Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masu zanga-zangar adawa da mulkin Hamas na ƙaruwa a Gaza
- Marubuci, Paul Adams
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Jerusalem
- Lokacin karatu: Minti 5
''Ku fice! ku fice! ku fice!
Muryar da ke bidiyon da aka yaɗa a shafin Telegram na da ƙarfi, kuma haɗe da kiɗa. Saƙon da ke ciki kuma a fili yake ƙarara.
''Duka ƴan ƙungiyar Hamas, ku fice!''
A kan titunan Gaza, ana samun karuwar Falasɗinawa da ke bayyana ƙin jinin ƙungiyar Hamas mai ɗauke da makamai da ta mulki Zirin na kusan shekara 20.
Mutane da dama na ɗora wa Hamas alhakin jefa yankin cikin rikici mafi muni da Falasɗinawa suka taɓa shiga a cikin fiye da shekara 70.
''Ku isar da saƙon'' wasu gungun mutane suna ihu suna faɗi, a yayin da suke kutsawa kan tinunan Gaza: ''Hamas ba ta da amfani.''
''Duniya bata san halin da zirin Gaza ke ciki ba,'' inji Moumen al-Natour, wani lauya a Gaza kuma tsohon fursunan siyasa wanda ya daɗe yana sukar Hamas.
Al-Natour na magana da mu ne daga ɓurɓushin ragowar birninsu da aka lalata.
''Duniya na tunanin Gaza da Hamas duk ɗaya ne,'' Inji shi. '' Mu ba mu zaɓi Hamas ba, a yanzu kuma Hamas ta dukufa ne wajen mulkar Gaza da kuma haɗa makomarmu da tata. Wajibi ne Hamas ta janye.''
Fitowa domin yin magana na da haɗari. Hamas ba ta jurewa adawa. Moumen bai tsorata ba, a yayin da yake rubutawa jaridar Washington Post wata maƙala cikin fushi a ƙarshen watan Maris.
''Goyawa Hamas baya na nufin halakar da Falasɗinawa,'' kamar yadda ya rubuta, '' hakan ba ya nufin samun ƴanci ga Falasɗinawa''.
Shin babu haɗari yin magana irin wannan? na tambayesa.
'' Ya kamata mu rika samun ƙarfin gwiwa muna yin magana,'' ya bani amsa ba ƙaƙƙautawa.
'' Shekarata 30. A lokacin da Hamas ta kwace iko, shekarata 11. Mene nayi da rayuwata zuwa yanzu? Na yi asarar rayuwata ne kawai a tsakanin yaƙi da karuwar rikice-rikice a banza.''
Tun lokacin da ƙungiyar Hamas ta karɓe iko da Gaza a 2007 ta hanyar kifar da abokan hamayya na siyasa da ƙarfin tuwo, shekara ɗaya bayan sun lashe zaɓe, an gwabza yaƙe-yaƙe manya sau uku da Isra'ila, da kuma wasu rikice-rikice guda biyu.
''Kasancewar mu ƴan Adam ne wajibi ne mu fito mu yi magana,'' a cewar al-Natour, '' duk da murƙushe mu da Hamas ke yi''.
Duk da Hamas na fama da yaƙinta da Isra'ila, hakan bai sa ta daina hukunta masu sukar ta ba.
A ƙarshen watan Maris, wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da Oday al-Rubai, ɗan shekara 22 daga wani sansanin ƴan gudun hijira a birnin Gaza.
Sa'oi bayan nan, an gano gawarsa ɗauke da munanan raunuka.
Hukumar kula da haƙƙin bil Adama ta Falasɗinawa mai zaman kanta ta ce an azabtar da Oday, inda suka bayyana mutuwarsa a matsayin 'mummunar take haƙƙin yin rayuwa na ɗan Adam da kuma kisan zalunci''.
Al-Rubai na daga cikin waɗanda suka gudanar da zanga-zangar ƙin jinin Hamas na baya bayan nan. Iyalinsa na zargin Hamas da kisan sa kuma suna buƙatar ayi musu adalci.
Kwanaki kafin a kashe shi, Al-Rubai cikin tsoro ya wallafa wani bidiyo wanda ba a iya ganin abin da ke cikinsa sosai a shafinsa na sada zumunta, wanda a ciki ya bayyana tsoronsa na cewa mayakan Hamas na farautarsa.
