Napoli ta ƙwallafa rai kan Garnacho, Anceloti na tattara kayansa don barin Madrid

Alejandro Garnacho

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Alejandro Garnacho
Lokacin karatu: Minti 1

Napoli na fatan za ta cimma yarjejeniyar fam miliyan 50 domin ɗauko ɗan wasan gefe na Manchester United da kuma Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 20. (Corriere dello Sport)

Aston Villa ta yi watsi da tayin da West Ham ta yi mata na fam miliyan 57 kan ɗan wasan gaba Jhon Duram, kasancewar Villa ba ta da niyyar sayar da ɗan wasan gaban na Columbia mai shekara 21 wanda darajarsa ta kai fam miliyan 80. (Telegraph)

Manchester United na tattaunawa domin ɗaukar ɗan wasan baya Patrick Dorgu daga Lecce, inda ake sa ran ɗan wasan mai shekara 20 zai iya cike giɓin da ake da shi a ƙungiyar da Ruben Amorim ke jagoranta. (Athletic)

Mai horas da ƙungiyar Real Madrid, Carlo Ancelotti na tattara kayansa domin barin ƙungiyar a ƙarshen kakar bana, kuma ana ganin cewa kociyan Bayer Leverkusen, Xabi Alonso ne wanda ya fi cancanta ya maye gurbin Ancelotti, ɗan asalin ƙasar Italiya. (Ondacero)

Inter Milan da Borussia Dortmund na ƙyalla ido kan ɗan wasan tsakiya na Ingila, Jack Grealish mai shekara 29, ganin cewa babu tabbas game da ci gaba da zaman shi a Manchester City. (Sun)

AC Milan na tunanin ɗaukar aron ɗan wasan gaba na Manchester United, Rasmus Hojland mai shekara 21 a duniya da kuma Joshua Zirkzee mai shekara 23. (ESPN)

Juventus ta tattauna da Udinese kan sayen ɗan wasa Thomas Krintensen mai shekara 23, wanda Tottenham da Leicester City ke ƙyalla ido a kansa. (Mail)