Brazil ta sanar da wadanda za su yi mata wasan Ingila da na Sifaniya

Asalin hoton, Getty Images
Kociyan Brazil, Dorival Júnior ya bayyana 'yan wasan da za su buga wa kasar wasan sada zumunta da Ingila da kuma Sifaniya a cikin watan Maris.
Tawagar daga Kudancin Amurka za ta je Wembley don fafatawa da Ingila ranar 23 ga watan maris, kwana uku tsakani ta je Sifaniya yin wasa na biyu a Madrid.
Sabon dan kwallon da Real Madrid ta dauka, Endrick yana daga cikin wanda aka gayyata, wanda zai koma taka leda a Santiago Bernabeu a karshen kakar bana.
Dan wasan Manchester United, Casemiro zai ci gaba da rike mukamin kyaftin, an kuma kira dan kwallon Paris St Germain, Beraldo.
An kuma gayyaci mai taka leda a Tottenham, Richarlison duk da raunin da ya ji a makon jiya.
Kenan sabon kociyan Brazil ya gayyaci sabbin 'yan wasa takwas matasa cikin tawagar, ko ta koma kan ganiyarta.
Brazil na fama da kalubale tun bayan kammala gasar cin kofin duniya a 2022 a Qatar, yayin da tawagar ta kasa samun gurbin shiga Olympic da za a yi a birnin Paris a bana.
'Yan wasan da Brazil ta gayyata buga wasannin sada zumunta

Asalin hoton, Getty Images
Masu tsaron raga: Ederson (Manchester City), Bento (Athletico Paranaense), Rafael (São Paulo).
Masu tsaron baya: Danilo (Juventus), Yan Couto (Girona), Ayrton Lucas (Flamengo), Wendell (Porto), Beraldo and Marquinhos (Paris Saint-Germain), Gabriel Magalhães (Arsenal), Murilo (Palmeiras).
Masu buga tsakiya: André (Fluminense), Andreas Pereira (Fulham), Bruno Guimarães (Newcastle), Casemiro (Manchester United), Douglas Luiz (Aston Villa), João Gomes (Wolverhampton), Lucas Paquetá (West Ham), Pablo Maia (São Paulo).
Masu cin kwallaye: Endrick (Palmeiras), Gabriel Martinelli (Arsenal), Raphinha (Barcelona), Richarlison (Tottenham), Rodrygo (Real Madrid), Savinho (Girona) da kuma Vinicius Jr. (Real Madrid).
Brazil ta kara kiran Paqueta a karon farko tun bayan Agusta

Asalin hoton, Getty Images
Brazil ta gayyaci dan kwallon West Ham, Lucas Paquetá a karon farko tun bayan da aka zarge shi da karya dokar yin caca a cikin watan Agustan 2023.
Zargin da aka yi wa Paqueta ya jawo an soke shirin da Manchester City ta yi niyar sayensa.
Sai dai har yanzu hukumar kwallon kafar Ingila ba ta tuhumi dan wasan ba, wanda ya ci gaba da taka leda a West Ham United.
Gabriel Magalhães ba zai buga wa Brazil wasannin sada zumunta ba

Asalin hoton, Getty Images
To sai dai dan kwallon Arsenal, Gabriel Magalhães ba zai yi wa Brazil wasan sada zumunta da Ingila da kuma Sifaniya ba, sakamakon raunin da yake jinya.
Tuni kuma Brazil ta sanar da madadinsa da dan kwallon Juventus, Bremer.
Kociyan Brazil, Dorival Júnior, bai yi karin bayani ba kan girman raunin dan kwallon Arsenal, amma Mikel Arteta zai yi fatan dan wasan zai murmure a kan kari domin fuskantar Manchester City a Premier League ranar 31 ga watan Maris.
Wasu 'yan wasan Brazil da ke jinya sun hada da Gabriel Martinelli da Ederson da Alisson da Marquinhos da kuma Neymar.
Wasu manyan 'yan kwallon da ba za su buga musu wasannin sada zumunta ba

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan tawagar Faransa, Antoine Griezmann ba zai yi mata wasan sada zumunta da Jamus da Chile ba, sakamakon jinya da yake yi.
Raunin da ya ji ya taka masa burbin buga wa Faransa tamaula, bayan fafatawa 84 da ya yi a jere.
Tuni Faransa ta maye gurbinsa da dan kwallon Lazio, Matteo Guendouzi.
Shi dai Griezmann, mai shekara 32 mai taka leda a Atletico Madrid, shi ne na hudu a yawan ci wa Faransa tamaula mai 44 a raga a fafatawa 127.
Haka shima Lionel Messi, ba zai buga wa Argentina wasannin sada zumuntar ba.
Mai shekara 36, bai yi wa Inter Miami wasa ba a Major League Soccer a gidan DC United ranar Asabar.











