu tarbiyya a tiktok musamman sakamakon yadda wasu matasa suka mayar da dandalin tamkar wurin cin mutumci da zage-zage.