Yadda kuɗin kujerar aikin hajji ya sauya a Najeriya cikin shekara biyar

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da aka fara shirye-shiryen aikin hajjin shekara ta 2025, tuni hukumar alhazai ta Najeriya ta sanar da kuɗin hajji a fadin ƙasar.
Daga shekarar 2019, farashin kujerar aikin hajji a Najeriya ya nunka fiye da sau biyar.
A wannan shekara ta 2025, maniyyata aikin hajji daga Najeriya za su biya kuɗin da ya kama daga naira 8,327,125 zuwa naira 8,784,085.
Kudin ya bambanta ne sanadiyyar bambancin wurin da mahajjat za su tashi daga ƙasar.
Yayin da mutanen jihohin Borno da Adamawa da ke arewa maso gabas za su biya kuɗi mafi ƙaranci, mahajjata daga kudancin ƙasar su ne za su biya kudi mafi tsada saboda bambancin nisar su daga ƙasar Saudiyya.
Farashin na bana ya ɗara na shekarar da ta gabata (2024), sai dai hukumar kula da mahajjata ta Najeriyar ta nuna farin ciki kan cewa farashin bai yi tsananin da aka yi tsammani ba.
BBC ta duba farashin hajji a Najeriya cikin shekaru biyar da suka gabata:
2024
Farashin Hajji a Najeriya a shekarar 2024 ya yi matuƙar haifar da ruɗani sanadiyyar bambancin da aka samu daga ƙarshe.
Da farko Hukumar ta buƙaci maniyyat su biya naira miliyan 4.5 a matsayin na kafin alƙalami, sai dai daga baya hukumar ta buƙaci alhazai da su yi ciko, wani abu da ya janyo suka daga ɓangarori da dama.
A ƙarshe hukumar aikin hajjin ta Najeriya ta buƙaci maniyyatan su biya abin da ya kama daga naira 4,679,000 zuwa 4,899,000 dangane da jiha da kuma yankin da mahajjaci yake.
Hukumar ta bayyana cewa hakan ya faru ne sanadiyyar sauyawar darajar naira idan aka kwatanta da dalar Amurka.
A cikin sanarwar da ta fitar, hukumar ta buƙaci maniyyata su cika kudin hajjin ya zuwa ranar 12 ga watan Fabarairun 2024.
2023
A 2023 maniyyata daga Najeriya sun biya kudin da ya kama daga naira 2,800,000 zuwa 2,999,000. Yayin da maniyyata daga Yola da Maiduguri suka biya naira 2,800,000, takwarorinsu daga sauran jihohin arewacin ƙasar sun biya naira 2,919,000.
Sai dai a lokacin da ya sanar da kuɗin, shugaban hukumar aikin hajji ta Najeriya na wancan lokaci, Zikirullah Kunle Hassan ya ce farashin kujerar hajjin ya kasu zuwa shida a jihohin kudancin ƙasar.
Mahajjata daga Edo sun biya naira 2,968,000 yayin da na Ekiti da Ondo suka biya 2,180,000, sai dai mahajjata daga jihohin Legas da Ogun da Oyo sun biya naira 2,999,000.
2022
A 2022 shekarar da aikin hajji ya dawo bayan cutar korona, hukumar alhazai ta Najeriya ta sanar da cewa maniyyata za su biya kuɗin hajji da ya kama daga naira 2,408,197 zuwa 2,496,815.
Lokacin da ya sanar da kuɗin aikin hajjin, shugaban hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan ya samu yabo daga mutane da dama, ganin cewa an yi tunanin farashin zai iya haura naira miliyan biyar.
Cutar korona, wadda ta addabi duniya ta kashe sama da mutum miliyan 6.3, a hukumance, duk da cewa ana ganin adadin a zahiri ya haura haka, sannan sama da mutum miliyan 550 ne suka kamu.
Wannan ya sanya Musulmai daga ƙasashen duniya sun gaza halartar aikin hajji a shekarun 2020 da 2021.
2019
A 2019, shekarar da cutar korona ta fara bayyana a duniya, Hukumar aikin hajji ta Najeriya ta buƙaci maniyyata su biya kimanin naira miliyan 1.5 a matsayin kuɗin aikin hajji.
Sai dai daga baya an samu ragowa a kudin kujerar, inda hukumar ta sanar da cewa an samu ragowar naira 51,170 a kan kowace kujera.
Hukumar ta sanar da cewa an samu ragowar ne bayan sake duba batun zirga-zirgan mahajjata a ƙasar ta Saudiyya.










