Me ya sa ake yi wa shugaban NNPC barazanar halaka shi?

Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya, Malam Mele Kyari ya ce ya fuskanci barazana mai yawa ta neman halaka shi daga wasu mutanen da ba sa jin daɗin ƙoƙarin da gwamnati ke yi na kamanta gaskiya a hada-hadar mai da hana satar ɗanyen mai da ke haddasa asarar kudin-shiga ga gwamnati.

Malam Kyari ya faɗi hakan ne a wajen wani taro da majalisar wakilan ƙasar ta shirya, inda ya ƙara da cewa gaskiya rigar-ƙaya ce kamar yadda ƴan magana kan ce.

Kuma wannan ne ya sa suke fuskantar kalubale tun lokacin da suka duƙufa wajen aiwatar da wasu sauye-sauye a kamfanin man ƙasar da nufin kamanta gaskiya a hada-hadar kamfanin, wato NNPCL da ƙoƙarin hana satar danyen mai.

Ya ce shi da kansa ma bai tsira ba, kasancewar wasu na yunƙurin kawar da shi daga doron ƙasa.

“Na fuskanci barazana ta halaka ni a lokuta masu yawa. Amma wannan bai dame mu ba, saboda ba wanda zai mutu sai kwanansa ya ƙare. Saboda haka wannan ba abin damuwa ba ne.

“Sai dai shi ne abin da ke biyo bayan duk wani yunƙuri na kawo sauyi. Mutane kan mayar da martani a duk lokacin da aka yi ƙoƙarin raba su da wani abin da suka saba da yi, wanda suke cin gajiyarsa.

“Amma kuma irin wannan martanin yana da amfani gare mu idan muka hada kai muka yi aiki tare,” ya ce.

Sai dai a cewar shugaban kamfanin man, sakamakon jajircewarsu, kwalliya na biyan kudin sabulu, saboda adadin man da Najeriyar ke haƙa ya ƙaru daga watan Yulin da ya wuce.

Ko da a watan Oktoban wannan shekarar adadin gangar man ya kai fiye da miliyan ɗaya, saɓanin raguwar da ya yi a baya da bai wuce 700,000 da ɗoriya ba.

Karin wasu labaran da za ku so ku karanta

Me masu sharhi ke cewa?

Wannan furuci na shugaban kamfanin man fetur ɗin, wato maganar barazanar da yake fuskanta ta ja hankalin wasu masu fafutukar yaƙi da rashawa a Najeriya.

Malam Awwal Musa Rafsanjani wanda shi ne wakilin ƙungiyar yaƙi da rashawa ta duniya, wato Transparency International a Najeriya, kuma shugaban kungiyar CISLAC, ya ce yaƙi da cin hanci da rashawa ya gaji haka.

“Ba mu yi mamakin barazanar da shugaban NNPC ke fuskanta ba don dama akwai mutane da dama da ba sa ƙaunar a kawo gyaran da zai rage cin hanci da rashawa.

“Kuma duk yadda za su yi su ga cewa sun yi maganin duk mai ƙoƙarin kawo wani tsari da zai yi karo da yadda suke tafiyar da al’amuransu za su yi maganinsa. Don haka ba mu yi mamaki ba.

“Illa iyaka idan dai ana yin aikin gaskiya daidai da dokar ƙasa don amfanin jama’a, to mutane za su tsaya tsayin daka don yin maganin duk mai kawo cikas ga tsari na gaskiya, kuma ƴan Najeriya za su mara wa wannan mutum baya,” in ji Rafsanjani.

Duk da cewa shugaban kamfanin man Najeriyar, Mele Kyari bai ambaci sunaye ba, bai kuma siffanta wadanda ke barazanar raba shi da ran nasa ba, Malam Awwal Rafsanjani ya ce ɓarayin kusa ne da na nesa. Wasu ma ana rufe ƙofa da su.

“Na yi imanin cewa wasu daga cikin masu yin wannan barazana, manyan mutane ne da ke amfana da rashin gaskiya da adalci a Najeriya. Wasunsu ƴan Najeriya ne suna cikin gwamnati wasu kuma ƴan ƙasashen waje ne," ya ce.

Ya ƙara da cewa “Ita kanta NNPC da tana bin shawarwarin da muke ba su da an samu cikaken ci gaba mai ɗorewa a wannan kamfani don a daina amfani da shi a wata hanyar sace kuɗin ƙasa ko kuma hada baki da wasu manyan kamfanonin kasashen waje da ke tsoma mu a halin da muke ciki.

Kamfanin man Najeriyar ya fara aiwatar da wasu sauye-sauye a tsakanin nan, wadanda suka kawar da tsohon tsarin da ya dade yana tafiya a kansu.

Kuma sakamakon sauyin kamfanin ya yi nasarar bankaɗo wasu haramtattun matatun man ɓoye da ɓarayi ke amfani da su, wadanda suka yi sanadin raguwar man da ƙasar ke samarwa.