'Bala’in da na shiga saboda rashin tsaro ya sa na manta duk karatun da na iya a duniya'

    • Marubuci, Halima Umar Saleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Digital Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC News Hausa, Abuja

Matsalar rashin tsaro a ɓangarorin Najeriya ya jefa miliyoyin mutane cikin tashin hankali da ɗimuwa sakamaon raba wasu da muhallansu, wasu kuma suka rasa danginsu, yayin da wasu kuma ba su tsira da komai ba.

An shafe shekaru yankin arewa maso gabas na fama da matsalar rikicin masu tayar da ƙayar baya na Boko Haram, wanda ya yi mummunan tasiri a kan mutane da dama.

Umar Dahiru Minta, ɗan ƙaramar hukumar Bama a jihar Borno na daga cikin irin wadanda wannan matsala ta yi wa illa, in da ruɗani da tashin hankalin da ya gani suka shafi walwalarsa.

Matashin mai shekara 22 a yanzu, ya ce tsabar masifar da ya gani a rikicin a shekarun yarintarsa ta sa sai da ya manta duk wani abu da ya koya a rayuwa.

Umar Minta ya aiko da labarinsa ne ga BBC, bayan wallafa neman jin ra’ayin mutane a wani shirin tattara labarai na musamman gabanin zaɓukan 2023.

Ya ce ya fuskanci ƙalubale da yawa da cutarwa daga hare-haren ƴan Boko Haram.

“Abu mafi girma da na fuskanta shi ne a lokacin da muka bar garin Bama shekarata 13 kuma ina da izu biyar a kaina don da haddar littafin Hisnul Muslim da Ahalari da Tajwidi.

“Amma bayan hijirarmu da wata takwas zuwa tara na nemi karatun da nake da shi a kaina na rasa saboda irin ɗimuwar da na shiga sakamakon tashin hankalin da na gani.

“Ga shi dai na san na yi karatu amma komai ya ɓace a kaina sai ɗan kaɗan, hakan ya tilasta min soma karatu daga farko,” ya shaida mana.

Kaɗuwa

Irin wannan hali da Umar ya shiga yawanci masana sun bayyana shi da yanayin kaɗuwa da ruɗu da mutum kan samu kansa a ciki a lokacin da ya samu kansa cikin tashin hankali.

Sai dai ƙwararru sun ce a ƙasashe irin Najeriya ba a fiye mayar da hankali kan abin da ake kira daidaita tunani da kuma taimakon mutanen da suka samu kansu a cikin irin wannan yanayi ba.

Shi ma Umar bai samu wani gata da za a taimaka masa da saisaita tunanin ba, don kamar yadda ya ce a wancan lokacin hatta da iyayensa da sauran dangi ba sa cikin nutsuwar da za ma su fahimci halin da ya samu kansa a ciki, balle har su taimaka masa.

Ya ce unguwar da suka zauna a garin Bama na daga cikin waɗanda hare-haren Boko Haram ya shafa sosai.

“A kan idonmu an kai hare-hare munana, an kashe mutane, an tarwatsa wasu, an ƙona wurare, ta kai ta kawo ko baccin kirki ba ma iyawa saboda fargabar me zai faru.

“Ban sake tsurewa ba sai a lokacin da mayaƙan Boko Haram suka sanar da cewa za su shigo garin kuma za su kashe dukkan mazan da suka samu.

“A gaskiya duk da ƙarancin shekaruna na shiga ɗimuwa, ina ga hakan ne ma sanadin da komai da ke adane a ƙwaƙalwata ya shafe,” ya ce.

Ya ƙara da cewa “wani babban tashin hankalin ma shi ne yadda a idonmu mayaƙan ke shigowa har da yara ƙanana riƙe da manyan bindigogi a hannayensu.”

Farfaɗowa

An sace motar mahaifin Umar da baburansa uku sannan an kashe makusantansa da danginsa da dama.

Daga baya da yaƙin ya ta’azzara iyayen Umar sun yi hijira zuwa garin Biu, inda a can ma rayuwar ta yi musu tsanani.

“A lokacin da muka koma ana tsananin wahalar ruwa a garin Biu don sai mun yi tafiyar a ƙalla awa biyu kafin mu samu ruwa.”

Daga baya Umar da iyayensa sun koma Bama inda suka tarar hatta da cokali na gidansu ba a bari ba an ɗauke.

“Hatta da dabbobin da muka bari na kiwo an kashe su.”

An ɗauki lokaci kafin Umar ya samu nutsuwarsa har ya koma karatu yadda ya kamata, in da sai da ya faro komai daga tushe don karatun duk ya zube.

A yanzu Umar yana aji biyu a jami’a, sai dai ya ce wasu daga cikin munanan tashe-tahsen hankulan da ya gani a rayuwarsa ba za su taɓa gushewa ba.