Yaushe aka fara yin sumba a tarihi?

Hoton birrai biyu na sumbatar juna idonsu rufe

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Masana kimiyyar sun fassara sumba a matsayin hada baki da motsin lebe ba tare da abinci a bakin ba
    • Marubuci, Victoria Gill
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science correspondent, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 3

Mutane na yi birrai na yi hatta wasu nau'uka na dabbobi ma na sumba, kuma yanzu masu bincike sungina wata hanya da suke ganin za su iya gano asalin dabi'ar.

Nazarinsu ya nuna alamun cewa sumba ta samo asali tun sama da shekara miliyan 21 da ta wuce, kuma wata dabi'a ce da mutanen zamanin da da birrai na zamanin da kila su ma suka rika yi.

Haka kuma wannan binciken dai ya nuna cewa mutanen zamanin da masu siffa kamar ta birrai suma kila sun yi wannan dabi'a ta sumba, kuma watakila an samu wannan alaka tsakaninsu da mutane irin na zamanin yau.

Masana kimiyyan sun yi nazari a kan wannan dabi'a ta sumba saboda kusan ta kasance tsakanin halittu tun na sali har zuwa yau - duk da cewa ba ta da wata alama ta zahiri ta lalle sai an yi ta za a rayu ko sai an yi ta za a haihu, amma kuma duk da haka dabi'a ce da hatta a tsakanin dabbobi ma ake gani ba mutane kadai ba.

Hotunan dabbobi suna sumbatar junansu

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Masu binciken sun gano shedar sumbata a tsakanin halittu da dama

Bayan da suka gano sheda ta yadda wasu dabbobi ke sumbatar junansu, masana kimiyya sun yi kokarin gina wani tsari na bincike inda suka gano lokacin da suke ganin kila an fara wannan al'ada ta sumbata tsakanin halittu.

Domin tabbatar da ganin cewa suna magana ne kan dabi'ar da take iri daya a tsakanin halittu ko dabbobi iri daban-daban, masu binciken sun bai wa dabi'ar fassara daya wadda ba lale ta soyayya ba ce - ma'ana ba za a ce lalle sumbata soyayya ce ba.

A nazarin nasu wanda aka wallafa a mujallar Evolution and Human Behaviour (published in the journal Evolution and Human Behaviour), sun yi wa sumba fassara a matsayin hada baki da baki ba cikin fushi ko fada ba, da motsin lebe ko bakin kuma ba tare da sanya wa daya abinci ba.

Mutane da birrai duka suna sumbatar juna, kamar yadda shugabar binciken

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dr Matilda Brindle, ta jami'ar Oxford ta bayyana.

Daga nan ne ta ayyana cewa suna ganin kila dabi'ar sumba ta faro tun kusan shekara miliyan 21 da rabi da ta wuce a tsakanin manyan birrai.

A wannan nazarin masana kimiyya sun gano dabi'a ko mu'amulla tsakanin halittu da ta dace da fassara da suka yi wa sumba.

Masu binciken sun ga hakan a tsakanin kyarkeci da kurege da wasu nau'ukan tsuntsaye dangin shamuwa da sauransu.

Masanan sun mayar da hankali a binciken nasu a kan birrai domin su gina shedara alamar asalin sumba a tsakanin mutane.

Nazarin ya kuma zartar da cewa nau'in birran zamanin da, wadanda suka gushe daga duniya kusan shekara 40,000 da ta wuce, wadanda kuma suka fi kusanci da kamannin dan'Adam, su ma sun yi wannan dabi'a ta sumbata.

Wani bincike da aka yi a baya ya kuma nuna cewa dan'Adam irin na wannan zamanin da wadannan birran suna da kwayoyin bakteriya a baki irin wadanda ake samu a yawun mutum.

''Wannan na nufin kenan sun rika musayar yawu tsawon dubban shekaru bayan da halittun biyu suka rabu,'' in ji Dr Brindle.

Birrai biyu na sumbatar junansu

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Masana kimiyyan sun ce wannan dabi'a ce da mutane da birrai suke yi

Yayin da wannan binciken ya nuna lokacin da yake ganin sumba ta samo asali, nazarin bai iya amsa tambayar dalilin da ake yin sumbar ba.

Akwai bayanai na fahimta da dama da ke nuna cewa, susa da cire kwari da birrai ke yi wa juna, kila ita ce silar sumba - wadda kila hanya ce ta sanin yanayin lafiya da dacewa ko sabanin haka a tsakanin masu sumbatar.

Dr Brindle na fatan wannan zai samar da hanyar amsa tambayar dalilin yin sumba.

"Yana da muhimmanci mu fahimci cewa wannan wata dabi'a ce da hatta birrai da sauran wasu halittu suke yi," in ji ta.

"Ya kamata mu rika nazarin wannan dabi'a, ba wai kawai mu yi watsi da ita ba a matsayin shirme saboda tana da alaka da soyayya a tsakanin mutane."