An gano tana mai rai a ƙwaƙwalwar wata mata

...

Asalin hoton, ANU

A karo na farko, masana kimiyya sun gano tana mai tsayin inci uku da ranta a ƙwaƙwalwar wata mata 'yar Australia mai shekara 62.

'Yar siririyar tanar an zakulo ta ne daga ɓangaren gaba na ƙwaƙwalwa da ta lalace a lokacin wani aikin tiyata a Canberra a shekarar da ta gabata.

Matar ta yi fama da abin da likitoci suka kira jerin cututtuka da suka haɗa da ciwon ciki da tari da yawaita gumi cikin dare, wanda daga baya ta shiga yanayin mantuwa da damuwa.

Ana tunanin tanar ta kasance a cikin kwakwalwarta na tsawon wata biyu.

Masu bincike na gargaɗin cewa wannan lamari na nuna karuwar haɗarin wasu nau'ukan cuta ko cutuka da ake iya dauka daga dabobbi zuwa bil'adama.

''Duk mutanen da ke wannan ɗakin tiyatar sun kaɗu matuƙa lokacin da likitar da ke jagorantar yi mata aiki ya zakulo tanar mai tsayin centimita takwas daga kwakalwarta,'' a cewar Sanjaya Senanayake, wani likitan cutuka masu yaɗuwa a asibitn Canberra.

''Ko da ka ɗauke abin da ake tunanin ya haifar da hakan, wannan sabuwar cuta ce da ba a taɓa samu ba, ko gani a tattare da ɗan adam.''

Masana kimiya sun ce babu mamaki tanar ta shiga jikin matar ce a lokacin da take tsintar ganye a kusa da bakin kogin da ke gaban gidanta.

A wani labari da aka wallafa a wata mujallar sabbin cututtuka masu yaɗuwa, Mehrab Hossain, kwararriya a fanin ilimin cututtuka masu zama a jikin mutum a Australia, ta ce tana zargin matar ta gamu da wannan cuta ce bayan ta yi amfani da ganyayyakin da tana ko kwaya-kwayai tanar ke makale wajen girka abinci.

Tanar da aka ciro

Asalin hoton, ANU

A karshen watan Janairun 2021 aka kwantar da mara lafiyar a asibiti. Wani bincike da hoton kanta da aka dauka ya nuna cewa akwai wani abu makale a ɓangaren kwakwalwarta ta gaba. Kuma ba a iya gano mene ne ba har sai da aka shiga ɗakin tiyata a watan Yunin 2022.

Tana farfaɗowa daga tiyatar duk da kafa tarihin da ta yi.

''Ba a taɓa samun labarin wannan nau'in tanar a jikin mutum ba", a cewar Dakta Hossein. "Sannan ya ce ko a bincikensu na baya da gwaje-gwaje ba a taɓa ganin yadda dabobbi irin su raguna ko karnuka da mage suka haddasa wa mutum irin wannan cutar ba".

Dakta Senanayake - wanda kuma farfesa ne a fanin lafiya a jami'ar AUN ta Australia - ya shaida wa BBC cewa wannan abin gargaɗi ne.

...

Asalin hoton, ANU

Tawagar kwararru daga jami'ar ta AUN ta rawaito cewa sun gano nau'ukan cutuka 30 a cikin shekaru 30. Kashi ɗaya cikin uku na cututtuka sun kasance waɗanda ake ɗauka daga jikin dabobbi zuwa bil adama.

''Ya ce akwai damuwa da kuma bukatar ankararwa, muna sake samun wayewa da kusantar abubuwa daban-daban. Wannan batu ne da muke gani akai-akai, kamar cutar Nipah da ke yawo daga jikin tsuntsaye zuwa aladu sannan mutane su kwasa, da irin su cutar korona da Sars da Mers da duk aka kwasa daga tsuntsaye zuwa jikin dabobbi sannan mutane suka kwasa suma.''

''Duk da cewa a yanzu korona na ja da baya, akwai bukatar masana kan cututtuka masu yaɗuwa...da gwamnatoci su tabbatar da daukan matakan sa ido kan irin waɗannan cututtuka da kuma kula da muhalli.''

Aun

Asalin hoton, AUN