Dan wasan bayan Portugal Pepe ya yi murabus daga kwallo

A

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Dan wasan bayan Portugal Pepe ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafa, wanda yana daya daga cikin wadanda suka fi cikin kofina da dama a yanzu.

Dan wasan mai shekara 41 shi ne ya fi kowanne tsufa cikin ‘yan wasan Portugal da suka buga mata Euro 2024, wasansa na ƙarshe kuma shi ne wanda suka buga da Franasa a gasar.

Tsohon dan wasan Real Madrid ɗin ya bugawa ƙasarsa wasa 141, Cristiano da Joao Motinho ne suka fi buga wasanni.

Ya buga wa Madrid wasa 334 lokacin da ƙungiyar ta mamaye nahiyar Turai.

Cikin abin tausayi Pepe ya yi godiya ga duk wandanda suka taimaka masa ya kai inda yake a yau a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na kafafen sada zumuna a ranar Alhamis.

Ya lashe Euro 2016 da Portugal sai kuma ya taimaka wa Real Madrid ta lashe Champions Lig uku da La Liga uku a zamansa na shekara 10 da ya yi a ƙungiyar.

Muguntar da Pepe yake yi a kwallon ƙafa a bayyane take, ta yadda ya fi kowanne ɗan wasa yawan samun jan kati a lokacinsa.

Tsohon ɗan wasan REal Madrid ɗan kasar Portugal, Cristiano Ronald ya ce "babu kalmar da za ta bayyana girman Pepe a wurina"