Ƙasashe biyar da mata suka fi samun kwanciyar hankali a duniya

Asalin hoton, D3sign/Getty Images
- Marubuci, Lindsay Glowey
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
- Lokacin karatu: Minti 7
Duk da cewa ana samun ƙaruwar yadda mutum ke son yin tafiya ko bulaguro shi kaɗai ba tare da wani rakiya ba a shekarun nan, har yanzu mata na fuskantar ƙalubale idan suna tafiya ƙasar waje su kaɗai.
Sai dai akwai wasu ƙasashe da suka fi samar da matakai na kariya da tabbatar da cewa mata ba sa fuskantar wata barazana.
Bayan da aka jima ba a tafiye-tafiye saboda annobar Korona, a yanzu mutane sun daina tunanin cewa lalle sai sun samu abokin rakiya kafin su yi tafiya.
Yanzu mutane na son yin tafiye-tafiye zuwa ƙasashe su kaɗai musamman ma mata.
Wani bincike da kamfanin shirya tafiye-tafiye na ƙasar Norway (Norwegian Cruise Line), ya nuna cewa ɗaya daga cikin mutane uku ya fi son ya yi tafiya shi kaɗai, inda mata masu shekaru ke kan gaba wajen son hakan.
Haka kuma kamar yadda wani bincike da kamfanin shirya tafiye-tafiye na Virutoso ya yi, ya nuna cewa, waɗanda suka fi son tafiya su kaɗai daga shekara 2022 zuwa gaba su ne mata masu shekara 65 zuwa sama.
A 2019, kashi 4 cikin ɗari ne kawai na matan da suke tsakanin waɗannan shekaru suke tafiya su kaɗai, amma a 2022 yawan ya ƙaru zuwa kashi 18 cikin ɗari.
Duk da ƙaruwar da aka samu ta yawan matanen da suke son yin tafiya su kaɗai har yanzu mata na fuskantar ƙalubale na musamman a lokacin tafiya wata ƙasar waje.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da cewa abu ne ya kamata, ya kuma zama wajibi mata su yi tafiya cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ko barazana ba duk inda za su je, maganar ita ce har yanzu mata na fuskantar barazana da tsangwama da wariya a ko'ina a duniya.
To amma kuma duk da haka akwai ƙasashen da suka tashi tsaye domin tabbatar da ganin sun kawar da duk wata barazana da fargaba da ƙalubale da mata ke fuskanta idan suka je ƙasarsu.
Domin gano ƙasashen da suka fi wannan ƙoƙari na kyautata yanayin tsaro da kwanciyar hankali ga matan da suke zuwa ƙasashensu su kaɗai ba tare da wani ɗan rakiya ba, mun yi amfani da ma'aunin ƙungiyar tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalin mata - WPS - ( Women's Peace and Security Index), wadda ke da alaƙa da jami'ar Georgetown University, da rahoton ƙungiyar da ke duba giɓin da ke tsakanin mata da maza a duniya (Global Gender Gap ), wanda Taron Tattalin Arziƙi na Duniya (World Economic Forum) da kuma mizanin ƙungiyar tabbatar da zaman lafiya da tsaro ta duniya suka wallafa.
Sannan kuma mun tattauna da matan da ke zuwa waɗannan ƙasashe su kaɗai domin sanin abin da ya sa ba sa wata fargaba ko fuskantar ƙalubale idan suka je can, da sanin shawarar da za su bayar ga mai tafiya shi kaɗai, da wuraren da ya kamata mutum ya je shi kaɗai da kuma abin da zai yi.

Asalin hoton, DavorLovincic/Getty Images
Slovenia
Slovenia ce ta kasance ta ɗaya a tsakanin ƙasashen tsakiya da kuma gabashin Turai, wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali da kawar da duk wata fargaba ga mata masu son tafiya su kaɗai zuwa ta ƙasa, kamar yanda ƙiyasin WPS ya nuna.
Rahoton ya nuna cewa kashi 85 cikin ɗari na mata a ƙasar ba sa wata fargaba ko tsoro, hankalinsu a kwance yake.
Lokacin da Claire Ramsdell ta fara zuwa babban birnin ƙasar ta Slovenia kuma birni mafi girma na ƙasar, Ljubljana, ta riƙa yawo a titunan birnin da daddare tana ɗaukan hotuna ba tare da wata fargaba ba.
"Ban fuskanci wata matsala ba ta yawo a birnin. Harshe da sadarwa, waɗanda galibi mutum ke samun matsala da su idan ya je wata ƙasa, shi kaɗai, ni ba su zamar min wata matsala ba," in ji ta.
Ramsdell, ƙwararriya ce a kan harkar yawon buɗe idanu da ke aiki da kamfanin Wildland Trekking, kuma tana da shafin intanet mai suna Detour Effect.
Ya ce : "Idan da a wata ƙasa ne da labarin ya sha bamban, to amma a nan abin sai hamdala."
"Ba wanda ya yi min wata barazana ko wata tsangwama a duk tsawon lokacin da nake ƙasar."

