Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Matsin tattalin arziki a Najeriya ya sa na jinkirta yin aure'
Matsin tattalin arziki da ke shafar miliyoyin mutane a Najeriya ya tursasa wa wasu da dama sauya tsarin rayuwarsu.
Hussaini Mukhtar, wani matashi a jihar Kano da ke arewacin kasar, na daga cikin mutanen da ke jin tasiri da raɗaɗin matsin tattalin arziki ta yadda hakan ya tilasta masa haƙura da wasu abubuwa na jin dadin rayuwa.
Hussaini yana daga cikin ɗaruruwan mutanen da suka aiko da labaransu ga BBC Hausa, bayan wallafa neman jin ra’ayin mutane a wani shiri na musamman gabanin zaɓukan Najeriya na 2023.
Tun wuraren shekarar 2019 ne matsalar matsin tattalin arziki ta ta'azzara a Najeriya, da ta haɗa da hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar, lamarin da ya yi ƙamari a 2021 saboda tasirin annobar cutar korona da na yaƙin Ukraine da Rasha da ke shafar ƙasashen duniya ciki har da Najeriya.
Baya ga waɗan nan dalilai, masu suka na kuma danganta lamarin na Najeriya da gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, wajen kasa fitar da matakan inganta tattalin arzikin kasar, duk kuwa da cewa hakan na daga cikin alkawuran da ya dauka tun a yaƙin neman zaben da ya yi nasara a karon farko, wato 2015.
Sai dai a nata bangaren, gwamnatin ta sha cewar tana iyaka kokarinta domin ganin abubuwa sun kyautatu a fadin kasar.
Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya kai kashi 22 cikin 100 a watan Yuli, kuma 'yan kasar na kashe kashi 59.1 cikin 100 na yawan kuɗin da suke samu a wajen sayen abinci kawai," kamar yadda hukumar kididdiga ta fada a wani rahotonta.
“Rayuwa ta yi wahala sosai, tsada da wahalhalu sun ƙaru saboda rashin kudi da tashin farashin kayayyaki da kullum ake ciki.
“Abubuwa da yawa na kasa yi ko na ce na tsayar da su saboda ba za su yiwu ba saboda tsada da kayayyaki ke yi a kullum ga tsadar komai da ake ciki.
“Abinci kawai muke kokarin saya kullum, shi ma don ya zama dole,” kamar yadda Hussaini ya shaida min.
Matashin mai shekara 26 wanda yake da shagon sayar da kayan masarufi ya ce wannan yanayi na taɓarɓarewar tattalin arziki ya sa ya haƙura da abubuwa da dama da matashi kamarsa ke buƙata.
End of Wasu labaran da za ku so ku karanta
Abubuwan da Hussaini ya haƙura da su
A matsayin shekarunsa, Hussaini ya kai ya ajiye iyali, amma ya ce rashin isasshen kuɗaɗen da za su ba shi damar yin auren cikin kwanciyar hankali ya sa ba ya tunanin yin hakan a nan kusa.
Ya ce: “Na farko idan na dauko aure a yanzu sai na nemi gidan haya, ga kuɗin kayan aure da na sauran tsarabobi.
“Ni kuma shagon nawa abin da nake samu da ƙyar yake isata biyan buƙatuna na dolen-dole, balle kuma na ɗauko aure, bayan ga nauyin iyaye da ƴan uwa na kusa a kaina,” a cewarsa.
Sai dai Hussaini ya ce hakan ba wai yana nufin ba zai yi auren ba ne kwata-kwata, amma zai ɗauki lokaci a ya shirya nutse ta hanyar tara kuɗinsa a hankali a hankali.
“Idan so samu ne ma sai na ɗan yi ginina ko ƙarami ta yadda biyan kudin haya ba zai ɗaga min hankali ba.”
Baya ga batun aure, matashin ya ce tun bayan kammala karatun NCS dinsa a 2018 ya so ya ci gaba da digiri, amma wannan yanayi na matsin tattalin arziki ya hana shi cimma wannan babban buri nasa.
“Tunanin kudin makaranta da na zuwa da komawa da sauran muhimman abubuwa da karatun ke buƙata su suka hana ni fafutukar ci gaba da karatun,” in ji Hussaini.
Hussaini ya ce ko hidimar rashin lafiya ce ta taso masa a yanzu ya gwammace ya sayi magani a kemis kawai ya sha maimakon zuwa asibiti.
“To kullum ana yaudararmu wai asibiti kyauta ne, bayan kuma ba haka ba ne, dole ne sai ka kashe kudi kuma hidima ce babba.
“Shi ya sa na gwammace rage zuwa asibiti ya zama cikin matakan da na ɗauka na rage kashe kuɗi.”
Ƙwalisar samari
Duk da yake matashi da ke kan ganiyarsa, Hussaini ya ga gara ya rage buruka da yawancin samarin zamani suka ɗorawa kansu.
Ya shaida mana cewa ba ya rayuwar ƙarya da ta fi ƙarfinsa duk da dai yana da shagonsa na sana’a.
“Ba ruwana da cewa sai na sayi kaya masu tsada ko babbar waya, gara a lallaɓa a samu na cin abinci kawai,” ya ce.
Hatta da yin ƴan mata Hussaini ya ce bai tsayar da ɗaya ba tukunna har yanzu, “saboda su ma hidimarsu mai yawa ce, to da kanka za ka ji ko da budurwa.”
“Dole ka haƙura da komai don ba ka da damar yin su. Addu'ar ƙara samun sauki da mafita muke daga Allah a kullin muke don hakan ne mafita gare mu kawai.”