Bikin al'ada a Senegal da jaririn farin zaki cikin hotunan Afrika na mako

f

Asalin hoton, SAMUEL ALABI/AFP

Bayanan hoto, Ɗaliban wasan kwaikwayo da nishaɗantarwa na jami’r Ibadan a Najeriya na wasan biki a ranar Juma’a
f

Asalin hoton, SAMUEL ALABI/AFP

Bayanan hoto, An shirya wasan ne domin samar da dankon zumunci tsakanin abokan karatun.....
f

Asalin hoton, JALAL MORCHIDI/EP

Bayanan hoto, A dai wannan rana Fitacciyar ‘yar fim ɗin nan ta Morocco Fatima Ezzahra el Jouhari ta yi sumba ga taron fim da aka yi na duniya a Marrakech......
f

Asalin hoton, DIMITAR DILKOFF/AFP

Bayanan hoto, Hilarion Kassa Moussavou daga Gabon (na biyu daga hagu) wanda ya fito a shirin nan na Guardians of the Forest, ya je taron hukumar raya al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya da aka yi a ranar Litinin tare da wasu taurari daga Mongolia da Brazil da Canada da kuma Papua New Guinea.
f

Asalin hoton, JUAN CARLOS HERNANDEZ/AFP

Bayanan hoto, Wata dabba sabuwar haihuwa jinsin zaki a Afrika ta Kudu da aka ɗauki hotonta a gidan namun dajin Las Delicias da ke Venezuela a ranar Laraba.
f

Asalin hoton, JAMES WAKIBIA/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, A Kenya, Elizabeth Ngusilo ce ke yi wa manema labarai bayani a wajen babbar kotun Nakuru, kan ƙorafin mutanen Ogiek na yunkurin gwamnati na korarsu daga dajin Mau.
f

Asalin hoton, CEM OZDEL/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Mutane sun taru a taron al’ada da aka yi a Dakar babban Senegal a ranar Lahadi...
f

Asalin hoton, CEM OZDEL/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Cikin waɗanda suka halarci taron har da masu tseren kwale-kwale...
f

Asalin hoton, CEM OZDEL/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Nan kuma mutanen Lebu ne ke rawa....
f

Asalin hoton, CEM OZDEL/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Duka waɗannan sun faru ne a wani yammaci da wata ya cika..
f

Asalin hoton, MAXIM SHIPENKOV/EPA

Bayanan hoto, Wata mai kayan ƙawa ‘yar Habasha Kunijina Tesfaye sanye da kayan nunawa a taron nuna kayan ƙawa da aka yi a Rasha a ranar Alhamis....
f

Asalin hoton, ALEX CAPARROS/FIFA/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Ibrahim Diarra (a tsakiya) yana jinjinawa abokan wasansa lokacin da ya ci kwallonsa ta farko a wasan da Mali ta buga da Fransa a kofin duniya na ‘yan ƙasa da shekara 17 a wasan daf da na ƙarshe a ranar Talata.
f

Asalin hoton, IBRAHIM BARRIE/EPA

Bayanan hoto, Wani soja ɗauke da gurneti a Freetown babban birnin Saliyo a ranar Litinin, bayan gwamnati ta ce ta daƙile wani yunƙurin juyin mulki a ƙarshen mako.