Wane ne Dharmendra, jarumin Bollywood da ya rasu yana shekara 89?

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Litinin ɗin nan ne fitaccen jarumin fina-finan Bollywood na Indiya, Dharmendra ya rasu a birnin Mumbai ƴan kwanaki kafin ya ciki shekara 90 da haihuwa.
Firai ministan India, Narednra Modi ya bayyana alhininsa ga rashin jarumin wanda ya bayyana da "ƙarshen shekarun fina-finan India."
Tsohon jarumin wanda ya auri jaruma Hema Malini ya yi fina-finai fiye da 300 da suka karaɗe duniya.
Tuni dai manyan jaruman Bollywood ɗin suka hallara wurin jana'izar marigayin a Mumbai, inda za a ƙona gawarsa.
A tsakiyar watan Nuwamba ne labaran ƙanzan kurege suka cika duniya cewa jarumin ya mutu a daidai lokacin da ake jinyar sa a asibitin Breach Candy da ke birnin Mumbai na ƙasar ta Indiya.
Tawagar wasu likitoci ce ke lura da lafiyar jarumin a kowane daƙiƙa.
BBC ta yi yunƙurin jin ta-bakin ɗaya daga cikin likitocin da ke kula da lafiyar tauraron na Bollywood, sai dai ya ƙi ya ce komai, inda ya kafa hujja da kare bayanan sirri na maras lafiya da iyalinsa.
Sai dai bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa an kwantar da Dharmendra sakamakon fama da matsalar numfashi da kuma cutar lumoniya.
An kwantar da jarumin ne a ɗakin marasa lafiya da ke neman kulawa ta musamman, bayan la'akari da shekarunsa.
Wane ne Dharmendra?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dharmendra ya fara fim ne tun zamanin fina-finai marasa launi, ma'ana tun zamanin hoton bidiyo fari da baƙi.
Ya fara fim ne a shekarar 1960, in da ya fito a matsayin mataimakin jarumi, wato 'supporting actor' a fim din Dil Bhi Tera Hum Bhi Tere.
Daga nan ne kuma ya ci gaba da fitowa a fina-finai.
Sai dai kuma fina-finansa na shekarun 1970, sun fi haskaka shi da kuma karɓuwa.
Sanannun fina-finansa sun hadar da:
- Sholay
- Dharam Veer
- Charas
- Ghazab
- Hukumat
- Dream Girl
- The burning train
- Seeta aur Geeta.
Akwai jituwa tsakanin Dharmendra da Amita Bachchan sosai, saboda yawancin fina-finan da suka yi tare sun samu karbuwa sosai a wajen 'yan kallo.
Fina-finansu tare sun hadar da:
- Ram Balram
- Sholay
- Chupke Chupke
- Chala Murari Hero Banne
Duk da yake Dharam ya girmi Amita, akwai kyakkyawar alaka tsakaninsu har yanzu, kuma suna ganin girman juna.
A kalla Dharam ya yi fina-finai fiye 300 a tsawon rayuwarsa.
To sai dai kuma duk da fitattun fina-finan da ya yi, bai taba samun kyautar gwarzon jarumai ba wato best actor award.
Yawanci dai maza na son fina-finansa saboda akwai faɗa, ba kasafai ya fiye fina-finan soyayya ba.
Ba kamar Amita Bachchan ba, Dharam ba ya fitowa a fina-finai sosai, koda yake akwai fim ɗin sa Yamla Pagna Deewana Phir Se da zai fito ranar 31 ga watan Augustan 2018.
Fim din na su ne, sun kuma fito tare da 'ya'yansa Sunny da Bobby Deol.
Yaushe Dhermendra ya daina fim

Asalin hoton, Getty Images
Shekaru bakwai da suka gabata, babu abin da Dharam ke buƙata illa ya rinƙa shakatawa a katafaren gidan gonarsa da ke Lonawala.
Ya ƙayata gidan gonarsa, shi ya sa yake zuwa don ya huta.
Kazalika Dharam mijin mata biyu ne, domin bayan matarsa ta fari da suka yi aure tun da kuruciya, daga bisani ya auri jaruma Hema Mailini a shekarar 1979, bayan ya kasa jarumai kamar Shatrungan Sinha da Manoj Kumar a takarar nemanta.
Su ma 'ya'yansu biyu mata wato Esha Deol da Ahana Deol.
Esha ita ma jaruma ce, domin ta taba yin fina-finai kafin ta yi aure, amma Ahana ba ta taba yin fim ba, kuma ita ma tayi aure.
Shin Dhermendra ya Musulunta?

Asalin hoton, Getty Images
Abin da yake daure wa jama'a da dama kai shi ne, ya aka yi ya ke da mata biyu?
Bayanin shi ne, lokacin da suka fahimci juna shi da Hema har suka so aurar juna, addininsu na Hindu bai ba su damar auren fiye da mace guda ba, don haka sai suka Musulunta suka yi aure, kasancewar addinin Musulunci ya bayar da damar auran mace fiye da guda.
Dharamendra dai duk da shekarunsa ba shi da wata cuta da ke damunsa, kuma akwai sa'anninsa da dama wasu ma ya girme su da ya fi su kyan gani.
Kuma shi na kowa ne, shi ya sa jaruman da ke tashe a yanzu, ke bashi girmansa.
Sannan kuma a baya ya taba siyasa, don har mukami ya rike a yankinsu.