''Gaza ta zama birnin fatalwa,'' in ji shi, yayin da ya juya yana kallon bayansa.
''Ina nan kan titi na rasa inda zan je. Ban ma san meyasa suke farauta ta ba. Sun lalata mana rayuwa.''
A wurin Jana'izarsa, taron mutanen da ba su da yawa sun buƙaci ɗaukar fansa, sun kuma nanata buƙatarsu ta Hamas ta fice daga Gaza.
A bara, Amin Abed ya kusa samun makoma irin ta Al-Rubai, sakamakon hukuncin da ya yanke na sukar Hamas.
Wasu mutane da suka rufe fuskokinsu sun lakaɗa masa duka, suka karya ƙasusuwa da dama a jikinsa, suka kuma ji masa rauni a ƙodarsa. Abed ya rayu, amma sai da ya fita ƙasar waje domin neman kulawa.
A yanzu haka yana zama a Dubai, amma yana ci gaba da shiga zanga-zanga.
''Ƙarfin Hamas ya soma ƙarewa,'' in ji shi.
''Suna kai hari kan ƴan gwagwarmaya da fararen hula, su duke su, su kashe su domin su tsoratar da mutane. Amma yanzu ba kamar baya bane.''
Kafin yarjejeniyar tsagaita wutar ta ruguje a watan da ya gabata, mayaƙan Hamas sun ɗauki aniyar nuna iko da ƙarfinsu.
Amma a yanzu da Isra'ila ta ci gaba da kai hari ba ƙaƙƙautawa, mayaƙan Hamas ɗin sun ja da baya zuwa gine-ginen ƙarƙashin ƙasa, yayin da aka sake jefa ƴan Gaza cikin yaƙi.
Zanga-zangar baya bayan nan na nuna cewa fararen hula, waɗanda aka kai bango bayan shafe shekara ɗaya da rabi Isra'ila na yi musu ruwan bama-bamai, su soma rage tsoron Hamas da suke yi.
Beit Lahiya da ke arewacin Zirin Gaza su ne suka fi nuna adawarsu.
A wasu saƙonnin murya, wani shaida na gani da ido - wanda ya buƙaci a sakaya sunansa- ya bayyana wasu lokuta da dama da mazauna yankin suka hana mayaƙan Hamas yin ayyukan soji daga cikin yankinsu.
A ranar 13 ga watan Afrilu, ya ce mayaƙan Hamas sun yi ƙoƙarin shiga gidan wani tsohon mutumi mai suna Jamal al-Maznan da ƙarfi.
'' Sun so su harba roka da wasu makamai daga cikin gidansa,'' a cewar sa.
''Amma ya ƙi amincewa.''
Daga bisani lamarin ya ɗauki zafi inda ƴan uwa da maƙwafta suka fito domin goyawa Maznan baya. Dalilin hakan mayaƙan suka buɗe wuta, suka jikkata mutane da dama, amma daga baya an kore su.
'' Harsasan mayaƙan bai tsoratar dasu ba,'' in ji sa.
Sun kusanto mayaƙan ƙungiyar suka ce musu su tattara kayansu su fice.
''Ba ma son ku a wannan wurin. Ba ma son makamanku da ke kawo mana bala'i da halaka da mutuwa,''
A wasu yankunan Gaza, masu zanga zanga sun shaidawa mayakan cewa su kauracewa zuwa kusa da asibitoci da makarantu domin gujewa lamarin da hare-haren Isra'ila ta sama zai shafi fararen hular da basu ji ba basu gani ba.
Amma har yanzu irin wannan adawar na da barazana, Hamas ta harbe ɗaya daga cikin masu zanga-zangar har lahira.
A yayin da suke ci gaba da cire rai kan zuwan ƙarshen yaƙin, wasu ƴan Gaza na nuna fushinsu ne kan Isra'ilar da Hamas.
Da aka tambaye shi ko wani ɓangare ya fi ɗaura wa alhakin mummunan yanayin da Gaza ke ciki, Amin Abed ya ce yanayi ne na gaba kura baya sayaki''.
Zanga-zangar na makonnin baya bayan nan ba tawaye bane, amma bayan kusan shekara 20 suna mulki, karfin ikon Hamas na soma raguwa.