Asalin hoton, Michael Cook - Altai World Photography/Getty Images
Rwanda
Rwanda, inda kashi 55 cikin ɗari na 'yan majalisar dokokin ƙasar mata ne , ita ce ta ɗaya a duniya wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali ga mata.
Ƙasar ce ke kan gaba wajen tabbatar da kwanciyar hankalin mata, kuma ita ce ta shida wajen rage giɓin da ke tsakanin mata da maza, ƙiyasin da ke nuna yadda ake damawa da mata a harkokin tattalin arzƙi da ilimi da kuma kula da lafiya.
Rebecca Hansen ta gani a zahiri yadda ƙasar take tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali, ba wata fargaba ga mata matafiya su kaɗai a lokacin da ta koma Rwanda daga Denmark a 2019.
"Akwai 'yansanda da jami'an tsaro da sojoji a ko'ina, dare da rana,''h in ji ta.
"Da farko idan ka gan su, abin zai tayar maka da hankali, to amma bayan wani lokaci za ka ga cewa duk waɗannan jami'an tsaro suna haba-haba da mutane, kuma a shirye suke su taimake ka."
Ta ce galibi mutane ba sa damunka. Kodayaushe za ka ga wani na son ya yi Turanci da kai, suna gaishe ka da Turanci, musamman ma 'yan makaranta sun fi yin haka
Ingilishi da Faransanci su neharsunan hukuma a ƙasar, tare da harsunan ƙasar naKinyarwanda da Swahili, saboda haka ba wata matsala game da harshe idan ka je ƙasar. ''Hatta waɗanda ba sa jin Ingilishi ma za su taimake ka, ta hanyar nune.
Rwanda ta kasance kan gaba a tsakanin ƙasashe wajen sasanto da wanzar da zaman lafiya tun kisan kiyashi na 1994 da ka ayi wa Tutsi.

Asalin hoton, Jorg Greuel/Getty Images
Haɗaɗɗiyar Daular Laraba
Haɗaɗɗiyar Daular Laraba, ita ce ta ɗaya a tsakanin ƙasashen Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro ga mata, a ɓangaren ilimin mata da sanya su a cikin harkoki da kuma tattalin arziƙ.
Ƙasar jigo ce a yankin wajen tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata, inda a baya-bayan nan ta cimma daidaito na yawan maza da mata a majalisar dokokinka.
Kashi 98.5 cikin ɗari na mata da 'yan mata da suka zarta shekara 15 sun ce hankalinsu kwance yake ba sa wata fargaba ta tsaro ko wani abu idan suna tafiya a titunan biranen ƙasarsu ko wasu yankuna da daddare.
Dubai ne ma birni mafi tsaro da kwanciyar hankali ga duk wata mace da ke tafiya ita kaɗai, kamar yadda kamfanonin inshorar tafiye-tafiye suka nuna.
Sandy Awad, mai tasiri a shafukan sada zumunta da muhawara, wadda ke zaune a Dubai da Paris, ta ce a kodayaushe ba ta jin wata fargaba a Dubai, ko da kuwa tana wajen birnin ne.

Asalin hoton, D3sign/Getty Images
Japan
Japan na ɗaya daga cikin ƙasashe goma da suka fi zaman lafiya da kwanciyar hankali
Japana tana da al'adar samar da ɗaki na mata kaɗai a tasshoshin ƙarƙashin ƙasa na jirgin ƙasa, da kuma masauki da mata kaɗai, wanda hakan ke sa matar da ke tafiya ita kaɗai ta samu kwanciyar hankali da tsaro.
Baya ga wannan, mutum na iya zuwa gidan cin abinci shi kaɗai ba tare da rakiyar wani ba, kamar yadda wasu abubuwan da dama mace za ta iya yi ita kaɗai a ƙasar ta Japan saɓanin wasu ƙasashen.
Japan ƙasa ce da yawan al'ummarta ke raguwa, saboda ƙasa ce da ba a sha'awar yin aure sosai, inda mutanen da suke su ƙadai ke cin moriyar rayuwarsu sosai.
Saboda haka akwai abubuwa da dama na jin daɗin rayuwa da hukumomin ƙasar suka ware domin mutane ɗai-ɗai.

Asalin hoton, Johner Images/Getty Images
Norway
Norway na daga cikin ƙasashen da suke kan gaba a duniya wajen tabbatar da daidaito ta ɓangaren tattalin arziƙi da kuma doka a tsakanin maza da mata, da kare lafiya da kwanciyar hankalin mata a cikin al'umma, kamar yadda ƙididdiga ta nuna
( Women's Peace and Security Index).
Ƙasara na cikin ƙasashe goma da suke da tsari na daidaito tsakanin maza da mata tsawon shekaru, kuma tana daga cikin ƙasashen da suka fi zaman lafiya da lumana da farin ciki a duniya.
Norway ta tabbata ƙasa ta zaman lafiya da kwanciyar hankali ga matafiya daga al'adu iri daban-daban, da suka haɗa da waɗanda suka fito fili suka bayyana kansu a matsayin masu neman jinsi ɗaya, ko kuma masu bulaguro su kaɗai.











